🖕 Gaskiya Daya ce🖕

3.4K 133 2
                                    

🖕🏼Gaskiya daya ce 🖕🏼

✍🏽
Kulsum Bappah
Umm Iman
Wannan shafin
Sadaukarwa ne ga
Members na Mata Aljannar dunia
بسم الله الرحمن الرحيم

01
Borno yerwa birnin shehu

Allah ya miki Albarka,ya baki sa'a ya taimake ki,ya baki abinda kika je nima,
Amin Ammi kamar yadda kullum nake gargadinki ( usiki bit-takuwallahi azza wajalla)ina miki wasice da kiji tsoron Allah madaukakin sarki , matukar kika rike Allah kika ji tsoron shi tabbas ba makawa ya isar miki.
Insha Allahu Ammi nagode Allah ya kara miki girma ,ya tsare ki ya kareki dga sharrin magauta ,
Amin AISAH,nan Ammi ta zurfafa cikin tunani babu abinda yake damunta kamar magauta,kullum tana fadada tunaninta akan haka dama rayuwar aure haka take ko kuwa a nan nigeria ce suke da wannan Al'adar saboda ita dai tun tasowarta bata ga haka a gidansu ba duk da cewa mahaifiyarta ita daya ce a wurin mahaifinta , amma bata ga dangin mahaifinta suna ma wa mahaifiyarta hakaba hmmmm Allah daya gari banban ta numfasa,

Aisah tace Ammi ya kamata ki rage Yawan tunani insha Allah bazasu ci nasara akanmu ba ,bamu cutar dasu ba Allah bazai basu ikon cutar damu ba" Inna wa'adallahi hakkun" 'lalle alkawarin Allah gaskiya ne,insha Allahu
Maza tashi ki karisa wurin Abbunku ,kuyi sallama karfe hudu jirginku zai tashi,eh bari na hanzarta yana sashin shine ko na ganawa da iyalan shi?eh bansani ba ,amma dauko min wayata akan madubi na kira shi naji
Amincin Allah ya tabbata a gareka" yaa nur qalbeey, hasken xuciyata"tare dake qurrata ainee ( hasken idaniyata )ta lumshe idanuwanta masu tsananin haske da girma, ina saurarenki, Aisah ce zata tafi ,yaa salam "lahazain bas" minti 2 kacal tace "malaishh nantazurka" ba damuwa muna jiranka,
Hmmmmmmm Aisah taja numfashi iyayenta suna matukar burgeta yadda suke gudanar da rayuwarsu cikin mutunta juna ,

ya shigo ya same su ya zauna Nan kaltum ta zauna gefenshi ,Aisah ta zauna daga kasa ta dukkad-da kanta,tana sauraren abinda mahaifinta zai ce mata,
Nan ya cigaba kamar yadda kaltum ta mata nasiha, ya cigaba da mata nasiha mai ratsa xuciya game da gargadi akan mutunta kai tare da nusar da ita illar shigan banza da yan makaranta suke yi musamman yan jami'a da suke ganin sune iyayen kansu kasancewar babu idon iyayensu akansu ,duk da yasan tarbiyar da yabawa yar shi amma duk da haka yasan wajibine akan shi ya sauke hakkin da Allah ya dora mishi,
Aisah ta share hawayen daya gangaro mata tace da ikon Allah zamu kiyaye, yauwa yayanki HAISAM zai kai ku Airpot

Amminta ta umarceta da shiga tayiwa hajja kime sallama ba tare da bata lokaci ba ta nufi sashin hajja kime nan ta jiyo kanwaarta BINAZIR tana cewa Amminsu kullum kiyi ta tura mu gaisheta tana mana walakanci ,tana ganin kamar cusa kai muke yi a wurin ta ,Binazir ban hanaki, Aisah ta shiga hade da sallama fuskarta yalwace da fara'a da murmushi ,ta riga da ta saba tasan hali yar mulkin tana kwance akan doguwar kujera ,ko dago kanta batai ba balle tasan da ita ake, Aisah ta risina a gefen gadon tace hajja na shirya xan wuce , katsina Umma ta gaida Aisha ,Mtswww ,an koya muku kissa da iyaye ina ruwa na da tafiyarki,nan kanwarta yaana ta banko kofar bandaki ta fito sanye take da pitted gown abin ba fasali,kasancewarta wanda shafe shafe ya batawa fuska gata kakkaura, Aunty yaanah kina ciki,da yatsina ta amsa eh kina nema na ne, Aisah ta murmusa zan wuce ne,owk ta mike ta bar dakin, nan yaana take sanar da hajja kime zata rakasu kasancewar tasan haisam ne zai kaisu, mtswwww kin makalkale wa yaron da ba mutunci ne dashi ba karewa ma bai son kina yi ba,uhmmmmm hajja kinan ta ina burin mu zai cika ba tare da mun sheshige din ba ,ummm na tafi ta sure mayafi ta feshe jiginta da turarruka ta fita, binazir tana hanko ta ta fashe da dariya ,don tasan za,a rina

Amminsu ta raka su har waje yayinda suke sallama da Aunty yabi itace take zama da Aisah a katsinan dikko da yace daga cikin yan uwan Alh bukar malah ,mijinta ne ya rasu a wani hari da aka kai masalacin juma'a na 707 , tana gama takaba da yake Allah bai bata haihuwa ba Aunty kaltum ta jawota gidan kasancewar yabi akwai nutsuwa da sanin ya kamata ,sai tasu ta zo daya da Aunty kaltum ,

Haisam na mota yana jiransu ,kasancewar Abbu ya sanar dashi binazir ma zatai rakiya kawai sai ga yaana nan ya hade kamar ba shi yake kwasar dariya shida binazir ba ,saboda tasu tazo daya binazir akwai surutu ga bata da tsoro sam akwai ta da gwasalewa shiyasa sai mutum ya gama iyayenshi ta gwasalishi ,shima haisam haka yake ,ga surutu kamar yaci bakin kaza
Yaana ta dunfaru zata shiga kaban motar ya dakatar da ita,ya nu na mata gidan baya ,Aisah da Aunty yabi basu san abinda ake yiba binazir ce take kokarin kintse dariyar da take son kubce mata, yaana ko tayi fam kamar balo balo da ya timbatsa yake kokarin fashewa.........

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now