🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace🖕🏼
( daga kinta sai bata)✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Umm ImanYA HAIYU YA KAIYUM BI RAHAMATIKA ASTAGISU ASLIH LI SHA'ANI KULLUHU LA ILAHA ILLA ANTA.
12
بسم الله الرحمن الرحيمAbuja
Alh Bishir ne da kannenshi ibrahim da prof shehu sai kuma Bappansu kanin mal lawalli, mal hudu, wanda yake zaune da iyalanshi a Kauran namuda suna tattauna akan saka ranar auren kaunarsu, malam hudu yayi matukar farin ciki da yadda suka girmama shi basuyi gaban kansu ba, duba da yadda zamani ya canza indai akace kanada kwabo a hannunka shikenan kana zartar da hukunci, to shikenan,
Prof yace to Bappah wani lokaci ne kake ganin za'a tsaida musu?
Yanzu wani wata muke Ibrahim yace muna watan May watan biyar kenan,
Malam hudu yace
Kai watan musulunci nake fada ba na yahudawa ba, suka murmusa gaba dayansu, suka fara tunanin watan musuluncin ma a wani watan ake suka fara dibi dibi can prop yace Muna watan Rajab,
Eh hakane to inaga zamu saka shawwal da kwana 15 lokacin wata yaje tsakiya.
Sukai dariya Bishir yace hala akwai wani fa,ida wannan lokacin, 'a'a kawai tubarraki muke nema.
Alh bishir yace amma dai bappah zaka kwana mana 2?
Ni a'a, miyasa Bappah,
Barni na koma cikin iyali na kasan wannan Abincinku na birnin ba son shi nake ba musamman wannan mai kama da tanar, Taliya kenan ko?
A'a Bappah ina tuwon gero kake so dana dawa? Eh to ai nan ma akwai dawar sai a maka ita, yace wallah ba irin na gida ba, matan birni da suke abinci danye, a'a zamu juya yau dinnan , ko kana nan kai? A'a
To Bappah mungode Allah yakara lafiya,
Amin bari na kira maman su husna kuyi sallama.
Yace bishir da akwai hali dana koma da mota domin jirgin nan yana daga min hankali ,
Juwa tai ta damuna idan na shiga,
Ka ga wani hukuncin ubangiji lokacin da zan tai saudiya ban ji wannan juwar ba,
Bappah ai motar ce akwai dogon tafiya,
Gashi dama kana fama da ciwon kafa bazaka ji dadin motar ba,
Kayya wannan ciwon kafar kam ai abokin tafiya ne, sai fatan Allah yasa mu cika da imani!!
Suka amsa Amin
Ibrahim ya kaisu Airport
~~~~~~~~~~~~~
Alh bishir ya kira kaunarshi haj kyauta ya kwashe komai ya fada mata,
Tace yar bado ka ga niko ban san da zancen samrayen ba,
Aiko mamansu husna haka tace,
Hala kunya take ji, eh inaga .
Allah ya tabbatar da Alheri,
Zata shiga babban gida kam,
Ga su da bid'ia Auren su akwai wahala,
Ba komai karki damu da wannan
A'a ba wannnan ne damuwar ba,
Haba yaya ai zancen kudi ba abin damuwa bane,Ni ko kisan mi gwoggo tace?
A'a
Hhmmmm wai bikin uwarta yazo dukanmu wai sai mun mata gadaje dai daya wai bata daukewa kowa ba har prof shi da samunshi bai kai namu ba,
Ah lalle don wannan kar ta damu akwai wani iron bed ma da nagani anan na riga da na saye shi, har da husna ma yamin kyau ne gashi bani da mace,
Shiyass na saya musu.
Amma yanxu gadaje hudu bu suyi yawa ba?
Gane man hanya makaho yaso tsegumi.
Koda yake bari muga dakuna nawa sukai, eh to amma kasan fa suna yin gado wa uwar miji in dai ban manta ba,
Eh gaskiya ya kamata mu bincika,
Eh akwai I.G na police, dan maiduguri ne kuma matar shi kawar mamansu husna ce, zan sa ta tambayeta,
Yauwa to haka za'a
Allah fidda mu kunya,
Amin.
YERWAAlh umar ne zaune gaban mahaifiyar su, yana mai da musu yadda sukai da EFCC BOSS, ta waya ya shaida musu sun tsai da ranan shawwal, 15 ga wata.
Hajja kaka tace. Eh yayi yanxu shekenan sai asa su a lalle rana daya kamar yadda aka saka ku,
Don koda yake dai haisam ya girmewa baanziye,
Eh shi da yake mai karamin ruwa ne, ai baanziye kuma gaba gaba ne, ai shi haisam dangin mamanshi ya debo, baanxiye kuwa kaine sak umar yace wallahi ai jini kenan.
To yanzu ya kamata aje tambaya ko?
Gaskiya a satin nan ya dace a tafe amma Abujan ne ko can zamfara inji hajja kaka,
Inaga idan zasu mishi kara ya kamata A Abujan ne saboda acan hannun shi yace ta tashi,
Kadai tambaya muji,
Bari na barshi sai gobe,
Na tambayeshi zuwah Alhamis sai mu tafi zan kira prof ma owk usman eh ya shirya zamu tafi da Aminu mu dauke shi kawai ya jira mu a Airport kawai.Oh Aminu yace shi zai je tambayar Aisah .
Bukar yayi shiru gaskiya karaa da hadin kai yayi a rayuwa.
Yadda umar ya dage yana ta kai kawo akan hidimar Auren danshi ko maganar nashi baya yi.
~~~~~~~~~~~~~ALQALAM.
KATSINA
Lecturer din nasu bai zoba, suna zaune akan kujerun siminti dake kofar department dinsu, shafa take tambayarta lafiya ta ga duk ta zama wata silent duk da dama ita hayaniya bai dame ta ba, amma yanxu kam Abin ya kara lalacewa tace ba komai saboda taki fadawa shafa abinda ake ciki, don zatai ta zolayarta tai gum da bakinta,
Ta karashi rakadinta ta kyaleta,
ABUJA
Sun isa cikin Aminchi da salama motar managern gidajen mansu ne yazo ya dauke su, sun hadu dattijai sun hadu gemu da gemun sun hade huhun goro Ashirin da hudu suka kai chewing gum haka sweet haka da dubu dare 200 na tambaya, don da suna son yafi haka, sai hajja kaka taja musu kunne bata son wannan bidiar
Dan dole suka Amince da hakan
Alh Bishir yace gaskiya yayi yawa da kyar suka amsa.
Sannan suka ce A fadawa mutanen gida ango zai je gaisuwa kuma nan da sati biyu za'a kai wushe wushe.
To maddala Allah ya nuna mana gaba daya suka ce Amin don girman zati.
Shafa tana komawa gida taga ana kiranta da wata number wacce bata sani ba, bata dauka ba, bayan ta isa gida, tace Abinchi ta kwant chan ta kara ganin kiran har zata daauka sai ta bar kiran ya katse.
Chan taji sakon kar ta kwana ya shigo kamar haka
Ki dauki waya.
Ta ce waye kai.
Mijin ki ne!!!
Waye haka kuma?
Ki daga zaki ji ko waye!!!
Ban daukar wayar da ban sani ba. Ana haka sai ga wayar husna
Sis baki da mutunci.
Mi nayi haka.
Har asa date din biki babu labari bikin wa??
Ke kar ki min basaja
Husna ta kashe waya dama cikin fushi take, tana ganin kamar ta boye mata tun daga neman abin har ya kai da aje wurin manya ta boye mata,
Shafa ta shiga rudani,
Ta rasa wa zata kira, sai dabara ta fado mata, ta kira gwoggonta jikinta na rawa zuciyarta bugawa dam dam dam uwata kinyi goshi,Allah ya nuna mana Auren nan..........
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
عشوائيLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.