Seventeen

2.2K 226 17
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            DOCTOR SHEERAH!

                                         •°17°•


             "Yoo! My guy, what's up??". Abdus-Salam, daya daga cikin abokan Moustapha ya tambayeshi cikin accent dinshi na yarbawa daya rike bakinshi kam, kasancewarshi bayerabe.

Moustaphan ya saurara da bugun punching bag din da yake yi babu kakkautawa a cikin gym din makarantar ta UCY, nishi yake kamar zai amayar da diyan hanjinshi. Sai daya dan nutsu kafin ya dauki goran ruwa ya kafa a bakinshi ya daddaka, kallonshi ya sauke akan Abdus-Salam din. "ya ne Abs? (nickname din da yawancin abokanshi suke kiranshi dashi kenan)".

Ya daga kafada, "karfe tara ta wuce, kusan awa biyu kenan kana motsa jiki. Kazo muje mu ci Abinci mana". Moustapha ya dauki singiletinshi dake rataye a jikin hanger ya sanya, yace "kasan bana cin abinci a ko'ina barkatai" Abs ya harareshi kasa-kasa, "picky eater son of...." hararar da Moustapha ya jefa mishi ita tasa yayi shiru tare da daga hannuwanshi sama cikin nuna alamun surrender, yana murmushi mockingly.

Yace "to zo ka rakani ni inci abincin, a yadda nake jina ba zan iya kaiwa gida ba tare da abu ya shiga cikina ba. Kasan jiya da dare ban ci abinci ba". Moustapha ya dan fitar da lebenshi ta gefen bakinshi ya kada, "ai bani nace kayi wasting Kwalbar champagne hudu ba a jiyan, ko ni ne?". Abs yayi dariya, "kasan ni da champagne ba mutunci, Mouh. Muje don Allah. I've got 11'o'clock lecture".

Fita suka yi daga cikin gym din, suka shiga motar Abs din. Wata karamar sports car, Peugeot e-legend. Yar karama mai kofa daya, ash color sai sheki take yi, daga ganinta kaga sabuwar mota. A kofar Moon Duckers suka yi parking, karamar restaurant ce duk dai a cikin makarantar take. Suka fita daga cikin motar gabadayansu, Moustapha ya karewa wajen kallo yana kada harshenshi a gefen bakinshi, "yanzu ka rasa inda zaka jefo mu cin abinci sai nan wajen?". Abs ya jefa mishi harara, "kai fa dan duniya ne, abincinsu zaka ci?". Moustapha ya girgiza kai yana tabe baki, "ni? Allah ya tsare ni!". Abs yace "to sai ka mana shiru. Don dai baka taba dandana abincinsu bane, amma abincin wajen akwai dadi. Gashi babu hayaniyar dalibai sosai". Cikin restaurant din suka shiga, suka samu table mai daukar mutane biyu suka zauna bayan sunyi odar abinda zasu ci. Moustapha coffee kadai yace a kawo mishi. Cikin lokaci kankani an cika gabansu da abinda suka bukata.

A hankali yake sipping coffee din, hankalinshi yana kan Abs dake dura abinci a cikinshi, yana ta zuba mishi labarin abinda ya faru a wajen partyn abokinsu da suka halarta a daren daya gabata.

Sansanyar muryarta yake jiyowa a bayanshi, daga fari yayi zaton wasa ne, sai daya juya kadan idanunshi suka yi tozali da ita. Zaune suke su kusan shida akan teburi mai daukar mutane takwas, dukansu da takardu a gabansu da alamun discussion suke yi. Wani irin sanyi yaji yana sirarawa cikin ranshi. Kimanin kwanaki biyar kenan da haduwarsu, amma koda wasa, tunaninta bai taba barin ranshi ko na sakan daya ba. Yayi dana sanin kin karbar lambar wayarta da yayi ranar. Kodayake, bai yi zaton abin zai yi girma har haka bane. Shi da mata kwata-kwata basa gabanshi.

Ranar jeans ne baki a jikinta da rigar blouse ruwan kasa mai haske, ta yane kanta da veil light brown wanda yayi matukar fitar da kyawun fuskarta, ya kara fitar da kalar kwayar idanunta da suka dinga ziyartar mafarkanshi ba kakkautawa.

A nutse, kuma cike da nuna kwarewa, take yiwa wadanda yayi zaton course mate dinta ne, bayani akan wata matsala a calculus. Lokaci-lokaci ta kan kurbi bakin tea da aka ajiye a gabanta, Yayin da sauran duk coffee ne a gabansu.
Gabadaya hankalinshi ya maida kanta, yana kallon duk wani motsi da take yi.

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Where stories live. Discover now