Tnx for reading.this chapter is all urs💌💌💌
Note: not edited
***Bayan sallah
Ranar ukun sallah muka shirya don dauko su Asmah don su gaida iyayen mu. Sai da muka nemi izinin baba sannan muka sa Rana.
Yadda Amma ke shiga da fita... Wannan shu'umar yarinyar suwaiba ma Sai wani shiga da fita take ko an Gaya Mata qawayenta za'a kawo oho Ni manta wa ma nake da ita kullum cikin daki take Yau Kuma gata sai rawan Kai take. Sai da muka yi la'asar muka je. Leshin da Amma ta musu na sallah shi ne a jikin su, sun yi kyau sosai dinkin ma modest don irin Borno style din Nan ne. Bamu dade ba muka iso cikin gidan mu. Side din hajia muka fara yi wadda ba yabo ba fallasa ta amsa musu gaisuwar su amma daga Nan Bata qara kallon inda muke bama balle ta tambayi wacece Hauwan. Ameer ne ya ce mu je wurin Amma muka dunguma bayan mun Mata sallama. A falon Amma muka tadda ta rungumar su tayi Daya bayan Daya, Ameer ya zauna kusa da ita tsabar Jin dadi. Suka gaisa Asmah kunya sosai take ji. Suwaiba ta gaida su cikin nitsuwa da girmamawa Ni da Ameer muka kalli juna muka yi dariyan da ba Wanda ya ganmu. A haka aka gabatar da abinci sinasir da waina da miyar taushe sai rice and stew din kaji ga wani lafiyyen zobo ko ranar sallah Amma Bata min irin wannan tarbar ba daga idi. Suwaiba ta zauna kusa da su ta ja su da Dan Hira har ta sa musu abinci. Amma da ta ga kunyan ta suke ji sai ta bamu guri. A haka suka Dan taba abincin dai. Amma ta dawo aka danyi Hira sannan muka Yi niyyan maida su gida,Nan ta bawa kowacce dubu goma sai ta ba khalifa dubu uku muka Yi godiya Baki daya. Daga Nan side din hajia na ce mu koma don Yi wa hajia sallama ba da son ran Ameer ba. Haka dai ta sa Mai aikin ta ciro wani box daga fridge na chocolate ne ta baiwa khalifa matsayin goron sallah,mu kayi godiya sannan muka wuce tudun wada. A kofar gidan magriba ta riske mu da haka mukayi sallama muka koma gida.Soyayyar mu da Asmah yayi qarfi don bana iya awa daya banji muryar ta ba. Komai nawa ita haka ma komai nata nine. Kullum qara shaquwa muke don yanxu Ni a ganina ta fi kowa sanin lamura na.
Gidan dai na malali na samu saboda nayi contacting agents din amma suka ce an fasa sayar wa saidai rent. Gidan ya min kyau sosai duk da bana son rent amma I'll have to get this. Duplex ne 3 bedrooms a sama da parlor sai parlor babba a qasa da quest room sai kitchen babba sosai da store a qasa da dinning room.balcony din sama ma is something to look at, I know I can't buy d house gaskia. #1.2 ne rent din sannan na two years suke so. Haka na fada wa Papa ya bani na biya Cox he offered to pay. Gidan Ameer Kuma a unguwan rimi Papa ya saya mishi #35mil. 3bedrooma da parlor da kitchen da BQ everything is good amma ya danyi renovating. Amma Papa ya min Alqawarin gida in har na samu.Munyi making parlor na qasa cream colour da touch of blue sai parlor na sama ash kawai. Sweet homes interior na sa suka tsara Mana gidan mu sosai. I spent almost 5mil Akan interior din gidan duk da Asmah na taka min birki. Gidan yamin kyau sosai tunba ma parlors din ba
.
Na dauki Asmah da khalifa muka je ganin gidan itama ya burge ta sosai
ŞİMDİ OKUDUĞUN
Life Person💞 -Hausa Story
RomantizmAllah kadai ya San jiya ya San Yau ya Kuma san gobe. A love story with a simple setting. Each and every swt story has a certain rough instance let's see what happens here. Alhamdulillah