3:35PM.~~
Rayuwar Fadeelah
By
Hafcy Ahmad
📄01
Chan na hango ta tana tafiya, yar baka doguwa, jikin ta masha Allah. Tana da kyanta ba laifi , tana dawowa daga makaranta. Tana Ss2 art. Ita da kaninta me suna faruk suna takowa tare. Na matsa kusa naji suna cewa. Fadeelah tunanin mekike yi haka kina tafiya kina hawaye se kin fadi. Budan bakin fadeela seta ce mai bazaka gane ba dan uwa wllh rayuwan nan ta isheni. Kullun abu daya. Kullun Abbah fadan shi karuwa yake. Ga so da fifita abin duniya fiyeda komai, kaninta Faruk wanda taba shekaru 4 yace mata Anty hakuri zamuyi Allah na tareda damu. Har suka isa gida suna hira abinsu, suka shiga wani gida mai gate ba laifi da sallamah. Acikin gidan wata mata me shekaru da bazasu wuce 47 ba ta amsa musu suka gaisheta da Umma inayini, ta ansa lfy lau yarana andawo lfy suka amsa lafiya lau. Tace musu abincin su na kitchen kowa ya wuce dakin shi.
Fadeelah Ahmad yar shekaru 17 ne tun tana karama iyayenta sukayi hatsari suka rasu aka dawo da ita wurin kanin Babanta, Wanda keda suna Saidu suna cema Abbah. Malam Saidu su uku ne wurin iyayensu. Alhaji Ahmad ne babba sai Malam Saidu sai kanwansu mace Anty Amina. Malam Saidu Allah ya sa mishi son duniya da rashin addini, shi kwata kwata ganin shi ya mace batada amfani dan bazata kawo kudi ba, aikin gwamnati yakeyi a garin Kaduna. Ranan zeje aiki a state secretariat se ya hadu da matansa me suna zainab a hanyan sa sna dawowa. Zainab yar gidan Alhaji Saleh Mai shanu ne. Su biyu Allah ya ba babanta. Da ita da wanta Shehu, sukayi soyyayan wata uku sukayi aure. Bayan aurensu suka samu gida a kawo suna zaune.kafin ta haihu Alhaji Ahmad ya rasu, aka kawo musu riqon fadeelah tana shekara 3. Bayan shekara daya ta haifi Faruk murn wurin Malam Saidu ba a magana Dan beson yara mata, bayan shekaru biyu ta haifi yan biyu mata Wanda aka samusu khadijah da Maryam. Bayan shekara biyu kuma ta kara haifan mace akasamata Jamila.
Cikaban labari, sun gama cin abinci suka fito Sega yan biyu d Auta jamila sun fito daga daki da shirin islamiyah. Ita Fadeelah tadena zuwa islamiyah acewan shi tayi iya yanda zata amfana. Kuma. Bata kawomai kudi, sede taita ci, suma sauran yara matan suna kai shekara 15 ze ciresu, namijin kadai ze cigaba. Haka fadeelah ta shriya kanne ta suka tafi islamiyah, sega Abbansu yadawo tazo cemishi sannu dazuwa ya rufe ta fada., wai ba ta share gida ba Umma nacemai yanzu tadawo makaranta ai itama tasama nata wai ai dama kullun tana cikin goyon bayan yaranta mata. Bataso ace sunyi laifi nan ta jabakinta tayi shuru, yace tagama sharan ta wanke mai mota dan haka yake musu kullun da dacewa ci abincin dayasiya ya kuma biya musu kudin makaranta dole suyi aiki. Fadeelah nagama shara taje ta wanke mota, tashigo ta Daura girkin dare, tana girki ta wanke uniform dinsu ita da kannen ta ta shanya. Da magrib tana kwashe tuwo kannenta nashigowa daga islamiyah. Faruk ya shirya yatafi massalaci shiko Malam saidu yana falo yana zaune tunda bazuwa sallan yke ba. Yara matan sukayi sallah suka ci abinci. Jameela ta kwanta barci, Abbah ya kira fadeelah tazo ta tsuguna yafara mata fada shiyagaji bata kawo mai komai se cinye mishi abinci, tanemo miji tayi aure nagaji. Tayi ta kuka tanabashi hakuri amma ko a jikin shi. Ta tashi ta fito ta koma daki tayi sallahn isha'i ta kwanta., karfe 3:am ta tashi tayi sallolin dare, takai ma Allah kukanta. Washe gari da safe ta tashi tayi aiyukanta tashirya tafiya makaranta, tafito zata tafi saboda tayi latti su faruk suntafi sega wata Benz jeep yazo wucewa driver din su Alhaji Muntari, dayake suna gaisawa suka gaisa yace tashiga ya kaita shima yakai yara yadawo ne taki. Tacigaba da tafiya Sega wata mota Lexus tazo wucewa da gefenta tabi motan da kallo ta wuce. Ta isa makarantan aka Zane ta latti, sega Aisha bestie dinta tazo tana lallasshin ta, se Aisha ketambayanta lfy tayi latti? Setake cemata wllh abbah ne yasata aiki har tayi latti. Ta bata hakuri suka wuce aji.Rayuwar Fadeelah
By
Hafcy Ahmad
📄02
Aisha kawar Fadeelah yar'gidan Alhaji Tanimu ne, Babanta attajiri ne. Ita kadai Allah ya bama iyayenta, Babanta na sonta sosai bayason abinda zerika bata mata rai. Aisha sun hadu da Fadeelah ne a islamiyah, lokacin da Abbahn Fadeelah ya cire ta a makarantan shine Aisha tasa aka maida ta makarantan bokon su Fadeelah saboda su rika haduwa. Dan tana bala'in son Fadeelah, suna tare tun SS1 har zuwa ynzu. Wannan kenan.
A makarantan aka buga break, suka fito sukaje wurin canteen, shine Fadeelah take fadawa Aisha ance ta fitar da miji tana kuka, Aisha tace mata kiyita addua watarana sai labari, daganan Aisha ta sai musu abinci suka tafi wurin ci, suka gamaci su ka koma aji.
Lokacin tashi yayi suka fito suna komawa gida saurayin Aisha yayi parking suka tafi gaisawa dashi, ya kuke cewan Anas saurayin Aisha kuna lfy, lfy lau. Nan Fadeelah tayi gaba tabasu wuri, tana tsaye sega Lexus 🚗 din safen nan yazo sai wuce setaji Anas nacewa kai Hafeez se mota yatsaya. Wani kyaykyawan saurayine dogo fari yafito daga motan yana fitowa gaban Fadeelah yayi wani mummunan faduwa tafadi innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ya tafi inda su Anas suke suka gaisa, ya juyo yakalli Fadeelah yace wannan fa Aisha tace kawata ce tagaishe shi ya yi kaman bejiba ya wuce mota abinshi. Nan Anas yake CE musu Hafeez abokin shi a university dasuka yi a Turkey Baban shi babban mutum ne mekudin gaske, ita dai Fadeelah tace zata tafi lokaci na kurewa kuma tayi latti kar taje gida kawun ta ya dawo yamata fada ta wuce su tana tunanin Hafeez ko metamishi yaki amsa gaisuwanta kodan ita ba masu kudi bane. Ta iso gida ta shiga da , Malam saidu ranan anje aiki andawo da wuri yanda aka saba tashiga a hankali taga su yan biyu da jamila har sun dawo zasu ci abinci, Taje tazubo nata sukaci tayi shara da wanke wanke. Suka wanke mota ita da Faruk, kannenta suka tafi islamiyah. Yafito yace mata wai tatashi taje ta nemo me gyaran generator Dan dama nasu ya lalace, ta tashi tasa hijjab dinta tafara dawowa cikin kasuwan kawo tana cikin tafiya tana hawaye dan wurin mazane da yawa bekamata taje ba. Kawai setaji horn din mota ta juyo yayi parking setaga ya leko kai taga Hafeez ne. Ta gaishe shi ya amsa fuska a daure yace INA zuwa tace mai zataneman me gyaran generator ne, nan ya tsaya yana kallon ta yana mamaki yace tashiga suje tace Aa yaga alaman kuka take yace suje yarakata toh, suna tafiya harsuka iso wurin yayi sallama yace yana neman me gyara dazasu tafi dashi gida, me gyaran na juyowa ya ga fadeelah ya fara ce mata yarinya kece, har ynzu Baban ki baze dena aiko ki wurin nan ba ko. Ko dayake wannan ai kinxo da wuri se Hafeez yasa baki yace Malam kasanta ne yace eh mana nasan ta inazuwa gyara gidansu Babansu bashida kirki seya taci masu mutumci a gaban mutane, yace to muje mana yace bazashi ba saboda baban baya biya kudin gyara yanda yakamata seyace shi #200 ko dari uku ze bayar kuma se ya aiko Fadeelah nikuma tausayinta yakesa inkarba. Hafeez yace ze biya koma nawa ne suje, Fadeelah duk abinda ake banda hawaye ba abinda take cewa, suka kama hanya se gida Hafeez y shiga mota ya zauna jiran me gyara ya fito. Da sallama tashiga gidan zetaji saukan mari se duka ta ko ina, nan me gyara ya riqe shi waitaje karuwanci shine seynzu zata dawo, megyran ya bashi hakuri suka wuce wurin gyara yana gyaran Generator Fadeelah natsaye a wurin har aka gama taje ta karbo kudin gyaran takawo yace tabarshi yayi tafiyan sa. Fadeelah ta boye kudin ta, tajira dawowan kanne ta. Me gyara nafita ya hadu da Hafeez ya bashi labarin komai Hafeez hankalinshi yatashi. Yaba mai gyara kudi yayi gida.