®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
DOCTOR SHEERAH!
•°21°•
Abin kamar wasa haka yaje mata. Ta kurawa wayarta idanu kawai tana kallo, gani take yi kamar kowane lokaci, zata ga text din Moustapha yana cewa 'buh!! I got you, babe. April fool!!'. Duk da cewa tasan babu yadda za'a yi watan Fabrairu ya koma Aprailu, ta dai yi fatan hakan ta kasance.
A hankali, reality ya dinga shigarta, sai data ji komi na duniyar ya fita a ranta. Abinda tayi tsoro kenan tun daga farko, ta damkawa wani amanar zuciyarta daga karshe kuma yazo yayi watsin ala-tsine da ita. Abinda Moustapha yayi mata kenan. And it hurt!.
To amma, sai me don yace ta manta dashi? It's not as if ba zata iya ba.
Sai me don ya daina sonta? It's not as if ba zata iya rayuwa ba tare dashi bane.
Yana tare da ita, ko baya tare da ita, she will survive just fine!.
Sai dai, fadar, tafi aikatawar saukin fadi a baki. Duk da haka, tana kokarin kwatantawa.Zuwan Fairoz ya taimaka mata kwarai ba da gaske ba, itama nata bikin bayan nasu Sheerah da sati biyu. Dama Fadima da abokanta sune suke ta kai-da-kawowa game da harkokin bikin. Ko sau daya, kafarta bata taka wajen sayen kayan daki ko na kitchen ba. Fadima da Anty Siddiqa ne suke ta fama. Kullum suna daki ita da Fairoz, tana mata nasiha game da hakuri da yarda da kaddara. Dama ta riga ta dauki kaddarar ai, ta dai rasa yadda zata yi da rayuwarta ne kawai. Tare da taimakon Fairoz kuma, da nasihu da maganganunta sai taji komi yayi mata sauki, ta samu sanyi da amincin zuciya sosai.
Biki aka yi mai sauki, babu wata gayyar jama'a, kuma babu wata hidima ta sanya ciwon kai. Kwana biyu kadai aka yi ana shagalin biki. Kowa yaga amarya Sheerah dai a lokacin, yasan cewa bata maraba da auren ko kadan. Duk da cewa tayi kokarin ta nuna komi ba komi bane, hakan bai samu ba. Har aka yi bikin aka gama, bata ga yan Nigeria ko daya ya leka su ba. Zuwa lokacin kam, sai yan faint pieces na memories dinsu kadai a kanta ma. Bayan an gama biki, kowa ya kama harkar gabanshi aka kai amare gidajensu. Wata unguwa mai tsada, mahaifinsu ya gina musu flats guda biyu a jere, nan aka kaisu. Gidaje ne na alfarma, wadanda suka ji duk wata alfarma ta duniya.
Bayan an kai kowaccensu gidanta, anyi musu nasiha, kowa ya watse aka bar ta ita kadai. Kodayake, nata bangaren kadai ta sani, bata san abinda yake faruwa a gefen Fadima ba.
Ta kwashe fiye da awanni biyu zaune akan faffadan gadon da aka zaunar da ita akai, kanta a yane cikin mayafin da aka lulluba mata. Waje mai girma na mayafin, ya jike da lemar hawayenta data dinga sharewa. Bayan dogon lokaci dai, ta mike tsaye. Bathroom ta laluba ta shiga, bata tsaya karewa komi kallo ba, kawai tayi abinta ya kaita. Wanka, brush, tare da daura alwala ta koma cikin dakin. Ta bude wardrobe, cikin jerin kayan barcin da aka jera mata, ta zakulo wata silk gown, red, wadda tabi jikinta ta zauna mata sosai kamar her second skin. Ko ruwa bata saka a cikin bakinta ba, duk da cewa bata saka komi a cikinta ba ranar tun daga karin safe. Amma bata ji tana bukatar cin komi ba. Haka ta hau kan tattausan gadonta, da tsabar fargaba da tashin hankali ya hanata jin dadin laushin gado balle har tayi relaxing gabobinta.
Ko a lokacin, haka tayi ta juyi akan gadon kawai ba tare da tayi barci ba. Har zuwa lokacin, ta kasa wrapping cewa Moustapha ya yaudareta a cikin kanta. Gani take yi kamar kila idan ta rufe idanunta ta bude, zata ga cewa mafarki take yi.
Can zuwa tsakar dare kuma, lokacin barci ya fara daukarta, ta jiyo motsin taba kofa alamun za'a shigo. Taji zuciyarta ta hau luguden daka. Sai ta kara nutsa kanta cikin bargon data rufa a jikinta. Tana gani ta cikin bargon, yadda haske ya mamaye dakin. Bata yi motsi ba, don ma kada ta nuna mishi alamun cewa idanunta biyu, tunda tasan angonta ne kawai wanda zai iya gigin shiga dakinta cikin dare, a irin wannan lokacin.
KAMU SEDANG MEMBACA
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
SpiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...