💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙06
** A kwana atashi yau yasir satinsu uku a asibiti, tunbasu saba harsun saba,tun yana zama ya zubawa fuskar Nihal ido harya fara magana shi kadai haka zai zauna yayita mata magana amma ko halamun farkawa batayi…
Ammie kuwa duk ta rame ta kode tun mutanen gidan namata habaici harsun gaji sun rage,gashi transfer Abban Nihal ya fito tare da promotion kuma harda gida aka bashi gashi yanzu zaibar aikin cikin asibiti zai fara koyarwa a school of nursing na damaturu.amma Sam yace shi bazai koma ba dakyar su bappah suka shawo kanshi ya yadda zaije saidai shima bashida kwanciyar hankali,yanzu nan da sai biyu zasu bar jama'are…en gidan su kuma sai gurmi sukeyi wai wayasan ma ko kungiyar matsafa yashiga don gashi daga batan yarinya harya fara samun arziki da cigaba nan fa magana yafara bin gari,Ammie kuma duk garin ya isheta Allah Allah ma takeyi subar garin ko zasu huta da fitinan mutane….
Khalifa tunda Nihal tabata bashida kwanciyar hankali babu megane mishi tundaga en gidan su har abokai, da Abba yace yagayawa iyayenshi suzo,kasa fada yayi saida Abba ya nemesu ya kuma sheda musu yadda yayi da khalifa ransu ne yabaci sosai donsu basusan ya aikata haka ba,sunyi kokarin baiwa Abba hakuri amma Sam yace a hakura kawai tunda dansu yajanye Allah ya hada kowa da rabonshi, dole suka hakura badon sunso ba...
Iyayen khalifa sun nuna mishi bacin ransu sosai harsanda yayita kuka yana neman su yafe mishi,baban shi yace su babu ruwansu kuma yayiwa kanshi ...
Tundaga ranan farin ciki yakarewa khalifa…tundaga abokanshi har en gidansu sun rasa gane abunda yake damunshi..yau ma kamar kullum yana kwance a dakinshi yana ganin yadda fanka ke juyawa saiga kiran babanshi tashi yayi yayi gyaran murya kafun yace hello daddy! Daga dayan bangaren baban yace maza ka shirya gobe kazo abuja akwai aikin dazaka tayani,kafun yace toh kit yaji yakashe bin wayan yayi da kallo…aranshi yace hakanma yafi don jajere baya mishi dadi yanzu ko kadan.
Yaune yasir yayi shawara da maa domin yanason su koma gida suci gaba jinyan a can,maa tace indai likitan ya yadda aiba komai tunda yarinyan batada ranan farfadowa gashi yanzu har watan mu guda a asibiti nan,kaga gwara mu koma gida inhada mata tare da rokon Allah ko Allah zaisa mudace, hmmm hakane maa yanzu bari nasamu likitan tace toh saika dawo, take yawuce office din doctor ya kuma ci sa'a shikadai ne, yana shiga likitan yace barrister yasir Kaine a tafe kanshi yashafa yana kokarin zama yace eh wallahi “dayake yanzu sun saba sosai da likitan harsun dawo kamar abokai” hannu ya mika mishi suka gaisa sannan yagaya mishi abunda ke tafe dashi. jinjinawa likitan yayi yace tabbas za'a iya sallaman Ku domin a yanzu haka batada wani problem kuma nasha mamaki ma da har yanzu bata farka ba ko don ba'a mamaki da ikon Allah amma dai har yanzu bamucire rai ba don dama masu irin wannan matsalan wani ma yanakai Rabin shekara ahaka wasu har shekara ma,don haka gobe zan rubuta muku sallama,kuma idan har kuna bukatan wani Abu zaka iya kirana sai kuma maganan alluran ta idan bukatan hakan yazo bansan ko akwai wani akusa dazai muku ba?ajiyan zuciya yasir yayi sannan yace badamuwa Ahmad ai medical student ne so inaga ba wana matsala he can handle that.. OK" doctor yace sannan yajawata farar takadda yayi wasu en rubuce rubuce yabawa yasir yace yaje phamarcy yasayo sannan sukayi sallama....
Washegari tun sassafe suka fara shiri, maa gana kuma taje gida tagyara musu tsaf tagyarawa Nihal dakinta nadaa kuma ta shirya musu girki kala kala.Bayan sungama shiri yasir yaja kujera gaban gadon ta ido ya kurama fuskanta nakusan minti biyar sannan ya Dan murmusa tare da lumshe ido sannan yabude yace, hi angel! Yau zamu koma gida hope u ar happy? Anyway I knw you will enjoy our sweet home because we have d most caring and best mum ever… maa ce tayi gyaran murya tace ikon Allah yasir din danasani dai da ko da mutane baya hira balle kuma dawacce ma bataji balle ganinshi..murmushi yayi yace a'ah maa kinmanta likita yace mana tanaji kuma watakila idan ana magana aka fadi abunda ta taba sani sai ayi dacen tashin ta,Dan kwalli maa take daura mata tace to kuma sai akacema turanci takeji dazaka sata a gaba kayita turanci kamar daga London, dariya yayi sosai har saida hakoran shi da dimple dinshi suka fito yace toh shikenan daga Yau zanfara mata Hausa,tabe baki maa tayi tace ai daganin yarinyan er Fulani ce sosai watakila hausan ma bataji sai fulatanci,yace kuma fa hakane,katse shi maa tayi da cewa maza tashi kaje ka duba mana likitan maa gana sai kirana takeyi sun matsu mu koma gida,mikewa yayi yana cewa ai muma mun matsu mu koma gida…
A hanya yahadu da likitan suka karaso tare yayi discharging dinsu karfe sha daya daidai suka isa gida, sosai suka samu tarba wajen su maa gana da sauran en uwan maa. Ankai Fulani dakin maa gana (sabo sunan da maa tasawa Nihal kenan). Ranan yasir yayi bacci sosai don dama kullum a gajiye yake yanakan sintiri tsakanin asibiti da gida gashi bai cika bari ana tayashi ba.
Su Ammie sun koma damaturu dazama…dukda damuwan rashin Nihal ko kadan bai fita aranta ba amma tasamu sauki daga fitinan mutanen garinsu don yanzu a quarters suke babu ruwan kowa da kowa..
Tsugune yake gaban babanshi kanshi akasa,cigaba yayi da cewa kadaiji duk abunda nagayama daga yau bazaka sake zaman jajere ba zakafara aiki da kamfani na anan don na lura gata ne yama yawa shiyasa kake kokarin sangarcewa, da wayonka da hankalinka da ilimin ka ace wai karasa wayanda zasu zugaka wai sai su ilu? Khalifa ilu fa, yaran dako kauyensu basu taba bari ba…kai kuma har waje kaje kayi karatu, jinjina kai dadynshi yayi yace gsky kaban kunya khalifa…tashi kaje inkaga dama kaci gaba da shashanci, babu abunda khalifa keyi banda gumi haka yatashi kamar kwai yafashe mishi aciki.
Kamar kullum bude kofan dakin yayi tare da sallama sannan yashigo, zama yayi a gabanta ya kura mata ido sosai kamar bazai kauda ba, sannan yasauke nannauyan ajiyan zuciya yace morning Angel! Hope u ar enjoying everything in diz house?murmushi yayi sannan ya rage murya kasa kasa kamar mesonyin rada yace bazan gaji ba harsai naga farkawan ki na maidake wajen iyayen ki kamar yadda nayiwa kaina alkawari…nasan dole iyayenki suna cikin tashin hankali kuma bazan so hakan ba,ki temakemu kitashi kinji baiwar Allah…maa ce ta bude kofan dakin tace toh inkagama saikazo ka karya karka makara.mikewa yayi yana cewa ina kwana maa tace lafiya yaron kirki maza kayi kafita don na lura inkana surutu da yarinyan nan baka son fita…har yayi gaba tace yauwa yasir inka tashi daga gun aiki kabi wajen malam bakura ka karbo mana addu'an yace toh.
Hoton ta yakurawa ido daka ganshi kasan yana cikin damuwa marar misaltuwa don ya rame kamar ba khalifa ba..mikewa yayi cikin hanzari kamar an zabureshi yacanja kaya yadauki key motanshi,tuki yakeyi kamar zai tashi sama ba tare da tunanin komai ba,saida yayi nisa sosai kafun ya tuno bai sanar da baban shi kamar zai mishi text sai kuma yafasa.Bai isa damaturu ba sai magrib kamar yawuce inda yakeson zuwa amma sai wata zuciyan tace mishi ko kajema bazaka samu mutane ba don dare yayi ,still tunani yakeyi ko yaje gidan baban shi ne da yake damaturu zai kwana amma sai wata zuciyan tace mishi kasan fa dole matarshi zata gaya mishi kazo kuma bakaso yasani…da wannan tunanin kawai ya wuce hotel.
*Abdlzty💞*