3

1.4K 66 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

     🖕🏼Gaskiya Daya ce🖕🏼
       ( daga kinta sai bata)

✍🏽✍🏽✍🏽
    Kulsum Bappah
            Umm Iman
     Na kine wannan shafin.
   Fatima saleh
   Uma dala
Allah ya saka miki da mafificin Alheri

بسم الله الرحمن الرحيم

03
           Inna safiya ga kayayyakin nan kisa a store, Aunty yabi da fatan kunzo mana da mutum? eh garin dalayi ba har burabusko duk munxo dashi, wannan kuma Aunty kaltum ce tace a kawo muku, ki fidda shaddar mani driver da lado maigadi ,wannan Atampopin kuma nake ne ke da sholi, Allah sarki baiwar Allah bata gajiya da hidima ubangiji Allah ya saka mata,
      Ke sholi taho nan ga  Abin kullum nan  zabi wacce kike so,

     A'a inna sahiya  zaba min kowwace ciki Allah ya kara bude ya yalwaata mata   Amin suka amsa nan safiya tai waje da tsarabarsu mani da lado.
    
     Aisah na ida sallar magariba ta bukaci sholi tazo ta shirya mata wardrobe cikin kwarewa ta fara aikinta,
   Ta shirya kayan tsaf kowanne ta ajiye shi a matsuguninshi
Tana ta tunanin irin wannan sutura kullum ta tashi komawa bata daukan ko tsinke amma haka take dawowa  da wasu shake cikin Akwatuna, da yake uwar gijiyar tata ma'abociyar sa dogayen riguna tayi ta jirasu a hanger kowanne da mayanin shi.
     Nan taje ta kintsa na Aunty yabi ma.
   
            MUSCAT
       ( OMAN )
   Zaune yake akan lallausan zagayayyen kujerun wanda sukai kawanya wa falon kafet ne masu tsananin taushi samfurin kasar turkiya kalar tsanwan tattasai, labulayen kuwa kalar kwanduwar kwai kana ganin falon dole ya kayatar  da kai kasancewar anyi amfani da kalolin da suke jan hankali,  ga  3D wall paper  da ya maye gurbin pentin gidan gaba daya   ruwan zaiba ne adon jiki kuma  wato fulawoyin  ruwan goro ne  makeken TV ne inchi 62 sakale a jikin bango  yana ta aiki, matakalar kanta abin kallo ne an kawata  wurin da manyan frames na Ayatul kursiyyy can saman kuma inda zai sadaka da  mahadar saman console ne jibgegen gaske  da wasu tukwane na kasa da suka sha ado da kalolin penti daban daban , gaskiya wurin ya haska domin ya bada kaloli maban banta " combination of colours" baka jin hayaniyar komai sai ta na'urar sanyaya daki, hannun shi rike da mujallar Oman today domin shi kwararre ne wajen jin larabarai da sanin abinda ke faruwa musamman ta fanni da ya shafi kasuwanci na hada hadar man fetur

       Nan ya tuna bai kira Amminshi ba yinin ranar cur, laluba aljihunshi yayi yaga babu karamar wayar sai ya tuna ya barta a sama, hadiminshi talaal ya shigo da tire dauke da gahwa da dabino dan madina shar dashi ,   ya aiki talaal din yaje sama ya dauko mishi wayar nan  yayi sa'a kuwa  ya hangota akan madubi, bugu na daya na biyu kuwa layin ya kama Assalamu Alaikum ya ummi Alazizah suka gaisa cikin harshen larabci tare da tambayar shi iyayenta, "Kulluhum fi tamami sihha" suna cikin lafiya  Alhamdulillah, tace kunyi waya da Aisah kuwa don ta koma makaranta dazu kai bamuyi waya da itaba nan binazir ta karbe wayar ya Baanziye indawaatu, bata jira amsar da zai bata ba ta fara mishi rakadi a waya yace wai yaushe zaki nutsu ne muna cikin waya da Ammi kin amshe, yaya zancen makarantarki ce? eh da dama wallahi akan makarantar nan ne fuskarta ta sauya domin ya motso mata inda yake mata kai kayi domin Abbunta   sam yake ya barta taje dubai karatu, eh binan din Abbu hakuri zakiyi kinsan ba daga shi bane umurni ne daga sama, Mahaifinshi Alhaji Malah Sharif ne yace bai yafewa duk wanda ya tura masa jikanya karatu waje ba ko bayan ranshi ne bai yafe ba ,haka suka amince, shiya sanya bukar malah ya jajirce akan wannan wasiyar, ya ce mata ai nan unimaid ma ana medicine ga ABU zaria ma duk ta zabi yadda take so tai kuka har ta gaji saboda an kwafsa mata sun shirya ita da kawayenta dubai zasu tafi karatu amma ita an hanata bayan cewa duk cikin kawayentan babu wanda Suka kai iyayenta kudi dukiya, da suna gashi kawarta Iman har ta tafi. Baanxiye ya bata hakuri yace tabi yadda Abbu yake so insha Allah zata samu nasara a cikin rayuwartaTo nagode ga Ammin.
  Ta numfasa tace Badaar yaya zancenmu hajja kaka ta matsa kwana biyun nan da maganarka wai idan baka fidda mata ba zata sama maka, a dangi tunda char kuke da yan mata ko baka jinane kam? ina ji Ammi insha Allahu karshen shekaran nan zanzo sai nasan abin yi zan kira hajja kakar ma, kai ka sani ku karata can, sukai sallama ya lula duniyar tunani. Shi sam baiga wacce ta mishi ba domin shi mutum ne mai high test ba kowacce mace ce take burge shiba yana da wasu qualities da  yake so ya samu a wurin mace domin ko kadan a nashi tsarin bai son ya auri mai kiba irinshi yafi son mace yar shafal shafal wacce zata lafe a jikin shi

  
Muhammed badaraldeen kenan  da na fari a wajen Alh Bukar Malah wanda suke kiranshi da BAANZIYE chiwun   ( takwara ) Alh Malah sharif, garjejen kato ne baki ne sosai sai annurin musulunci kana ganinshi kasan cikakken kanuri ne  idan ba  don gashin kanshi ba baza'a taba cewa  ya hada dangi da larabawa ba, larabawan ma na oman, masu Asalin kyau da usuli hakoranshi farare tas, ga gashin gira a kwance luf hanci kuwa ya dauko na dangin uwarshi sak kamar zai shiga bakin shi, Alhamdulillah sai neman Abokiyar zama tagari.
  🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now