1

3K 112 14
                                    

*GIDAN* *SOJA*



*NA*

*YAR* *MUTAN* *KAGARA*



*DEDICATED* *TO* *MAIMUNA* *MATAR* *ABDULLAHI* AM


*wattpad :yarmutankagara 100*

🌈 *KAINUWA* *WRITERS* *ASSOCIATION*.............✍



*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHIM*



                       *1*


Sojoji ne jere reras a kan titin niteco road kowa kagani cikin su rik'e yake da bindigar sa sun daura jan kyalle a kansu.

Sai kaiwa da kawowa sukeyi sun rufe hanyan da ze kai mutun cikin tunga low-cost.

Indai zaka shiga low-cost tofa sai dai kayi zagaye kabi ta shiroro road.

Jerin motoci nahango masu kyau da daukan ido sun tunkaro wurin sojojin nan.

Motocin ne naga sun tsaya cak dede inda sojojin suka datse hanyan, motan dake gaba naga driver yafito yana tambayan sojojin meyake faruwa ne haka.?

Yace kun kosan "me girma commission ne yake son yakai ziyara gidan marayu.

Wani soja yace "an rufe hanya an kuma bamu umurni kada kowa ya wuce.

Motan dake tsakiya ne naga ya bude Alhaji Nafi'u Sulaiman wato commission for lands and housing, ne naga ya dunfaro inda sojojin suka rufe hanyan.

Sojan dake jagoranci wannan tafiyar wato command yana zaune daga gefe yana kallon yadda yaran shi ke gudanar da aikin su.

gani Alhaji Nafi'u Suleiman ne yasa shi tasowa da sauri.

Alhaji Nafi'u yace "meyake faruwa ne? da wata matsala ne?

Yana fadin haka yayin da yake k'araso wa wurin

Command  ne yace "barka da war haka yallabai,be bari Alhaji Nafi'u yayi magana ba yaci gaba dayi mishi bayani.

"masani ya muka samu kan cewa 'Baleri dashi da yaran sa suna cikin wancen dajin, na bayan gidan marayu.

"yarana sun shiga cikin dajin suna dubawa shiya sa muka rufe hanyar.

ba'a barin farar hula ta wuce tawurin, dan kar ana cikin bata kashi dasu harbi ze iya samun wani shi yasa muka bada tsaro sosai.

Commission yace "to gashi kuma nayiwa kai na alk'awarin kai ziyara kaman yadda nasaba kaiwa gidan marayu duk juma'a.

Amma ai ba nisa nan din da gidan marayu zan iya zuwa in dawo" cewan commission.

Command yace "yi hakuri yallabai gaskiya da hadari bin wurin nan, commission yace "tunda gaku anan ai zan iya zuwa inyi ziyara na indawo.

Command yace "yallabai tunda ka matsa bari wasu daga cikin yarana su bika saboda tsaro.

Yauwa hakan ma yayi cewan"commission

Commanda yace "Jacob wanda aka kira da Jacob ya amsa da "yes sir, "command yace kadibi mutane hudu dakai biyar ku raka commission gidan marayu.

"yes sir!!

Suna dab da gidan marayu suka fara jin harbi na tashi tako ina.

Sojojin nan sukayi iya k'ok'arin su na ganin sun kare commission sai bata kashi sukeyi da yaran 'Baleri commission in banda k'yarma ba abin da jikin shi keyi.

Da kyar suka sha saboda yawan da su 'Baleri kedashi suna gani sojojin nan sun kashe musu mutane biyu shine fa sukayi cikin daji da gudu.

Koda sojojin nan suka koma barrack sukayi reporting superior d'insu yaji mamakin yadda 'Baleri yasan da zuwa sojoji wurin.

Brigadier General yakai duban shi ga commission yace "amma Alhaji Nafi'u ai kayi ganganci bin hanyan da 'Baleri yake, ka kuwa san wanene 'Baleri? hmmmmm ina ganin jin sunan shi kawai kakeyi.

"Duk fa han yan da 'Baleri ya tsare tofa ak'alla in be kashe rai sama da goma ba to ze kashe tara, ido commission yafitar kamar zasu zube k'asa tsoro ne k'arara a cikin su.

Wani farmaki daya kai sojojin mu 12 ne suka rasa rayukan su yana da hadari sosai.

Brigadier yaci gaba da magana cikin kausashi yar murya mai cike da 'bacin rai yace " yanzu da bakayi ma yara na dole ba.

wurin zuwa gidan marayu ba, da yanzu 'Baleri na hannun mu saboda munjima muna neman shi.

Shiyasa yanzu muka shirya mai sosai amma yanzu gashi komai ya rushe mana a dalilin ka.

Wani babban sojo dake zaune yana sauraron su yace "yanzu dolene musake shiri dan in muka ba 'Baleri k'ofa koda so dayane tofa yasamu logonmu ke nan.

"commission yayi saurin shewa a'a Brigadier ni a ganina zaku iya kama 'Baleri cikin sauki.

"Kamar ya? cewan ogan Brigadier "

"yauwa inda za'ayi amfani da wata hanya tattausa wace base antura sojojin fad'a ba, kagani idan akabi da dubara ina ganin kamar zefi.

kar azo afkawar ku bata samu nasara ba.

Brigadier General yabuga table d'in dake gabanshi da k'arfi wanda hakan yayi sana diyar jawo han kalin yaran shi wuri.

Sai gasu da gudu kowanne da gun d'in shin a hannu.

Cikin fushi da d'aga murya Brigadier General
Yace "afkawar mu zata samu nasara!!!

Be jira cewan commission ba ya fita daga cikin office d'in cikin sauri da bacin rai.

Brigadier General be zame ko ina ba sai office d'in Major abubakar Sadiq brigadier nashiga Major ya mik'e da sauri bakin shi dauke da "mon'g sir!!

Brigadier General yace "easy Brigadier yace Sadiq
Major Sadiq yace "yes sir

Brigadier yace "kahada yaran da kayaba da aikin su saboda zan turaka kamo 'Baleri kasan yana cikin dajin nan na bayan gidan marayu.

Naga in ba kai natura ba bazamu samu biyan buk'ata ba, Major yace ok sir.

Brigadier yace "Sadiq kayi duk abin daya kamata dan 8:pm nake son kushi ga dajin nan domin kamo 'Baleri.

Major yace "ok sir"

"your wish is my command sir yana k'ara sara mishi.

Smile dauke a face d'in brigadier general yafurta" i trust you Major Sadiq yana d'an bubbaga kafadan shi.

Brigadier yace "Sadiq kasan dai hatsabi banci irin na 'Baleri dan haka kakula sosai duk da dai nasan kai d'in jankwar zo ne.

Yakara she zance sa yana dariya, major yace "nagode sir.

Cikin farin ciki Brigadier yabar office d'in Major Sadiq, kamar ba yanzu yagama fada da 'bacin rai ba.

Yana tafe yana murmushi jin dadi dan yasan wannan karon 'Baleri zezo hannu tunda dai Major Sadiq ne ze je aikin yasa ba wasa.

Brigadier General yana fita major Sadiq yahada yaran da zeje aikin dasu........





*yar* *mutan* *kagara*✍

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 02, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIDAN SOJAWhere stories live. Discover now