Abeesh
Dan ladi yace yi hakuri baaba,saratu Dan me sama kivar yarinyarnan ta xauna kinga koh wankau da aikatau seta dinga miki
Saratu ta danyi jimm tace toh hikkenan maye nasan idan ban yadda bah haka xaka yita takuramin tanayi tana yatsine fuska ,shiko Dan ladi sunkuyar da kaii yayi
Ke dahare kike koh wa?daga rana irin ta yau zaki fara wankau, kinajina, Abeesh tace ehTun daga ranar Abeesh da sassafe zata tashi tayi shara, tayi wanke_wanke, tayi wanki
Abinci kuwa se wanda aka bawa baba jummai suke lallasawa, sbd abincin a dai cine Dan befi loma biyarba
Baba jummai tana zuwa Kasuwa tana siyarda kayan kadi, inda idan ta samu 'yar naira ashirin seta bawa abeesh wato shatu
Setace koh bayan raina ki dauki kudinnan kije tasha ta kaiki Garin NIJER koh Allah zesa ki gane garinku, toh kawai Abeesh take cewa, gidan wata wadda mukai aikatau tare zaki sauka, sunanta barira inda inada yakinin cewa zata taimaka miki idan kinje, toh abeesh kawai tace
A kwana a tashi yau ya Kama asabar inda Allah yayiwa baba jummai rasuwa, inda saratu ta ceh ae abeesh ceh ta lashe baba jumman ,Dan ladi kuwa ya hau ya yadda ,har yana XE kira yan sands su Kama abeesh
Dama bana fada muku bah dama nace muku mayyace,
Ta rufe abeesh da duka abeesh dataga ba haza ta shige daki ta dauko kudin da babajummai ta keh bata, da gudu ta ficeh daga gidan
Kasuwarda baba jummai ta keh zuwa taje sbd wata ranar tana zuwa da ita,
Wani tsoho ta gani tace dan Allah inane tasha
Bayani Yamata tace nagode, dataje tashan ta hau motar zuwa birnin NIJER
Bayan sun isa ta sauka daga motar ta rasa inda zatayi, zama tayi a wani tudu ta dinga kuka
Mutane da suka ganta zata sukayi mahaukaciya ceh, sbd yanayin shigarta
Takalmi daban _daban
suma din na baba laure nehKaya sunyi budu_budu gashi hijabin jikinta a juye duk jurwaye a jikinsa
Tana Nan zaune har magrib
Mu leka wurinsu Dr Affan
Tun ranar da abeesh ta bata, mama kullum kuka, Affan kuwa shima duk jarumtarsa kuka yake zama yanayiwa mommy
Kullum kuwa se yaje gdnsu abeesh yaji koh da wani canji, Abuja, kaduna bbu inda baa baza neman abeesh bah
Gashi ynx watan abeesh 7 da bata
Affan rashin lfy ya fara, kullum kuwa ba sauki da daa gaba rashin lfyr ta kehKullum cikin kiran sunan abeesh yake, wani idan ya ganshi seya zata ya tabu neh
NIJER
Abeesh tana zaune tanata kuka, wanine yazo wucewa yace baiwar Allah meke damunki?
Ki wuce ki tafi gidanku mana kinga magrib hartayi, ya sunanki?
Abeesh tace sunana dahare kuma banida gidan da zanje sbd baba jummai ta mutu kuma ita kadai ke garenii ta qara fashewa da kuka, baba jummai tace inje gidan baba barira kuma bansan ina gidan yake bah
Yace tooooh🙉
Nasan tabbas kinada wasu 'yan uwan,koh number wasu haka,abeesh tace banida , daga ina kike, tace daga kauyen mazo ,yace kixo in maidaki toh nasan halan yan uwanki nacen tace banida yan uwa kuma idan nakoma baaba saratu kasheni xatayiWani irin tausayi tabashi ,yace idan bazaki damu bah kizo na kaiki gidanmu nasan ummana xata riqeki da Amana,idan yaso se mu fara neman baba bariran daga baya