18

608 60 5
                                    


JUNE 2007

“Wai kina nufi har da wannan ‘yar alfarmar zamu kai dinkin kayan anko?”

“kausar ba ni nace haka ba, mami ce, kuma ita ce ta bada kudi aka sawo ma amina. Kuma this is the last time da zan roke ki ki daina kiranta da ‘yar alfarma. Idan mami taji, pls kar kisa sunana a ciki.”

Kausar ta kula ran naana ya baci, ba yau suka fara fada akan amina ba. A tunanin kausar naana da mami suna kai amina wani matsayi da bata isa ta taka ba, saboda ba yau ne kungiyar su mami suka fara taimakon maras galihu ba, ko an zo dasu wani lokaci a ofis din su ne, amma wannan aminar an kawo ta gidan mami,ta tare har tana zuwa school. A gidan ma maimakon a bari ta zauna dakin inna jummai inda take tare da dije a yanzu, sai aka kawo ta dakin naana, dakin da ta ke kallo a matsayin second room nata. Yes! Gidan mami ne second home nata ta sani ita da yaya abdul, kuma sam bata son zaman amina a gidan.

Ta kara gyara zamanta akan gado, gadon da idan tazo gidan take dauka nata ne, sannan ta yamutsa fuska tana kallon naana dake zaune akan kujera, tace “sorry fa, na tabo masoyiyarki, yaushe za muje kasuwa, ko daga school zamu wuce gobe?”

“wai sayen takalma? ki bari muje sabon boutique da na gani kusa da ofis nasu mami. Akwai designer shoes sosai.”

"kin san me? So na keyi mu hadu sosai a bikin yaya da anty meena. So na keyi mu hadu sosai saboda duka kawayenmu na gida da na school zamu gayyacesu ne, kin gane ai."

Nana tayi dariya tace kauuuusaaaar, Allah Ya sauwake miki abinda ya sameki, ke dai haduwa dai haduwa. Ai na sani dole mu shirya sosai, amma ni a gaskiya ba don kawaye ba, saboda biki ne na yaya fari! Dole mu hadu. Suka kwashe da dariya kamar ba sune suka haura ba.

Daidai nan Amina ta shigo da sallama. Tana sanye da doguwar rigar atampa purple da kalar siminti, jikinta rufe da hijab mai haske iya gwiwa, hannunta rike da jakar littafai da waya. Ta kara fari da jiki kadan fiye da lokacin da tazo gidan. Naana ce ta amsa sallamar cike da fara’a, idanunta akan amina wadda tun shigowarta ta sha jinin jikinta saboda ganin kausar a dakin a kuma kan gadon da take kwana akai.

“Bingyel daliba, ba zaki zauna ba?” naana tayi mata nuni da nata gadon saboda lura da tayi yadda kausar ta kara yin rashe-rashe akan gadon tana yatsina fuska kamar taga kashi. Amina tayi murmushi ta isa kan gadon naana ta ajiye Jakarta, tana kokarin cire hijabi. Juyowar da za tayi suka hada ido da kausar din, wadda ke kallonta a yatsine cike da gadara. Ta cire hijab din sannan ta dauko karamin mayafi baki daga cikin wardrobe tana kokarin yafawa.

Ta mayar da kallonta ga naana tare da fadin, “wai naana ban gane ba, wa ke kwanciya akan gadona yanzu? Naji odour na bed cover ya canza, ni fa bana son sharing ke sani.”

Tana kokarin basar da maganar tace, “amina ba kya gajiya da lullubi ne, naga an dauke wuta, akwai zafi. “wai fita zanyi wajen inna. Zan je naga yadda zata hada garin masa, tace zata jira dawowa ta na ga yadda yadda ta ke yi.”

Kausar ta kula daga naana har amina sun share ta, abinda tafi tsana a rayuwarta. A ranta tace “a whole me! Da ni kuke zancen.” Ta tashi zaune daga kwanciya tana kallon amina da ke kokarin fita daga dakin tace, “bingo kike ko amina? Kawar taki bata fada miki wannan gadon nawa ne duk lokacin da na zo gidannan. Why not ki dinga kwanciya dakin su inna?”

Har ta kai bakin kofa kamar ba zata tanka ba, sai ta juyo fuskarta dauke da muirmushi, ta kai dibeta da kyau da idanunta masu haske, tace, “ kausar, ba bingo bane bingyel ne, kuma mami ce tace na dawo nan dakin, kina iya fada mata cewa na koma dakin inna, duk daya ne a wajena.” Bata jira amsar kausar ba, ta fice daga dakin. Baki bude kausar ta juyo tana kallon naana, wadda ta ware ma ta hannuwa alamar babu ruwanta.

Maimakon ta wuce dakin inna inda take zama da diyar kanwarta da ta dauko saboda shekarun girma da suka fara kamawa, sai ta wuce zuwa hanyar garden. A nan ta nemi ginanniyar kujera daya da ke kafe a kasa ta zauna. Tunaninta cike yake da maganganun kausar, na yau din da kuma wadanda ta saba yi mata a daidaikun haduwar da suka yi tun zamanta a gidan. Ta tuna wata rana da kausar tazo gidan, aka ce ta sauke ta a center da suke karatu, bayan mami ta shige ciki tace ba zata shiga mota daya da ita ba. Tana ji suna fada da naana akan haka sai ta dauki Jakarta tq fice. Allah Ya taimake ta tana da kudi a hannunta a irin kudaden da mami take bata duk sati, sai kawai ta hau keke napep. Daga baya da ta samu labari mami tayi fada sosai, hart a kira kausar din a waya ta yi mata fada.

A zuciyarta tace, “ban san me nayi ma wannan baiwar Allah ba, amma na daukar wa babana alkawari zan zauna nayi karatu, Insha Allah ba zan bari ta dameni ba. Duk abinda za tayi min ba zai kai na inna hadi ba.” Ba ta san tana zubar da hawaye ba, sai da taji sanyi yana bin fuskarta. Tayi nisa a tunani ta sa hannu tana sharer hawaye, sai taji muryoyi suna kusanto ta. Kafin ta ankara, sai ga mutane biyu a kusa da ita. Samari ne matasa, yan kwalisa.

Baya da haske sosai duk da ba za’a saka kirashi da baki wuluk ba. Yana da saje da wushirya kuma bai cika tara gashi a kansa ba. idanuwansa sak irin na naana masu daukar hankalin wanda suke kallo. Kakkarfa ne kuma yana da tsayi da fadin kafadu , Aliyu Adam Lema kenan, wanda aka fi kira da Imam. Kamar mafi yawan ranaku, yana saye da kananan kaya, shirt ce navy blue da wandon jeans a jikinsa.

Dayan kuma fari ne tas! Mai dogon hanci, idanunsa a ciki suke basu cika girma ba. A kallo daya za ka kirashi lauka-lauka, sai dai kuma a tsaye yake sak, tsawonsu kusan daya da danuwansa. Yana da gashin kai baki mai laushi irin na fulanin asali. A jikinsa shadda ce kaftan  mai kalar ruwan zuma da hula kalar shaddar. AbdulHameed Bello Lema ne da aka fi sani da Abdul Lema.

Da sauri amina ta mike tsaye tana gayar dasu, da alamun daburcewa kadan. Ina wuni Ya imam. Ta fadi da dan sauri kadan, sannan ta juyo ga wanda suke taren ta gaida shi. Suka amsa mata, imam ne yace, “ya dai amina, me ki keyi anan ke kadai." "Ahhh... Ba komi, na fito ne…. am… yanzu zan koma.”

Yayi shiru kadan sai da yaga zata wuce sannan yace “ina naana ne hala.” “Tana ciki tare da kausar.”

“It’s o.k. karatun dai babu matsala ko?” ta girgiza kai tare da fadin “Babu matsala yaya. Nagode.” Daga nan ta wuce ciki tana sauri tana mamakin irin kallon da Abdul ke bin ta dashi kamar ya taba saninta a wani wuri? A ranta tace “ko dai shi din ma irin kausar ne baya da kirki?”

Abdul ne ya maye gurbin kujerar da ta tashi, yana fadin, “kaiiii am damn tired wallahi, wannan shirye shiryen sun ki karewa.” Imam ya dibeshi ya tabe baki sannan ya mayar da hannuwanshi a cikin aljihu yace “lazy ango.”

“Wai wacece wannan mai sunan amaryata?” “Oh wai amina, tana zama a hannun mami ne, ta samu matsalar aure ne." "Ohhh, naji kausar tana maganarta, ko wani matsalane blah blah… ka san kausar da condemning jama’a, cant remember abinda tace dai. Wait! Wannan ce tayi aure? Kai fake imam ko dai baka ji daidai ba ne.”

“Allah anyi mata aure da wani acan kauye, yanzu babu auren tana attending center ne nasu mami.” “So bazawara ce! Too bad. mami suna kokari fa. but i was surprised naga ka na kulata, ko dai tana dafa abinci ne, na san ka da son girki.” “Wai har za kayi auren ma ba za ka daina sa ido da iskanci ba, Allah ni tausayi take bani. Bari ka tambayi naana zata fada ma labarinta akwai tausayi.”  "eh sai naana kam, ita da bakinta ba ya ciwo. Ina tausayin matar da zata zauna da kai wallahi." Ya mike tsaye sannan yaci gaba “kai muje ciki, ni fa yunwa na keji.” “oh, ashe bani kadai nake son girki ba.”

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now