19

359 22 0
                                    

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
 
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼

(Daga kinta sai bata)

✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
     Kulsum Bappah
       Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

سبحنا الله وبحمده، عدد خلقه ورضه نفسه وزينة عرشه و مداد كلماته
SUBHANALLAHI WA BIHAMDIHI ADADU KHALKIHI WA RIDA NAFSIHI, WA ZINATU ARSHIHI WA MI DADU KALMATIHI.

19
       Shirye shirye yana ta kankama ta kowani bangare gidan mata na nasu gidan maza na fama,
Alh malah ya gayyato magina  kar kashin jagorancin ENGR usman daga yola suka. Zo suka baza bajintarsu ta zamani zamani da masu zane suka shata mishi yadda gidan 'ya'yan nashi zai kasance,
An kawata gini sosai magina sun zuba fasaharsu,
Anyi falo guda biyu da dakunan bacci guda 3 amma cikin falon maigidan daki dayan yake, sai falon matar gida da dAkuna biyu mu hadu a falo nata da na bakinta, kowanne da makewayi a ciki,
Alh malah ya zuba furnitures a dakin 'ya'yan shi kujeru labulaye, dai dai da Tv ya zuba musu,
Inchi 33 sharf  TARE Da C.D ,
Iyayen sauda sun zo ganin daki,sun nuNa bacin ransu akan yadda suka samu an zuba gado da kujeru a fannin mazaje,
     Sunyi aune aunen su na labule da kafet sun tafi,
Nan shatu ta tura kyallu gidan su yaa kime domin su zo suga gidan ba bata lokaci suka zo, sukai ta murnan an rage musu aiki,
Tun kafin subar gidan suke cewa yaa kime tayi goshi.
     Alh malah bai barsu haka ba sanda ya hada musu Kayan lefe na gani na fada,
   An sanar da Bukar abubuwan Alkhairi da ya musu, yace shima satin nan zai shigo,
A dakata zancen kaiwa kayan sai yazo,
    Bukar ya sauka tare da dirma dirman akwati set biyu, kala daya ba abinda ya banbanta,laces ne da zannuwa samfurin sheraton da vlisco na kamfanin HOLLANDAIS,
DA bugaggun shadda duk dan kamfanin SHERATON, Dogayen riguna samfurin TURKEY OMANI DA MALAYSIA, 
Hajja kaka ta dunga shi mashi Albarka saboda zumuncin da yayi,.umar ya gani yayi matukar farin ciki da yadda yayan nashi ya mishi kara.
Bukar yace a duba idab akwaai abinda babu. A karo.
  Eh inaga za'a karo kananan zannuwa irinsu cote D, voire   sai a kara da WAGAMBARI,
An kai kayan aure suna ta farin ciki da murna musamman gidansu yaa kime, da basu saba da kayan Arziki ba, sai gayar mutane suke azo aga yaa kime tayi goshi uwar kuwa habaici take tayi akan cewa yan bakin ciki sai su mutu jingirin yarta ya zama Alheri,
   Bukar ya koma OMAN ya sanar musu aure yazo sauran wata biyu,
Umair yaji dadi yace  amma ya akai kabar suwailim,
Nan ya labarta mishi yadda abun ya kasance, yace aure lokaci ne,Allah ya tabbatar da Alheri,
   To yanzu sai a fara gyaran side din da yake kusa da naku,
Yayi ta godia yace amma matar tana makaranta ne, acan gida,
Umair yace ba komai a dai gyaran idan tayi hutu ta ringa zuwa,
Yayi ta kwararo mishi Addu'a
Yace Bari zamu tattauna da Abbeey ( saalim Abdulhalim) muji minene zamu taimaka maka dasshi, yace ba damuwa nagode.
    Bukar ya kasa sanarwa uwargoyon shi ta Oman Zubaida kan cewa zaiyi aure sanda umair ya fada mata,
Taso ace umm kulsum zai aura saboda yanayin nagartarshi, da kuma yadda ta lura yana matukar kaunar diyar tata,
   Bai dai fada mata ba,amma ai shi IDO BA MUDU BANE AMMAN YASAN KIMAH.
Tabar abin a ranta,
    Aure yazo ansha bidiri da hidima zur'ar saalim Abdul halim sun musu kara Mota suka saya musu samfurin BMW, na Bukar ruwan bula yayinda na umar launin tsanwan tattasai ne,
   Zubaidatu kowa ba karamin tsaraba tai wa hajja kaka ba, jallabiyoyi na gani na fada da takalma masu tsananin tsada da sarkar DAHAM mai hawa uku ya kawo mata ashe ta fadawa Bukar yace wa hajja kaka tasa sarkan ranar biki zaauyi anko da takalman nan,
Kar kiga ruwan fitina a idon yan uwan Malah musamman wanda suke yi da shatu,
  Sai yada habaici suke, wai su ala tilas suna taya shatu KISHI,
  Zubaida dai ba jinsu take ba,sai ta fahimci ana mata kallon banza KO A JIKINTA A AN TSABIRI KAKKAUSA.
      SHATU kuwa kasa kwantar da hankalinta  tayi ta isa sashen mai gidan yana tare da baki, tai sallama tace ina son ganinka,
Yayi tsammanin ma ko akan hidimar bikin ne,
Suka haura sama, ko zama batai ba ta fara fadin
Ashe yanzu abin har ya kai ka ware hajja kaka kayi mata irin wannan sayayyar saboda za'ayi bikin 'ya'yanta kuma a fakaice da cewa tsaraba aka kawo mata,
To kasani bazan yarda ba wallahi sai ka kudi yanzu yanzu an sayo man wannan ai rashin Adalci ne,
Duk yadda na tsaya akan bikin yayanka amma kace zaka nuna wariy.......
Kafin ta kai aya ya daka mata tsawa,
Saurara ni akan mi kike magana,
Ta kwashe kayan da ta gani a jikin hajja kaka ta fada mishi,
Yace ashe  ke  shashasha ce,
    Kawai don kinga sarka a wuyarta sai kice ni na saya mata,
Kinsan halina tunda nake daku ban taba banbanta kuba, wani abin ma sai dai yaa kaka tace abar miki kin fita bukata badon komai ba sai saboda hakkin zaman tare da adalci,
Tab lalle fanna tayi gaskiya, an juya maka lissafi ( fanna kanwar Alh malah ce ubansu daya)
Oh su fanna din ne suka turo ki,
To daga ke har su zanyi maganinku, ku mata bansan daliliba maimakon idan kun girma kuyi hankali sai ku kara zama dabbobo,
Muhammadu nice dabbar?
Eh mi zakiyi?
  Tab ka nimo tsiya akan ka kuwa
  Sai na nuna maka ni dabbace,
Ta juya a fusace tai hanyar sauka,
Ki dakata!
Kika je kikai hayaniya ma kece da jin kunya,
Kuma ai wadanda suke zuga kin ma zanyi maganinsu,
Mtwssssss taja tsuka ta fita yaji haushin tsukannan amma da yake yau ranar farin cike ce shiyasa bai yanka mata ba,
Ya kirkiro murmushin dole, don kar bakinshi su gane,
    Yasa aka kira mishi hajja kaka,
Ta tsaya ta gaida vakin falon su saalim da umair kuma tai musu sallama tadan harhado larabcin da ake mu su a islamiya ta musu,suka haura sama da mai gidan
  Lokacin ne yaga irin sarkar da take sakale a wuyanta gashi tasha kunshi sai haskawa  take yi suka zauna ya tallabi hannunta kinyi kyau uwar angwaye,
Tai murmushi ai uwar angwaye kam SHATU  ce
   Hmmmmm wato bata sanma abinda shatu tayi ba kenan.
    Wannan sarkar kamar DAHAM?
EH,
Itace
ZUBAIDA ce daxu ta  dauko min wai muyi anko,
Ayya nasan ta wuce wacce na saya muku ta fitan biki girma,
Ka ga harda takalmin nan ma da jakar nan,
  Kai tayi kokari
Sosai ma
Allah ya biya su,
Amin kam.
Gani ance kana kirana,
Eh,
   So nake ki kiyaye duk abinda zaki gani ko kiji a cikin gidan nan,
    Lah ba komai,
Kece kike ganin ba koman,
Ki kau da idonki da kunnenki akan su shatu da yan DIKWA,
     TO Alh insha Allahu zan kiyaye,amma kar ka damu don ba komai ma,
  Tana fituwa daga shiyar maigidan tai arba da fanna.
    A'a su uwayen ango, yauma bazaki hakura ba ana hidima amma kina like da miji.
     Ta murmusa ta wuce kunsan abu mai ciwo kenan ka nemi fitina a kyaleka,
    Aishatu yayar su Bukar ta fito daga daki tana nemanta,
Suka karisa ciki.
Fanna bata so hakan ba,
tayi niyar ta
Ta tar watsa mata farin cikin amma sam bata kulaba,
   Shatu kuwa tana can daki danginta dana maigidan suna mata famfo,
Sai hawa take yi tana zama,
Lokacin daukan amare yayi dangin uba su fito su tafi suka ce:
Sun gaji a tura wasu,
nan hajja kaka ta gaane plan ne, nan ta sanarwa yan uwanta suka kasu biyu,
Suka dunguma gidajen amare,
Amaryar umar ce suka fara iso wa,
Aka sauke ta a fannin Alh malah ita da kawu nanta, maza matan kuma suka kare sa shiyarta,
Sai  yayar mahaifinta daya, suka danka amanar yarsu a hannun Alh malah da su eng usman da Dr Aminu,
Shiru shiru ana jiran isowarsu yaa kime ashe suna can sun kunna redio da sipiku ana jin kida🎼🎼  anan Alh mala ya tura Dr Aminu ya kira matan gidan hajja kaka ta iso ita da zubaida da yayyenta,
Shatu kuwa sanda ta bata lokaci kafin tazo tana ta shan qamshi,
    Akai addu'oi suka sanya Albarka nan malah ya umurci zubaida da shatu su kama hannunta sukai ta sashinta nan ENGR ,ya nemi da a tsagaita ajira isowar Amaryar BUKAR,
    SAI MUHAMMAD autan hajja kaka yace ai sun iso tuntuni kidan da kuke ji ma a sashen su yake fituwa,
Z ubaida ko taji ta fito sa tsaraban amare,
   Aka aika kiran yan uwan hajja kime da su taho da tasu Amaryan,
Ina har sun watse sai kawayenta, kawai har ta sunce LIFFAYAR da aka kawota dashi
Suna kwasan rawa, akai musu bayani,
Haka dai ta fito daga ita sai wani matsiyacin gyale wai ala tilas ace itama yar gayu ce,
  Kuma dama kawayen su kyallu ne, sai wasu yan cikin unguwarsu,
Babu dai tarbiya a yananin Tazo ta tsallake mutane tsagal tsagal sai gata a gaban shatu,
Ba matan ba har mazan abin ya musu ciwo,
Haka dai suka daure akai musu nasiha mai ratsa zuciya,
Hajja kaka ta dauki takardar filaye ta basu sannan zubaida ma ta basu sarkokin gwal tare da awarwaron su.
Nan ma shatu ta shaka wai wulakanci ne ai sai a sanar mata za'a yi kyauta a lokacin.kafin a umurce amaren da tashi tuni yaa kime ta fara gwada yan hannun tana cewa ya mata kadan.
   Tsabar mamaki sanda sauda ta dago cikin lifayarta ta kalle ta,
Aisha kuwa tace to malama kin bari ai abar gaban sirkayen naki ko,
Shatu tayi dariyar mugunta, DAYA KENAN, Tana ganin za'a tafi da ita kenan,
kyaleta gaskiyarta ai sai ta karbi abinda bazai mata ba,
  Zubaidan kanta ta fahimci akwai wani abu  amma da yake ba hausar take jiba sai ta kyale,
   Hajja kaka tace kyallu karba min sai a canzo mata ko a kasuwa  ne,
   Kyallu ta mika hannu tace a'a sai naga dahir.
Kunya ta kamawa kowa na wurin.
Akai maza aka kaisu sashinsu kafin ta kara kwafsawa,
Futar su keda wuya Engr usman yace kai Malah ina bukar ya samo yar tasha haka,

Yace bari kawai wallahi zabin muce,
Asan yaya kuka zaba mishi wanan,

Kamar ta hannun yar dakinka tazo,umar ya fidda mata shi kuma bai fidda ba shine shatu tai mana hanyarta,
Kai amma LAUJE CIKIN NADI.

wa kenan shatu mana.
Amma kuwa ai daga gani tarbiya ta mata karanci,
Inaga batai zurfin karatu bane?
eh inaga kamar batai secondary ba ma , a islamiya suka hadu da kyallu,
To kaga yanayin shigarta ma kamar bata da mafadi,
eh
  Illar kananan gidajen ke nan
    Amma kaga ita ta umar da yake yar babban gidace ai a nutse take
Ko kadam kar ka hadasu,
Ai graduate ce shiyasa
To Allah ya dai daita zaman  suka ce Amin.

KALU BALENKU JAM'A'À ANA ZAGIN YAN JAMI'A BASU DA TA IDO ( KUNYA) HAR ANA KYAMAR AURENSU TO KUN GA BANBANCI TSAKANIN MAI ILIMI DA JAHILI

🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

  🖕Gaskiya Daya Ce 🖕Where stories live. Discover now