®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
DOCTOR SHEERAH!
•°20°•
Ba ranar ta fara farkawa ta ganta a gidan Moustapha ba, and it wouldn't definitely be the last. Wannan shine mafari. Shi ya bude mata kofar kora ruwan maye, sai dai idan bata ganta ba, ko a gidan Moustapha, ko a parties din da ta riga ta zama regular.
Kamar yadda Moustapha yayi alkawari, a cikin satin suka je gidan marayu. Suka tafi da gifts sosai da kudi ya kai. Yayi mamaki matuka da yaga yadda Sheerah ta saba da wasu daga cikin ma'aikatan wajen har ma da wasu yaran wadanda ba'a dauke su daga gidan marayun ba. Daga can wani gidan marayun suka je a takaice sai da suka je gidajen marayu hudu ranar, da rehabilitation centers, gidan makafi da guragu biyu. Sai yamma likis suka koma makaranta.
☆☆☆☆☆
A gajiye likis ta shiga dakinta ranar. Kai tsaye kan gado ta fada ta kwants idanunta a lumshe. Ranar sunje matuary, gabadaya acan suka wuni. Kwana biyu karatunsu yayi zafi sosai, kwana uku kenan rabon da taga Moustapha, sai dai su hadu a waya ko chats. Sai data dan huta sannan ta tashi ta shiga tayi wanka da ruwa mai dumi, fitowa tayi tayi sallar isha'i kafin ta fita falo. Fadima da abokanta duk basa gidan. Ta duba fridge da sauran kicin din gabadaya taga babu abinci ci, tsaki taja ta koma dakinta ta kira inda suka saba sayen abinci tayi placing order din abinda za'a kawo mata. Yoghurt ta laluba ta koma kan kujera a cikin falon ta zauna tana sha, har aka kai mata abincin ta ci, kafin ta koma dakinta.
Tana shiga wayarta tayi kara akan gado, ganin sunan Moustapha yasa ta saki dariya tare da daukar wayar ta zauna a gefen gado. "hello, babe!".
Tana jiyo shi yana murmushi, "don't babe me, baby. Saboda Allah, tun safe sai yanz kike tunawa dani? Oh wait!! Nine ma na kira ki ashe, da sai gobe sannan zaki kira ni?". Komawa kan gadon tayi tana murmushi, "afuwan, am sorry, okay? Dawowa na kenan fa! Abinci kawai naci, na shigo kenan shine naga kana kirana. Ta yaya za ayi in manta da kai? Yinin yau curr kana manne a cikin raina, habibi!". Yayi murmushi, "yanzu naji dama-dama to. How was your day?".
Kusan awa daya daga rabi, suna hira akan events dinta na ranar.
Karfe sha daya da arba'in da biyar, yace mata yana kofar gidansu ta sauka kasa yana jiranta. Ta kalli agogo, "yanzu Moustapha? Ba zaka yi hakuri sai da safe ba kuwa?". Yace "it's urgent. Beside, ba zaki jima ba. Minti biyar yayi yawa". Tayi shiru kamar mai shawara, kafin tace "to gani nan saukowa".
Rigar sanyi data saukar mata har gwiwa ta dora akan kayan jikinta, riga da wando na cotton. Sai ta nada gyale a kanta ta fita. Tana sauka kasa, taga text dinshi kan cewa taje coffee shop din da suka saba haduwa. Duk da cewa tayi mamaki ganin cewa coffee shop din basa kai karfe sha biyun dare, haka nan ta taka har zuwa shagon. Shagon kwalam, babu alamun mutane ko kadan, ko masu waiters da masu daukar oda babu.
Tana shirin daukar waya ta kira Moustapha, agogon shop din ya buga karfe sha biyu dai-dai. Dai-dai lokacin kuma taji ihun 'Happy Birthday!' ya tashi daga bayanta. A tsorace ta juya.
Moustapha da tawagar abokanshi, da wasu daga cikin class mates dinta da take hanging around with, tunda ba zata kira su abokanta ba. Bata san komi game dasu ba sai sunaye da courses din da suke yi. Suka nufeta, hannun Moustapha dauke da katon cake two steps an kunna candles akai, suna rera mata wakar happy birthday.
ESTÁS LEYENDO
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
EspiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...