CHAPTER 1

179 7 0
                                    

[1:20PM, 2/20/2018] RØØKÎEY KÆXS✍🏻: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA*  ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄  *_A STORY BASED ON FICTION &  CONCOCTION_*

® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touched the heart❤of Readers_*

*BY*
*Rukayyah Kakumi*
*_(ROOKIEY KAXS)_*

        *DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*

       GODIYA

'''Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki mai kowa mai komai da ya bani ikon fara wannan littafin Allah ya bani ikon isar da sak'o me amfani kuskuren da ke ciki Allah ubangiji ya yafe min.

SAK'O GAISUWA GA
Haneefah Usman
Jiddah Ja'o
Yar_ficika
Ramalurv
Kausar Lurv
Ummiey Big
Fatiey Azland
Amnoor
Meelart AHK
Ayusha Iliasu
Asy Khaleel
Billy Sarki
Sweery
Deejah Jahun
Deejah Wazeeri
Aunty Jiddah Musa
CwtJiddah
Mr's Fawwaz
Umma yahya
Mommy sulti
First Lady
Memxiey
Maryam Abdool
MSB
Duduwa PML

Wanna Littafin tukwici ne ga each and every member of  '''         '''PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S Up! Up!! together we stand divided we fall ,we rock even in the heart of our enemies # one ❤ '''



1-5

SHIMFID'A

    Jami'ar Umaru Musa Yar Adu'a Jami'a ce da ke d'auke da mutane daga sassan Nigeria daban-daban kama daga Gabashin Nigeria zuwa yammaci,kudanci da Arewaci.
a cikin d'aliban da ke wannan Jami'ar ya had'a da wasu Kyawawan 'yan mata guda biyu AYUSHA DA ANEESERH.
AYUSHA yarinya ce kyakkyawa ta ajin farko tana da shape me kyau me d'aukr hankali, ba fara bace amma kuma baz'a a kirata bak'a ba tana da gashi har gadon baya sai dai matsalanta d'aya Allah bai hore mata yalwataccen dukiyar Fulani ba asalin ta yar garin katsina ce.

     ANEESERH ma kyakyawa ce ta ajin farko bambancin su da Ayusha kad'an ne ita fara ce sol sannan tana da wadataccen dukiyar fulani sai dai gashi ya mata yawa domin dakyar ake samun na parking.asalinta yar Jigawa ce wani gari da ake kira Dangyatin karatu ne ya kawota katsina har Allah ya had'ata da Ayusha suka fara k'awance ita a campus take zama sab'anin k'awarta da cikin gari.

*GUNDARIN LABARIN*

     A nutse suke taku kamar basa son taka k'asa Aneesa ta dubi Aminiyarta tace " 'yan mata ya kamata mu d'aga k'afa fa dan wannan tafiyar tamu ba inda zata kaimu kuma kin san Mr Ojokolo ba mutunci gareshi ba yana riga mu shiga sai dai muji a slow last week ma bamu samu munyi attending lectures d'in shi ba"
"Hmmm!!k'awata kenan wallah baza ki gane bane, Yau tunda garin Allah ya waye nake jin jikina very week dak'yar na iya tashi na shirya har na samu na shigo school"
"subhanallah,me ke damun ki haka"
"Wallahi nima ban sani ba nasan dai yau am abnormal, zai yi wuya idan ba wani mummunan aika aika ke shirin faruwa dani ba" sai ta fashe da kuka.

    
     Aneeserh tayi saurin rufe mata baki tana fad'in "please sistor ki daina fad'an haka falyak'ul khairan Auliyasmut (ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru) in shaa Allahu babu abinda zai faru dake sai alkhairi" itama sai ta fashe da kukan,waje suka samu suka zauna suka ci gaba da kukansu sai da sukayi me isarsu sannan suka bari, a k'alla sun d'au minti talatin a zaune ba wacca tace da yar uwarta k'ala daga bisani Ayusha tai k'arfin hali tace "Sistor tashi mu tafi hostel tunda munyi missing period din nan idan yaso da yamma sai mutafi gida muyi weekend a can dama Mummy na complain wai kwana biyu kin daina zuwa"
Aneeserh zatayi magana tai saurin rufe mata baki " bana son jin  unnecessary excuses naki dole sai kinyi weekend a gida"
Murmushi tai sannan tace "Al-masifatu your wish is my command" dariya sukayi gaba d'ayansu suka nufi hanyar hostel.

'''A dai-dai lokacin alk'alamina ya tsaya for today ku biyoni gaba dan bibiyar labarin wad'an nan yammatan da fatan wannan soman tab'in ya k'ayatar da ku'''

*ROOKIEY D BEST*
[1:30PM, 2/20/2018

ALLURA TA TONO GARMAWhere stories live. Discover now