HASKEN RAYUWA TAH 7 & 8

67 5 0
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ





📙07 & 8


Washegari yana idar da sallah asubah Yakama hanyan borno bai tsaya ko ina ba sai kauyen da aka kade Nihal shiga cikin kauyen yayi amma sai yarasa wazai tambaya, tashan mota yanufa yaje wajen en union saida yamusu sallama sannan ya mika musu hannu suka gaisa yace Dan Allah tambaya nakeyi ko kun taba ganin wannan yarinyan ko lbrnta? Yana maganan ne tare da Ciro hoton ta a aljihunshi.

Karba sukayi wannan yakalla yanunawa wannan kaf sanda suka gani,shikuma duk yaqagu dajin abunda zasu fada,babban cikin su ne yace tabbas kamar watanni biyu da suka wuce ankawo mana hoton wannan yarinyan ana Neman iyayenta, da sauri khalifa har jiki na rawa yace Dan Allah kunsan wayanda sukazo nemanta?

Mutumin yace police officers ne, shuru yayi sannan yace ko kunsan daga garin da suka fito?kada kai mutuminan yayi alamun a'ah sai wani yace inaga fa police din Maiduguri ne don nagane daya acikin su...


Godiya yayi musu harya juya zai tafi sai babbansu yace bawan Allah! Juyowa khalifa yayi don sauraren shi,yace meye halakan ka da yarinyan? Kai tsaye yace mishi kanwa tace, mutumin yace Allah yasa kusameta Amin yace Daga nan yasa kai yawuce.

yajima yana jingine jikin motan shi yana tunani don gaskiya bazai iya tunkaran police station akan case din Nihal ba, kuma idan iyenshi sukaji yace musu meye? Da wannan tunanin yakama hanya ya juya…

damaturu yakoma Ammie Nihal ce tafado mishi don yaji sun komo nan da zama…tunanin yadda zai samu address din su yafara, wani cousin din shi yakira yafada mishi address din, direct gidan yawuce dukda zuciyan shi tanajiye mishi tsoron haduwa da Abba amma babu yadda zaiyi don a halin yanzu jiyake kamar yafisu yin dashi,kamar zai iya mutuwa sanadiyan ta, sai yanzu yagane Ashe Nihal haske ce a rayuwar shi…


Yana isa kofan gidan fitowa yayi zuciyan shi na mishi matsanancin bugu ya nufi kofar gidan.
Nock nock nock! Ya buga daga ciki yaji ance ana zuwa,baifi minti biyu ba aka bude kofan gidan, ganinshi ne yasa ta yin baya da sauri don ta tsorita, rike kofan tayi sannan tadake tace mishi lafiya?

Kawai ganin shi tayi ya zube akasa yahada hannu shi,yace Dan Allah Ammie kiyi hakuri ki saurareni nasan ni me laifi ne agareki badon halina ba Dan Allah kuyafe min, kallon shi tayi da kyau tace Abban Nihal yakusa dawowa shawara nake baka dakayi saurin Barin nan kafun yazo yasameka…


Kuka ya rushe mata dashi kamar karamin yaro, Dan Allah Ammie ki temakeni wallahi bazan rayuwa babu Nihal ba,mutuwa zanyi Allah nagane kuskurena kuma Nihal itace HASKEN RAYUWA TAH!

Sake baki tayi tana kallon shi tace yau naga ikon Allah to indai akan Nihal kakeyin haka to ai muma bamu ganta…katseta yayi da sauri…. Wallahi na miki alkawarin nemo Nihal bazan tsaya ba harsai nasamota Dan Allah kiban izni Ammien  mu….

shuru tayi don yafara kashe mata jiki, kuma dama yanzu bata da weakness din daya wuce Nihal…nisawa tayi kafun tace kadaina wannan katashi idan Abban ta yadawo zangaya mishi duk yadda mukayi zakaji, amma yanzu kayi hanzarin tafiya don ya kusa dawowa…

tashi yayi yana godiya ya nufi motan shi bata shiga ba saida taga tashin shi…ji tayi duk jikinta ya mutu don yataba mata inda yake mata kyaikayi kuma yafara bata tausayi.


Kamar ko wane weekend don sun maida hakan kamar al'ada tunda suka dawo daga asibiti, ko qane weekend a dakin Fulani suke har sai dare kowa yake tafiya yauma suna zaune akan sofa dakin maa kuma nakan kujera sunata raha kala kala, modu ne yaketa basu labaran abun dariya, sai dariya aketa sha maagana harda hawaye.

Kafan Fulani ne yayi motsi…kamar a gizo yasir yagani, yatsan shi yasa akan baki yayi musu shshshhh.. Shuru sukayi sai ya nuna musu kan gadon, shi yafara tashi duk suka bishi kanta sukayi kowa ya tsaya,maa ce tace yasir meye ne? Duk kataso mu, nuna mata fuskan yarinyan yayi…ai kuwa kamar a mafarki gani sukayi kallon su takeyi daya bayan daya, maa tasamu waje a bakin gadon tazauna tace Alhamdulillah, Allah Kaine abun godiya, mika mata hannu tayi tace tashi ki zauna Fulani, FULANI? Sunan ta maimaita, ba musu maa ta temaka mata ta tashi.

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now