💥HASKEN RAYUWA TAH💥 1

201 9 0
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥

By :Zeety A-Z💞

Wattpad@Zeety-AZ

Bismillahir Rahmanir Rahim!

Godiya marar misaltuwa ga masoya na, naji dadi sosai yadda mutane kebani karfin gwiwa akan incigaba da Rubutu, gaskiya banyi tunanin litaffi na nafarko zasamu karbuwa haka ba, inshaa Allah bazan manta daku ba☺.

*Allah yaqarawa annabi daraja,Amin*

📙01

Qiiiii...birki yake takawa iya karfin shi tareda yin salati amma duk da haka abunda yakejin tsoro sai da yafaru,gif! Faduwar yariyan kakeji akasa a take jini yafara fitowa a bakinta da hanci,damqe idon shi yayi yanata maimaita innalillahy wa'inna ilaihir raji'un, zuciyar shi bugawa takeyi kamar zata fito duka jikinshi bari yakeyi.
tsoron fitowa yaga abunda yafaru yakeyi, saidai bashida mafita don haka dolen shi ya fito, marfin kofan motan ya bude ya fito amma ji yakeyi duk kafanshi na bari kamar bazai iya daukan shi ba duk yafita a hayyacin shi kamar shi aka buge, ganin yadda jinin yarinyan keta kwarara akan kwalta shi yaqara gigitashi ya karisa kanta da gudu,yana zuwa bugun zuciyanshi yaqara tsananta don gani yayi yarinyan kamar harta mutu,gefe da gefenshi yafara kalla ko zaiga me taimaka mar su sata a Mota...amma saidai kash wajen yayi jejin da lallai Kaga koda tsuntsu ba saidai motoci masu wucewa, suma kamar an daukesu don tunda ya buge yarinyan har yanzu ba motan data wuce. Duk da bayajin karfi haka yadage ya ciccibi yarinyan ya bude bayan motan yasata,komawa yayi ciki yatada motan, juyawa yayi yana kallon yarinyan sannan yafara tunanin ina ma zaiyi daya? Juya kan motan kawai yayi yakoma baya tafiya yakeyi amma hankalinshi baya jikinshi ikon Allah ne kawai yamaidashi garin bai tsaya ko ina ba sai TH yana zuwa emergency yawuce da ita da gudu aka kawo gadon daura marassa lafiya akai, take doctors da nurses sukayi ca akanta don ganin halin da take ciki.Abu temakawa numfashi aka samata dasauri suke tura gadon shima yanabinsu da gudu har saida suka iso dakin daza'a shiga da ita don mata aiki aka dakatar dashi, suna shiga aka kullo kofan.

Kai komo yafarayi a kofan don duk tunaninshi ya kulle, tunowa yayi da wayanshi dasauri yaje mota yadauko,tsabar yadda hankalin shi ya kade yama rasa wazai nema ,numban maman shi yafara dialling batare da yasan mezai ce mata ba. sallama tayi taji shuru tace "yasir kana jina?" sai lokacin yace maa! Ido tazare kamar yana gabanta tadafe kirjinta saboda yadda taji tashin hankali acikin muryan shi ba kadan ba,cewa tayi nashiga uku! Yasir meya sameka? Badai accident kayi ba? Cikin rawar murya yace maa na kade wata yarinya...hawaye ne sukafara sauka a idanun shi,mikewa tayi tace yanzu kana ina? Muna TH yabata ansa a takaice, kashe wayan tayi tafito waje da sauri don duba Ahmad amma bata ganshi ba,Neman shi tafarayi a Waya yana dauka tace "Ahmad duk inda kake kazo yanzu nan karka bata lokaci, kafun ya tambayeta meye ne kit ta kashe wayan,shuru yayi modu ne ya dafa kafadan shi yace abokina meyafaru? Maa take nema na kuma hankalinta a tashe mikewa modu yayi yace kuma shine kake zaune? Maza katashi muje muga abunda yakefaruwa ba musu ya bishi mota yatayar acinki minti biyar suka iso gida saboda dama basuyi nisa ba,megadi na bude musu suka hangota a filin gidan sai sintiri takeyi,tana hango su tayi wajen motan, ido suka hada ganin yadda ta birkice amma sukasa cewa juna komai. bude motan tayi tafada tana cewa maza muje mu tafi TH ,zuciyan Ahmad ne ya tsinke yajuyo yace lafiya maa?waye bashida lafiya?atakure tace yasir ne yayi accident mu tafi Dan Allah karku batamin lokaci,kan motan yajuya suka wuce asibiti babu me iya magana acikin su,suna isa maa ta kira wayan yasir tun kafun suyi parking, tace kuna inane gamu acikin asibitin,a take ya gaya mata inda suke suna parking ta fito su Ahmad sukabi bayan ta,yasir na hango su ya taho da sauri hannu maa tabude mishi yafada rungumeta yayi kamar mejin tsoron karta gudu,bayan shi take shafa tana cewa its ok ya isa haka kaji we ar all here for u...dagowa yayi yace nashiga uku maa in yarinyan nan ta mutu.... sai hawaye Ahmad da zuciyan shi tayi laushi sosai ya tako a hankali yafara sharewa yayanshi hawaye yana cewa kadaina kuka yaya bazata mutu ba, hannu Dan uwanshi ya rike yana girgiza kai don bayajin zai iya magana, Ahmad ne ya ajiyeshi akan kujera yace kayi hakuri yaya ka kwantar da hankalin ka kaji. Maa ne ta zauna a gefen shi tace yasir ya akayi ka kadeta? Dago kai yayi da sauri yace wlh maa ba da gangan nayi ba, hannu shi ta rike tace ' nasani, inason kaban lbr ne koda hukuma zasu shiga ciki, hawayen idon shi ya share yace lokacin da na muku sallama na kama hanya ina isowa gamdu har na fara Barin garin na fara isowa jeji,banyi aune ba kawai ganin yarinyan nayi ta taho kan kwalta da gudu, duk yadda naso nayi controlling motan abun ya gagara saida na bugeta...ajiyan zuciya maa tayi tace Innalillahi wa'inna ilayhUr raji'un! Allah ya sauwaqe ya kuma tashi kafadan ta, duka suka amsa da Amin.

*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now