Twenty Two

2.1K 264 24
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            DOCTOR SHEERAH!

                                         •°22°•



        Watanni uku cur da yin auren, babu abinda ya karu, kuma babu abinda ya ragu na daga cikin rayuwarsu. Abin har ya zama kamar wani routine. Zata yi duk shirye-shiryenta da al'amuranta daga rana zuwa dare, ita kadai a gida. Sau tari takan fita waje Shopping ko kuma bude idanu da zagaye unguwar da suke. Anan tayi kawaye, wata makociyarta mutuniyar New Delhi, Salaamat. Yawan zama da ita yasa ta fahimci abubuwa da dama game da auratayya da zaman aure, anan ta fahimci cewa ba karamin zaman cutarwa suke yi ita da Sageer ba. Ya maidata kamar wata sex slave, babu abinda yake hada su sai wannan kawai. Shima ba ta hanyar Allah da Annabi ba.

Rana ta farko data yanke shawarar mikewa ta kwatarwa kanta yanci, ba karamin dana sani tayi ba.

Kamar yadda ta saba yi kullum, da dare taje kwanciya ta saka lock a dakin, sai ta kara da sakata ta kuma bar key din a jikin kofar. Hankalinta kwance taje ta kwanta, musamman da taji lokacin da Sageer yaje ya taba kofar yaji ta a rufe. Tana jin alamun sanya key a jikin kofar, da yaga cewa ba zata bude ba sai ya tafi. Ta saki wani irin murmushi, wani sanyi yana sirarawa cikin zuciyarta. Barci mai dadi data manta rabon da tayi shi ya kwasheta. Sai dai na dan lokaci ne.

Kara kawai taji kamar na faduwar abu. A matukar firgice, zuciyarta na duka da karfi a kirjinta, ta tashi ta zauna a tsakiyar gado dangargar. Sageer ta gani tsaye a jikin kofa da wani katon abu a hannunshi, yayin da kofar dakin take yashe a tsakiyar dakin.

Kafin tayi yunkurin motsawa, yayi jifa da abin hannunshi ya nufeta a fusace. Hannu ya sanya ya janyota daga kan gadon, ta fada kasa kan carpet. Ya sake tunkararta, ya kamo gashin kanta da karfi yaja, ta yadda ya daga fuskarta suna ido da ido. Daga ganin yadda idanuwanshi suka yi ja, kasan cewa a matukar fusace yake.

Yace "ke har kin isa! A gidana? Kice zaki rufe min kofa??". Cikin rawar murya da nata kalar fusatar, itama tace "ai gidan ba naka bane! Na mahaifina ne!!".

Maimakon taga gwiwarshi tayi sanyi, sai taji ya kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya, yace "shi uban naki da yace ya sai mana gidaje, bai fada miki cewa da sunana ya saye shi ba? Yanzu haka maganar da muke yi, shi wanda kike ikirarin bai isa ya nuna min isa da mulki game da gidannan ba! Kina fahimtata?". Ya karasa fada yana sakin kanta, ta koma kan carpet din ta zube.

Binta yayi ya fara zare rigar barcin da take jikinta, aikinshi kenan. Da sauri ta saka hannu ta dafe rigar tana harararshi, tace "ka san Allah? Ka daina wulakantani a gidannan. Ina mutuntaka a matsayinka na mijina, dole ka mutunta ni a matsayina na matarka. Idan kuma ba haka ba...!".

Ya daga gira daya yana wani irin murmushi, da alamu ko kadan maganganunta basu dada shi da kasa ba. Yace "... Idan kuma ba haka ba? Me zaki yi??" tace "duk sai mu manta da komi kawai. Kaci gaba da harkarka nima inci gaba da tawa. Amma ina tabbatar maka da cewa, ba zan kara yarda ka kusanceni ba tare da amincewa ta ba!".

Sageer yace "inda kika yi kuskure kenan. Kada kiyi tunanin cewa akwai abinda nake bukata a jikinki, ko kina burgeni ne ko wani abu. You are just a play thing to me, baby. Ban aureki don radin kaina ba, ban kuma aureki don ina son aurenki ba, neither did I marry you don kiji dadin auren. You made my life miserable saboda aurenki da nayi, I'm just returning the favour!".

Hannunshi ta buge daga jikinta, ta mike tsaye tana karkade kayan jikinta tana harararshi. "you are sick! Kana bukatar ganin likita wallahi, ina kuma shawartarka da ka gaggauta zuwa ka ganshi...".

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang