🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
بسم الله الرحمن الرحيمAddu'ar Tsoron Shirka:
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ أَنْ أُشْرِكَ بِكَ وَأَنَا أَعْلَمْ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا لاَ أَعْلَمُ.
Allahumma innee a'oozu bika an oshrika bika wa-ana a'lam, wa-astaghfiruka lima la a'lam.
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN
ALLAH YA JIKANKI HAJJA UWANI,ALLAH YA GAFARTA MIKI,YA KARBI BAKUNCIKI,
KU TAYA MU ADDU'A ALLAH YA YIWA KAKARMU RASUWA DA YAMMA NAN
21
Haka dai suka ci gaba da rayuwa abin sai ya sauya yaa kime kishi take muraran da sauda ita ko bata ma gane ba,
Ga masifar karya,
Kullum ta shiga side din sauda sai tace mata ke nimafa inada irin wannan fridge din yana gidanmu ba'a kawo min bane,
Amma kina shiga gidanmu zaki ganshi akan baranda, ayya to a dauko miki mana sai ki hada da wanda kika samu,
Akwai wata rana sun shirya zasu gidan Adda Aisha sai sauda ta dauke su a motarta
Suna cikin tafiya sai yaa kime tace babana sanda yace zai saya min mota nace ya barshi da lokaci,
Ya bari ba yanzu ba,
Haba to ai da kin bari ya saya miki ita mota tana da amfani akwai biyan bukata,
Eh haka ne fah,
Zan mishi magana to,
Ita kanta sauda ta lura akwai karya a hidimar saboda mutum da common blinder da zatai markade sanda miji ya saya mata,don lokacin da zata fara girki blinder ma bata da shi
Ta shigo da kayan miya wai tazo markade,
Saudat ta karbi kayan miyan tana markads mata sai tace,
Blinder tawa tana karkashin gado ne,
Kirjina ciwo yake yi, bazan iya dagawa ba
Au haba ayya,
Kusan sati kullum sai ta shigo ranar da kanwar sauda tazo sai ga yaa kime da kayan miya ta shigo ta fara iyaye wallahi naso yaukam naso da ga gado na dauko blinder ta,sai na tashi da ciwon kirji,
Ayya sanda aka gama markaden sai yasmeen kanwar sauda tace to muje mana na taimake ki, na daga miki katipar sai ki dauko kawai,
Lah kar ki damu idan Bukar ya dawo zan sashi ya dauko min a haba yanzu sai ki sashi ya dauko miki a'a ba girmanki bane ,haba ina!
Nan saudat ta kira yasmeen wuf yaa kime ta sulale
Yasmeen miye hakan ki kyaleta mana tai ta karyarta,
Haba Aunty saudat wallahi da kin barni kullum karya ai maganinsu ake yi,
Kyaleta zata gamu da dai dai ita,
To rufuwar asirinta daya ne ta fito zata sashin sauda markade sai ga Bukar ya fito.
Ina zaki da kayan miya a hannu kuma
Markade zani,
Baki da abin markaden
Ne ?
Eh,
Wallahi kasan kyallu tace wa iyayena kar asaya min komai saboda kun sai komai shiyasa basu saya min abubuwa,
Owk amma miyasa baki fada min ba da kika ga ba hakan bane?
Ba komai yanzu baki ganin abin kunya nee kullum sai kin shiga gidan kanina markade,
Muje naga abinda babu a kitchen din ,
Tofah sanadi kenan data lura Bukar bai da son kaskanci, ta samu lagon shi,
Komai sai tazo ta ce mishi ina son yi kaza amma bari na shiga wurin sauda, sai yace a'a kira muhammad ya sayo miki,
Suka sauka a gidan Adda Aishatu Al'adar sauda bata yadda ta hau kujera idan akwai babba a wurin,
Yaa kime ta dale abunta a saman kujera sauda ta dauki yar Adda Aisahtu tana mata wasa, ta fiddo da alawa dasu biscuit ta bata ta dauko turmin zani da turare da gyale mai kyau ta mika wa Adda Aishatu tace gyale da turaren dayan na yaa kime ce ta bayar ,
Adda Aishatu dai tasan kawai ta fada ne saboda ya kime sun fahimci macece mai son abinta ga wayon tsiya,
Domin Adda Aishatu a kwai ta da nazari lokacin da saudat ta fito da tsaraban yaa kime daure fuska tayi,
Sai da taji ance itace ta bayar ta washe baki,
Haka dai sukai ta fama yau wannan gobe wancan ,
Ko ina sai ta bakanta saudat kyallu suka hau tsangwamar saudat,
Hajja ta lura da hakan sai taja saudat a jiki sosai koda yake saudat tana da shiga rai saboda kyawawan halayenta na kyautatwa ga daraja mutane tasan yadda zata zauna da kowa
Shatu da kyallu kuwa kamar su jefa ta a wuta takanas sai kyallu da yaa kime suje kusa da windown ta idan umar bai nan suyi ta galauci suna tafawa. Suna jefarta da bakar magana,
Itako bata san da tashar suba,
Ana haka ranar umar bai fita ba kanshi na ciwo yana kawance yaji sun zo sun zauna suna da shewa sai daga baya ne ya lura da habaice suke wa matar shi,
Suna cewa
Kyallu na cewa oh nikam na rasa mi yaya umar yake da wannan ramammiyar ke sai kin ga kirjinta ma zaki san bata cika mace ba,
Mata sai tsayi kamar lisha cewar yaa kime
Haba ai kamar wata skeleton sai gashi da take fama dashi inji kyallu
Kamar wata sadaka yallah ba,
Yoo miye a jikin gashin idan naga dama sai na sa na doki
Kai yaa kime
Ni fah bata bani dariya sai taga mijinta idan tana kare raya kya ce karyewa zataii
Wai ita mi ladabi, don ma umar din naga baya kyaleta kinsan fushi ne dashi,
Hahhhhhaaa
Kyallu kenan to wani miji ne zai ji shawa'awr zama da ita.
Sai irinmu yan duma duma
Yan duma duma da basu da hali ko?
Kyallu kinji kunya indai har zaki iya hade baki da matar bukar ki ki matata ko kuma ki hada baki da matata ki nuna kiyayya wa matar Bukar babbar asara ce a gare ki saboda abinda yayi ni shi yayi bukar kuma shi yayi ke amma tsabar rashin sanin ciwon kai kike biye wannan jahilar don bata da maraba da jahila mai kwakwalwar kifi
Tabbas ko bulugari ce a haka nake son ta saboda iliminta, ladabinta biyyaya, uwa uba girmama iyaye na da sanin ya kamata da take musu,
Kinci darajar yayana wallahi,
Ke kuma zan gamu dake,
Kawai kyallu tasa kuka suka wuce wurin shatu wai umar ya zagesu ita da yaa kime
Eyyeh harda yaa kime lalle kuwa nan ta shirya karya ta sanar da yaa kime ta fadawa Bukar idan ya dawo,
~~~~~~~~~~~~~~~
Yamma nayi Buka ya shigo ya shiga gaida Alh da su hajja tana ganinshi tayo dakin hajja Bukar ka jawa umar kunne ranshi zaiyi matukar baci idan yana shiga har kar baiwar Allan nan iyayenta sun kawo ta Amana amma haka kawai an tsangwameta ko don ita ba yar kowa bace?
To kasani talauci ba hauka bane,
Idan yama kyallu na kyale shi bazai ma wa yaa kime na sa mishi ido ba,
Ta juya ta fita tana kwafa,
Hajjja kaka tace wai mi yake faruwa ne?
Yace wallahi ban sani nidai kullum yaa kime tana cewa wai mai dakin umar tana mata habaici da cin fuska akan Arxiki, bana dauka gaskiya ganin cewar matar nada sanin ya kamata,
Duk fa yadda zasu je ita take kaisu kuma Adda Aisha ta taba fadamin saudan na kai mata tsaraba sai taje dukkansu ne, kuma wallahi ko ni nasan cewa yaa kime kwabonta ba zai amfani wani, ba
Bukar kenan Alhamdulillah nagode Allah da ya nufa kanku a hade yake, su suke su raba muku kawu nanku dama tun farko da manufa tai auren nan duk fadin maiduguri ta rasa wacce zata aura maka sai yaakime bata san darajarmu ba babu kunya,
Na tabbata bazata bar muhammad yA auri itinta na,
Ko lokacin bana son nayiwa babanku gardama ne,
Amma kaka gaskiya ta fito ai
Ba komai ai nikam nayi kusan komawa oman ma,
Ah toh
Ga Abinci don yau dinma nasan ba girkin tayi ba anan suka ci da kawar tata,
Mtwsss kayi hakuri kowa da nashi kaddarar ba yadda za'ayi ace Allah ya barka cikin jin dadi dole sai ya jaraba ka domin yaga imaninka
Zai
Zaka gode mishi ne ko kuma zaka butulce mishi,
Haka ne,
Hajja na gode
Amma insha Allah Akwai abinda zanyi hajja lokaci nake jira,
To Allah ya muku Albarka
Ya ci burabuskon da miyar taushe da tasha ridi,
Ya tattara ya koma sashin shi yana isa ya tarad da yaa kime a cike idonta duk ya duje tsabar kukan munafurci
Shiko ko kallonta bai yiba ya shiga daki ya barta
Kayi ma wa kanninka kashedi idan ba haka ba zan mishi rashin mutunci bai sanni bane
Yaje unguwarmu ya tambaya wacece yaa kime
Nice wacce idan naga ana fada zan tara na shiga,
Kai lokacin ina dandali har fadan saye nake nema,
Ta karishi rashin hankalinta ta fita kala bai ce ba
Dare na yi yace tazo ta rakashi wurin hajja,
Ta na zuwa ta taradda umar da saudat suna zaune a kasa hajja na basu labari suna ta dariya,
Sai wani basarwa take tana ganin Bukar zai bi mata kadinta ne
Ya aiki umar ya kira kyallu da mahaifiyarya
Suka shigo a tare suna wani shan qamshi saudat ta gaishe da shatu da kyar ta amsa.
Bukar yayi guaran murya ya bude zaman da Addu'a yace abubuwa suna faruwa a gidan amma bani da masaniya akai sai yau mama shatu take fadamin
Shatu ta gyada kai kamar wata kadangaruwa
To maganar gaskiya yaa kime ki maimata min abinda sauda take miki na daga irin gorin arzikin da take miki,
Ta hau gifgifta mitsi mitsin idanunta kwarjinin umar ya hanata shera karyar,
Ta hau dibi dibi
Shatu tace ki fada mana abinda a gabana take miki
Sauda kuwa kallaon ikon Allah take don bata san abinda yake faruwa ba umar dai yace ta shirya su shigawa hajja hira,
Bukar ta tsinkayo yana cewa yaa kime ina so ki kwana da sanin cewa baki isa ki hada ni da dan uwana, kinyi kadan kinyi karya,
Akan yan uwata zan yi mummunan saba miki saboda har gobe bature bai hallice soso da sabulun raba jini daya ba bari na fada miki ''BLOOD IS THICKER THAN WATER,''
Ki sani BA'A TABA RABA HANTA DA JINI,
KI shiga taitayinki da kyau idan ba abin kunya ba har ki hada kai da kyallu,
Dakata Bukar
Ya juya yana sauraren shatu TALAUCI BA HAUKA BANE saboda sauda yar masu kudi ce shiyasa kake fifita ta akan yaa kime,
Kuma kayi kuwa dole ne su hada da kyallu tunda tare aka gansu sallamemme, kaninka ya shirya maka karya kabi ka dauka baka ga irin wulakancin da yake mata ba,
Yaa kime indai ni nake aurenki to ya isah yinin cikin gidan nan na haramta miki
Hajja kaka tasa baki tace a'a Bukar ai baza'ai hakan ba,
Ta dai kiyaye kawai,
Ta kiyaye mi?
Tab a dage ka a hanaka kuka haba hajja, NI kuwa da yaa kime NAN GANI NAN BARI FuREN TUMFAFIYA,
Kwarai kuwa mama inji kyallu
Tasssss
Umar ya zabga mata mari umurni nake baki ba nanda karshen satin nan KI FIDDA MIJIN AURE
kut me lesi sannu Alhaji muhammadu malah sharif ubanta,
Kwarai kuwa idan bata fidda miji ba ko a cikin masu gadin gidan nan zan aurar dake.muryar Alhaji malah taji
Kyallu ta zabura ta miki tsaye na shiga uku!!!!!🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
DiversosLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.