💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙16
Yau asabar Nihal da ya yasir zasu kaiwa maagana ziyara amma banda Ahmad saboda sunfara exams ya koma ma cikin makaranta dama haka yakeyi idan exams ta kusa sai ya koma cikin school, wannan karon ya matsu yakoma cikin skull din saboda Nihal yana ganin kamar yawon kallon ta zai iya hana shi karatu shiyasa ya tattara ya tafi.saidai fa kamar ya kara tayarwa da kanshi hankali ne don Nisan tan ta shiyafi komai tayar mishi da hankali, duk da suna chatting ya daura mata WhatsApp a wayan ta don haka yanzu kullum suna cikin chatting da video call.
duk yadda bena takeson kauda kai abun yagagara don ta fahimci akwai shakuwa sosai a tsakanin su ita babu abunda tatsana kamar taga wata tana kokarin raban Ahmad.
Saida suka fito zasu tafi ne takira Ahmad yana ganin call dinta murmushi yayi yai picking tare da sa wayan a kunne shi..dataji shuru ne tace ya Ahmad sorry na tasheka a bacci ko? Lumshe idon shi yai yasa hannun shi a kirji don ji yayi bugun kirjin shi ya tsanan ta saboda tayi maganan ne cikin shagwaba,hello tasake cewa saboda jin shuru…a hankali yace bakin shareni ba tunjiya da dare nake Neman ki baki dauka ba kuma baki hau WhatsApp ba…itama murmushi tayi tare da cije leben bakinta tace kayi hakuri yaya na jiya nayi bacci dawuri ne..yace da safe fa? Tace ya Ahmad ka yafewa kanwar ka mana…yace ainaga kamar kanwar tawa bata gane yayanta yana missing dinta bane…no ya Ahmad wallahi nima ina missing dinka,hmm nifa nagaji ingama jarrabawan nan indawo gida…tace gaskiya gwara kadawo don muma mungaji da rashin ka…ga bakinta kamar dagaske,dariya tayi tare da rufe bakinta kamar yana kallon ta,tace yanzu dai guess wat,yace meyafaru…tace zamuje gidan maagana ne nida ya yasir murmushi yayi yace shine zakuje bazaku jirani bako,no ai kaima inka dawo sai mukara zuwa ko..umh toh shikenan amma dai ki kula da kanki kinji…tace toh zan kula yaya nah.
Saida tagama kafun tashiga motan,ya yasir ya juyo yakalleta yace kingama ne er shagwaban yaya dariya tayi tace ina missing din yaya Ahmad dinane…
Tada mota yayi yace masu yaya manya….tafiya sukeyi Nihal kuma sai surutu take mishi har suka isa…tundaga window maagana ta hango su bakaramin dacewa taga sunyi ba a idonta,tahowa sukeyi tana ta mishi tadi shi kuma sai dariya yakeyi gwanin sha'awa.
inshaa Fulani rabon ya yasir ne,may b shiyasa Allah yakawo mana ke maagana ce take magana aranta...
Shigowa sukai tare da sallama maagana ta amsa musu tanacewa ahh lallai yau munada manyan baki a gidan nan,ya yasir ne yace Ashe dai kina kusa tace eh wlh yanzu na shirya yara suka tafi islamiyya shiyasa,ku karaso mana bismillah Fulani kin tsaya saikace wata bakuwa,murmushi tayi tasamu kujera tazauna maagana ta kawo musu abun motsa baki,nan suka yini har yara suka dawo daga islamiyya itakam ta koma hidima da yara tabarsu sunata tadinsu…har sai dare suka tafi da sukazo tafiya yaran suka dage saidai anty Nihal yau ta kwana a gidansu dakyar ta lallabasu suka tafi.
Washegari bayan sun karya Yusuf yace mishi ya shirya suje wajen malamin ba musu khalifa ya shirya suka tafi,sunje sun sameshi sun mishi bayani shima sosai abun ya girgiza shi,yace amma farin cikin shi daya da khalifa yagane gaskiya kuma yakeson yabar kungiyan,addu’o’I ya baiwa khalifa sosai kuma yace kar yayi wasa dasu inshaa Allah, Allah zai temake shi sudaina bibiyan shi kuma yadage da karatun Qur’an da ikon Allah komai zai daidai ta,godiya suka mishi suka koma gida.sosai khalifa ya dage akan addu’o’in da aka bashi kuma harda Yusuf dinma sukeyi tare,saidai khalifa tunda yafara yakeyin mugayen mafarki…sai yayita ganin en kungiyan sunzo sunason tafiya dashi, amma ko a mafarkin ma addu'a yakeyi su watse…
ranan daya cika sati yana addu'an ranan yayi mafarkin duk sun mutu…yana fara addu'an yaga suna ta faduwa wasu na rugurgujewa haka har suka bace,da safe daya gayawa Yusuf, Yusuf cewa yayi maza suje su gayawa malam,sunje sun sannar mishi yace Alhamdulillah in Allah ya yadda akwai nasara, saidai kuma kar kaga ana samun nasara kace zakayi sakaci da addu’a,yace inshaa Allah malam bazanyi ba,Yusuf yace mungode sosai malam Allah yaqara nisan kwana yace Amin.
Kamar kullum yauma Nihal tana kwance a gado suna chatting da ya Ahmad sai murmushi takeyi bata Ankara ba kawai taji anfado kanta saida ta tsorita daga kan dazatayi kawai taga yaran maagana ne..nan taho musu oyoyo suko sai tumur musheta sukeyi yaran bakadan ba suke son Nihal,maagana ce ta shigo tace lallai aiki yasa meki kema Fulani,yau fa su suka damemu akan dole sai munzo wai kince musu zaki dawo kuma baki dawo ba..dariya tai tace ai ya Ahmad nake jira yagama exams sai muje tare..baki maagana ta tabe tace mukam bazamu iya jiranshi ba don haka dole yau ki shirya mutafi ko zarah? Karamar erta take kallo Zara tace eh mama.
yaran maagana uku ne babban sunan shi sayyid yanada shekara 7 sai sayyada tana da shekara biyar sai zara me shekara uku itace karama.
*Abdlzty💞*