PART 1-2

262 3 7
                                    

*_RASHIN ASALI_*
         
         🕊🕊🕊🕊

*_WRITTEN~BY✍🏻_*

*_ANTY MAIMOUNATH O.G_*

*_SADAUKARWA GA👇_*
*_MAHAIFIYA TA😘_*

*_🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟_*
                    *_G.W.F_*

~*Home of gorgeous, intelligent and experts writers, we are d best among d rest*~

Https://www.facebook.com/
Groupsgorgeouswritersforum/
1726580770789237/

*_GODIYA DA YABO SUN TABBATA GA ALLAH(S.W.T), MAHALICCIN DUKKAN WANI ABIN HALITTA BAKI 'DAYA_*
*_TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU K'ARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMADU DA ALAYENSA DA SAHABBANSA BAKI 'DAYA_*
*_YANDA NA FARA NOVEL D'IN NAN LAFIYA, ALLAH KA YARJE MIN IN GAMA SHI LAFIYA,AMEEN_*

*_WANNAN NOVEL SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA, BANI DA KAMAR KE MAMA NA, ABINDA KIKAYI MIN BAN ISA IN BIYAKI BA SAI DAI INYI MIKI ADDU'AR GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA, ALLAH YA SAK'A MIKI DA GIDAN ALJANNAH_*

*_GARGADI_*
*_BAN YADDA A YI AMFANI DA WANI SASHE NA WANNAN NOVEL D'IN BA,KUMA BANYI DAN CIN ZARAFIN WANI BA, DUK WANDA YA GA YAYI DAIDAI DA RAYUWARSHI TO AKASI NE_*

*~________________________~*
_RABBI HABLI MILLADUNKA ZURIYYATAN 'DAYYIBA🤲
*~_________________________~*

*DEDICATED TO*
*UMMU BASHEER*
      *HU$$@IN ATK*
*BEAUTY QUEEN*
       *PRINCE ABDALLAH*

*_BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHIM_*

           *1-2*

Yarinya ce wacce bata wuce shekara 12 ba ke ta faman gudu kayan jikinta duk datti gashi da alamar ta matuk'ar galab'aita dan wuya.....

Wasu k'artin maza biyu ne naga sun biyo hanyar da yarinyar ta bi da gudu, ina kyautata zaton ita suke bi, Allah ya taimake ta ta samu wani wuri ta la6e, suka gaji da binciken ta basu ganta ba sai suka koma baya da gudu......

Yarinyar na ganin haka ta tashi ta cigaba da gudu bata ma san ina zata ba, ita dai gudun ceton ranta takeyi idan ka ganta abin tausayi.....

Bata tsaya da gudun ba har ta kawo bakin titi, tsautsayi bata ko kallon gabanta mota ce tazo ta kwashe ta a nan, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un......

Mai motar ya tsaya, shi da matarshi ne a cikin motar, da sauri suka fito daga motar, basu wani b'ata lokaci ba matar ta d'auketa ta saka a mota, alhajin ya ba ma motar wuta sai cikin gari......

Kai tsaye asibitin suka wuce da ita, da isar su aka amsheta dan bata taimakon gaggawa.......

Bayan kamar 30mnt doctor ya fito yana cewa'' ina wa'yanda suka kawo yarinyar nan?,

Alhaji da matarshi suka nufi inda doctor yake, Alhaji ya bashi hannu yace'' Sunana Alh.Ahmad mune muka kawo ta'', doctor ya kalli alhaji yace'' a gaskiya yarinyar nan tana cikin wani hali, dole a baku gado dan ta samu buguwa sosai a kanta, kenan zamu bari mû ga yanda zata farfad'o tukun'',

Innalillahi kawai suka furtawa, Alhaji Ahmad yace'' doctor zamu iya shiga mû ganta?

'' Eh muje ciki'', bayan doctor suka bi har d'akin da aka kwantar da ita, kwance take ko motsi batayi, an d'aura mata drip a hannu......

Kwanan yarinyar nan uku a asibiti sannan ta farfad'o, ihu ta saka tare da dafe kanta da ke mata ciwo, da sauri likitocin sukayo d'akin doctor na biye dasu, hajiya kuma ta d'an zaga ne.....

Fusge-fusge takeyi kamar mai ciwon hauka, allura sukayi mata a daidai lokacin hajiyar ta fito, doctor yace da hajiya idan alhaji yazo ya sameshi a office d'inshi.

Hajiya da zuwan alhaji ta sanar mishi sak'on doctor, ya iskeshi can office d'in, bayani yayi mishi kan ciwon yarinyar ya kuma ce a gaskiya kanta bai dawo daidai ba da alama akwai abinda ya firgita ta,

Alhaji yace'' to yanxu meye abinyi?, dan nima ban san yarinyar ba kawai tsautsayi ne ya ratsa ta taho da gudu kan titi na kad'eta da mota, kaji yanda akayi'',

'' To akwai abinda ta gani wanda ya bata tsoro, amma karka damu insha Allah zamuyi iya bakin k'ok'arin mû dan ganin cewa ta samu lafiya'',

Godiya alhaji yayi mishi sukayi sallama ya koma can d'akin.

Wasa-wasa sai da yarinyar nan tayi kusan wata d'aya a asibiti sannan ta samu sauk'i, a wata safiyar laraba ne ta farka tana fad'in'' ina ne nan, wayyooo zasu kasheni ku taimake ni, me nayi muku ne?,

Hajiya ce da 'yarta duka isa bakin gadon, hajiya ta kamata tana cewa'' 'yata ki nutsu nan asibiti ne babu wanda zai kamaki kinji ko?,

'Kuru tayi tana binsu da kallo kamar wata zararra, suma d'in ita suke kallo, da yamma aka basu sallama suka tafi gida.

*Wanene Alh.Ahmad?*

Alh.Ahmad haifaffen garin zaria ne, iyayen shi sun rasu tun yana d'an shekara 5 a duniya, ya taso gaban k'anin mahaifinshi, ya nuna mishi so tamkar shi ya haifeshi da yake shi Allah bai bashi haihuwa ba,

Ba wani mai arziki bane kawai saidai rufin asirin Allah, haka yasa Ahmad a makarantar boko daman yana islamiyya, da dad'i da wuya a hakan har Ahmad ya kammala karatunshi Allah ya hore mishi ya fara kasuwanci daman fannin kasuwanci ya karanta dan yafi son harkar bisa ga aikin gwamnati......

Cikin ikon Allah Ahmad ya samu bud'i fiye da tunanin mai karatu, k'anin mahaifinshi wato baba Abdu ya matsa mishi cewar ya kamata yayi aure tunda ya kai minzalin auren......

Ya samu wata yarinya mai suna Fatima suka daidaita akayi bikinsu cikin k'ank'anin lokaci ta tare, bayan shekara d'aya Allah ya albarkace su da samun k'aruwa ta d'a namiji, sunan mahaifinshi ya saka mishi wato Mohammad amma ana kiranshi da Rafeek, amma shi Ahmad yana kiranshi da abbana saboda sunan shi.....

Sai da Rafeek yayi shekara 7 sannan Allah ya sake basu wata haihuwar wannan karon mace suka samu sunanta Ramlat.

Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin jin dad'i, a wani dare ne Allah ya d'auki ran baba Abdu ba tare da yayi wani ciwo ba, amman kamar yasan lokacin shi yayi dan a safiyar Ahmad yaje gidan shine ya sashi a gaba yayi mishi nasiha mai ratsa zuciya.....

Allahu akbar haka duniyar ta gada, rayuwa abin tsoro 'yan uwa, duk da Ahmad yana namiji amma sai da yayi kukan rashin mahaifi duk da bashi ya haifeshi ba amma ya rik'eshi da gaskiya da kuma amana.

Bayan wasu shekaru Fatima ta sake haihuwar 'yan biyu mata amma d'ayar sai ta rasu, sai suka sa ma d'ayar suna Ihsan, tun daga nan basu k'ara wata haihuwar ba.

Wannan kenan........

*Cigaban labari*

Ku biyoni danjin cigaban labarin, kuma nafison comments ba wai yawan heart ba

*'YAR MUTAN KAZAY👑*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 12, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RASHIN ASALIWhere stories live. Discover now