🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
🖕🏼Gaskiya dayace 🖕🏼
[ JIRE TILO](Daga kinta sai bata)
✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
Kulsum Bappah
Ummu iman
Follow me on wattpad
@kulsumbappah.facebook @ukb696354.kb@gmail.com
🦚🦚🦚 *UNIQUE ONLINE WRITER'S FORUM*🦚🦚🦚
_(Home of Extraordinary, Uniqueness, outstanding, special and Remakable Writer's)_ 👌🏻
Wanda Ya yi Mafarki mara kyau.أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)39
Jidda ce tace
Aunty yaana ya za'ayi kice bazai yuwu ba shida matar shi ta sunna
Nan yaana ta ankare ta tuna da irin katobarar da tayi,
Sai ta wayince da yake yar dunia ce domin ita yaana har tafi yaakime barikanci ko don ita tana makaranta ne
Ta shiga dakinsu wurin Auntynta
Yaa kime ta ganta a wani yanayi lafiya kike kuwa ?
Da sauki
Kinga abinda haisam yayi kuwa a gabana anya bokan nan kuwa da gaske yake yi,
yace fah sam zai kashe mishi karfin mazakutar shi amma abin mamaki dazu naji binazir tana bawa jidda labarin wai ya dawo unguwa ya wuce daki wai can sai gashi nan dauke da Aisah ya mata wanka wai tsabar rashin mutunci har da tambayata wai ko bansan wankan janaba bane,
Shegiyar yarinya kenan ai wannan da kike gani da gwara gwaran idonta kamar na uwarta nan ba cikakken mutunci take dashi ba
Aunty duk gidannan ba wacce na tsana irin binazir
Ke ko ni ai wallahi da Alhaji zaiji maganata da auren ya mata itama tunda har tasan wani abu shi wankan janaba,
Yanzu Aunty inaga zan koma TSATSUNBUR Inje in sanar da boka abinda naji
Ki hakura kiga gudun ruwansu tukunna mana
Haba Aunty ga zahiri nagani,
Yaana hanyarce ba kyau ,
Eh hanya ba kyau amma ko don na cimma burina dole ma naje,
Nikam da kin hakura muga gudun ruwansu Alkawari ya miki yace dole haisam ya dawo gareki
Aunty yaakime bana fatan haisam ya fara kusantar wata maace bayan ne,Aunty biki san yadda nake matukar kaunar shi ba ji nake kamar nai gaggawar jawowan lokacin da boka yayi Alkawari
Wallahi Aunty idan naga haisam gaba daya tsikar jikina tashi take na rasa wannan masifa nifa Aunty kar kiji da wai ko bai aure niba na samu ya kwanta dani shikenan na cire kwadayinshi a raina,
Oh yaana yaushe kika zama haka?
Aunty gaskiya nake fada miki wallahi,
Baza'ama ayi hakan ba aurenki zaiyi idan yaso saudatu da kaltum su mutu,
Hmmmnmn
Ni kuwa nasan abinda zan musu wallahi sai na rabashi dasu kwata kwata,
Ina bayanki bari kika na kwanta Asubanci zamuyi
To
Kince kina da test gobe?
Bar batun test dinnan Aunty lecturer mutumi nane
Zai iya bani kyautan marks
Saboda yasan ni yasan kokarin da nake mishi,
( wa iyazu billah kuji fah tsabar rashin basira )
Allah ya shirye mu wani course mate dinta ne ta mishi waya yazo ya kaita niger,
Yace to amma kinsan akwai test ko
Haba kar ka damu da wannan ai nawa ne kasan ,
To shikenan mi aka tanada min
Mi kake so?
Kwai na dan huta a jikinki,
Ba damuwa kayi yadda kake so indai wannan ne
Ba'afi awa daya ba sai gashi da mota kuwa land rover ta babanshi ya dauko,
Suka tafi yaakime ta bata kudi masu uban yawa,
Sun yi nisa a hanya sosai ya tsaya,
Lafiya?
Klau so nake na samu ENERGY,
Kaifa dan iska ne a dokar dajin zaka samu energyn
Yace eh,
Ya zagayo ya kwantar da sit din ta take zaune yasa hannun ya ya fara sarrafata abinda ya kaisu harda lulawa dunir ma'aurata.
Ko kefa ,
Da da hali su nake ki bar min abuna a bude idan na juyo ina ganin shi sai tafiyar tafi armashi,
Bazai yuwuba kasan akwai check point a hanyar haka ne,
Ya tada mota sun isa inda custom suke suka bukaci takardar neman shiga wata kasa,
Yace babu
Ganin irin shigar da yaana tai officer din yace babu kuma?
Kasancewar yasan nigeria da cin hanci da karban rashawa ya zaro kudi ya mika mishi,
Bana bukatar wannan,
Haba oga sir mi kake so to nayi Alkawarin zan baka shi indai zaka barmu mu wuce domin abinda zamuje nema yana da muhimmanci,
Kayi Alkawari kenan,
Eh
To ku fito daga motar,
Nan ya fara tunani ko motar zai karba da ya shiga uku tunda motar ta mahaifinshi ce kuma bai san ya dauka ba,
Officern ya kewayo yasa kan bindigarshi a kirjin yaana ga abinda nake so,
Zuciyarta kamar zata fashi don tsoro wannan bindigar da tagani ya tayar matada hankali,
Nan lukman yace wannan mi sauki ne yaana bada hadin kai kawai,
Ranta ya sosu ina zata kai wannan mummukin bayarabe fuska duk zane gwaya gwaya,
Gaskiya bazata iyaba duk iskancinta takan so mai fasali saboda yawancin lecturers din da take basu hadin kai ba laifi suna da tsabta,
Kunyi shiru zaku juya kenan
Nan kuma haisam ya fado mata,
Kai ya zama dole na amince indai har zan samu haisam ,
Nan ta wani kada mishi jikinta kar kadamu indai wannan ne,
Ya nuna mata tent din da zata shiga,
Lukman kuma akace ya yi parking a gefe ya jira su,
Abinka da rashin Arziki lukman yace ba damu officer a fito lafiya,
Kafin officer ya shiga,
Ya samu yaana
Daga ita sai short naker dinta da brightop
A wace irin hausar shi yake cewa ace ke yar gari ce,
Ya auka mata kamar wasu dabbobi
Bayan tantin taje tai tsarki ta tashi har yana ce mata Allah yasa idan suka tashi dawowa su dawo yana on duty,
Lukman yaja mota suka kara gaba,
Abin mamaki ko a jikinta,
Tana ta mishi kwatance har suka isa,
Tace wa lukman ya jirata a mota,
Ya zauna kuwa,
Ta shiga cikin rumfar a kewaye take da wani fallayen zannuwa na saki,
Nan ta koro mishi abinda tagani
Yayi dariya yace karyani ,
Aljani na tura mishi idan yaji zai kusanceta
Sai mu kashe mishi jiki bazai iya komai ba sai kasala ta lullubeshi ya fara jiri sai bacci,
To yanxu Allah ya taimakeka,
Bata karisa ba ya katseta kar ki kara kawo min Allah,
Idan kina kawo min Allah aikina bazai na yuwuwaba,
Yi hakuri ni dama so nake yi ayimin abinda zai ji sha'awata har ya kusancen,
Mai sauke kenan,
Sai dai fah idan kika kuskura ya kusance ki bazai aure kiba sai dai ku kare gantali kullum akan hanya,
Yauwa zanso hakan ma domin mu cusawa iyayensu bakin ciki,
To yanzu jeki mota zan kira ki domin akwai abinda za'a cusa a gabanki wannda idan ya kusance ki bazai kara kusantar wata mace ba sai ke,
Nan taji wani sanyi a ranta
Ta tashi ta fita shi kuwa ya janye wandonshi ya hau rubuce rubucen karya akan Alkalaminshi,
Bayan ya gama ne ya kwala mata kira ta shiga
Ya nuna mata shimfida
Ki wanta bana son na ganki da komai haihuwar uwarki nake son ganinki taji wani rass,
Hankalinta ya tashi duk iskancinta bazata iya tarawa da wannan kazamin ba
Ta kare mishi kallo tana tsammanin yakai wata biyar bai ga ruwa ba
Zaki kwanta ko sai nasa Aljani ya kwantar dake,
Kayi hakuri don Allah ka canza wani abin banda wannan
Karya kike yi ina hango ku kafin kizo sanda mutane biyu suka ci ki a banza ma wannan kuwa ya nuna Alkalaminshi dashe zai miki,
Kai gani take kamar bazata iyaba sai yasa dariya ya fara kulunboto nan da nan taji tana juyawa tana ganin kamar dakin na juyawa da ita,
Bata san sanda ta cire kayan jikin taba
Yasa dariya yayi kirari wa kanshi ya afka mata tunda take bata taba yin nadamar iskanci ba da biye biyen bokaye ba sai yau,
Domin ita ko a School ne lecturer yace zai bata carry over to sai tasan inda ta shawo kanshi da bokaye ya fara mu'amala da ita zancen carry over ya kare,
Ya durjeta yadda yake so,
Ya tashi ya barta yayi ta wasu maganganu da bazAta iya ji ba, domin ya barta ma bazata iya ko daga hannunta ba,
Daga yau ya zama naki.
duk yana ganinki idan bai kwanta dake ba hankalinshi bazai taba kwanciya ba,
Da yaga bazata iya tashi ba yaje yacewa lukman yazo ya tattarata yasata a mota idan ba haka ba Aljanu sun kusan dawowa hutawa zasu iya hutawa da ita a sabain ya shiga yaga yarda ta koma da kyar ya nutsu ya zuramata doguwar rigarta,
Bai bi takan pant bama balle bra da kyar ya iya tayar dai ita ya sata a mota ya kewa ya debo ruwa ya bata ya shafe mata fuska kamin ta fara dawowa dai dai gabanta kuwa kamar zai fadi tsabar azaba,
Lukman kanshi mamaki yake yi yana tunanin mi rai take nema wanda zai kaita ga halaka haka tafoya suke amma kwata kwata hankalinshi baya tare dashi yana tunanin yadda mata suke kauce hanya akan abinda bai zama dole ba,
Bai ankara ba sai yaji kamar karar wani abu ashe taya ce ta fashe musu ga kuma babbar mota a gabansu duk yadda zaiyi ya kauce abu ya gagara ji kake gararau ,
*INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN* motar kuwa ko ta gansu bata biba suka gudu, abinsu,
Ana haka sai ga wata motar BAGA ta kai kifi NIAMEY tana dawowa suka ga number motar ta borno ce ASKIRA UBA,suka tsaya suka ciccibesu ,babu mutuwa kam amma akwai munanan raunuka aka sasu a bayan *ROKA* SUKA kama hanya,
Yaa kimee haka kawai hankalinta ya kasa kwanciya gashi ta rasa wacce zata kira har shabiyun dare shiru gashi ita keda girki Bukar yaga tana ta zirga zirga
Ya tambayeta tace babu komai
Ta rassa yadda zata 'yi
Barci fir ya kaurace mata,
Wajen ukun dare taga kiran yaana sai taji muryan namiji ,gabanta ya fadi,
Miya faru ina mai wayar?
Kwantar da hankalilnki gamu nan muna emergency na teaching hospital Baga,
Baga kuma miya sameta,
Accident mukayi a hanyar mu ta dawowa dag wajen mai magani a tsatsunburi,
Gashi wayar ana jinta rangadadau,
Alhaji yaji duk abinda ake fada
Ta kashe wayar yanzu yaakime miye kike nema a dunia da bazaki hakura da biye biyen bokaye ba,
Wallahi ba aikenta nayi
Tafiyar kanta ce,
Ko baki aike taba abinda taga kina yine take yi balle na tabbata kice kika aike tanma,
Ta hau rantse rantse yace oho can miki sai ki tashi kije ki dubata,
Kar ki yarda ki dauka min driver tunda Abinnanku bana Allah bane ya kauce wa tsarin Allah ,
Shirka yaa kime haba,
Wallahi ina da na sanin aurenki yaakime,
Tausaya miki nake yi kawai shiyasa ban sake kiba ,
Domin wallahi ba namijin da zai iya aurenki,
Ga rashin hali ga rashin haihuwa,
Itafa ba wannan ne a gabanta ba
Ta fita ta koma side dinta ta ttaro kudade tasa a jaka muhammadu ta tayar tana kuka ya rufa mata asiri ya gaita baaga yaana sunyi hatsari a hanya
Hanya kuma hajiya eh
Daga makaranta aka turasu ai
Owk ita da dalibai kenan
Eh kuma Bukar yace kar na dauka mishi driver a tsakar daren nan
Ba komai gani nan zuwa,
Suka kama hanya wajen 5 sai gasu cikin baaga aka nuna musu Asibiti sunje sun same yanna anyi mata Alluran bacci tsabar azaba da ihu da take musu,
Nan likitocin suka musu bayanin ta samu karaya uku a kafa daya sannan mahaifarta ma ta Zazzago kasa gashi cikin mahaifar an samu wani abu kamar anyi shi da rubuce rubuce amma mun gagara gane wa,
suka dauko abin a cikin kwalba suka mika wa muhammadu gagara karva yayi,
Yaana ta karba,
Sannan inafa hannunta na haku ma akwai karaya amma yanzu munyi kokarin tsaida jinin da yake fita daga mahaifar,
Dauri ne bamuyi ba mukace ko zaku yi na gida,
Lukman kara dayace a hannunshi,
Yaana tana tambayarshi abinda ya faru,
Sam ta manta da muhammadu a wurin tsabar yadda taga halin da yaana take,
Shikuwa tun daga kayan da yasa mata da sakata amota sanda ya fada,
Sai anan ne ma ta lura yanar irin rigar da take jikinta muhammadu ya kau da kanshi
Lukman yana mata magiya ta taimakeshi bai san mi zaice wa mahaifinshi ba
Ya mishi asara da mota,
Domin masu gadin gidan sun ganshi sanda yake fita daga motar,
Muhammadu kamar ya nutse tsabar kunya sukai sign aka saka yaana cikin Ambulance sai teaching hospital na maiduguri,
Su muhammadu kuma suna binsu a baya,
Gida ya wuce tare da wannan kwalbar domin yaakime ta barta a motar,
Ya zayyanewa Bukar da umar abinda ya faru,
Da labarin da saurayin ya bayar,
Umar yayi tur da halinsu yaakime,
Bukar yace wallahi ba don wasiyyar Alhaji ba da yayi akan ya haramta mana saki ba yau dana sake ta,
Hakuri zakayi inji umar
Muhammadu ya wuce da kwalbar wurin shatu gashi ranar su jidda a dakinta suka kwana sukai tsit kamar wasu masu bacci
Duk abinda muhammadu yake fadawa shatu sun kwashi tsab a kansu jira suke ya tafi su fito suga kwaf,
Abin ba karamin tsoro ya basu ba,
Yaana kuma mi ya kaita,
Haka har kabari wani kazami ya kusance ka
Nan fah zance ya watsu
Tab abinka da family house aka samu *LATEST TOPIC OF DISCUSSION*
BINAZIR
Tace Aunty Aisha dole sai kun dage da Addua kinji ranar yadda mukai da ita da jidda,
Hmmmmmmm
Nan ta tuno da abinda yake faruwa dasu zasu yi wasa iya wasa ai anje makura kuma a gagara,
Tayi Alkawarin wannan abin sirri ne bazata taba fadawa kowa ba,
dai dai da mahaifiyarta,
Aunty kinyi shiru?
Babu Aunty kinsan abinda tabani mamaki har cewa take wallahi karya ne,
Hmmm
Ita tasani, ba gashi ba Allah ya nuna mata iyakarta ba,
Yanzu da ace mutuwa tayi a hanyar dawowa daga gidan boka fah,
Ki dai ki dage kawai Aunty
Kaltum da ummi sauda ne suka je duba yana
Tana ganinsu ta hau shirme da shirbuci
Yauwa ummi kinzo?
Ina mijina haisam?
Kinga yaki zuwa ko?
Yazo ya karbi sakon shi na wurin Boka,
Ummi sauda tace ba lafiya
Lalle kwakwalwa ta samu tabuwa,
Yaakime ya kamata a duba kwakwalwarta fah,
Eh dama an dauki hoton kwakwalwar amsar muke jira
Suna cikin maganar sai ga likita yazo yana mata turanci sai sauda tace yace ki bishi office ne,
taho muje,ai kinsan ba turancin nake ji ba,
Ya shiga sauda take tambayarshi,
Yaya
Eh sakamakon binciken da akayi ya fito Kwakwalwar ta dan tabu amma ba gaba daya ba idan tasha magani na wani lokaci zata samu sauki munyi kokarin mun tura mahaifar ta koma amma gaskiya ta gama aiki bazata taba haihuwa ba,
Domin mun gano tana shan kwayoyin tsarin iyali,
Sannan yanzu haka akwai *inplanon*a hanunta insha Allahu jinin da yake zuba munyi tsaidashi,
Nan sauda ta kwashe bayani ta fadawa yaakime ,
Ya kime tace tsarin iyali,
Mi ya kaita da tsarin iyali yanzu,
Eh muje ki duba hanunta,
Suka nufi yaana ta duba hannunta sai ga abu a hannunta,
Na shiga uku ,
A'a yaakime batun yau ake miki magana akan yaana ba domin akwai sanda umar ya mata magana kikai mirsisi kika ce a kyaleta an sata a gaba
To
Kinga abinda ake fada miki kike cewa yar jami'a ce
Mu kanmu munyi jami'ar ai,
Suka tafi suka barta cikin damuwa ta shiga uku tonar asiri kenan lokaci daya Allah ya kamata,
Haukane kawai bata yiba yaakime tace yaana kin cuce ne ashe bin maza kike yi duk tsiyata ban taba bada kaina a wani ba,
Sauda sun shiga gida maza ta kira haisam tace yazo shida Aisah
Tana neman su ,
Suka zo suka gaisah nan ta fara mishi bayanin da taji yaana tana yi don haka kar ku kuskura kuce zaku je,
Ai kuwa ummi dazu nake cewa EASHA ta shirya muje da daddare mu dubata,Kar ku fara,
Daga nan Aisah ta shiga gidan shafa,
Mi zata gani shafa Amai kike yi?
Badar hankalinshi ya tashi, nace mu tafi Asibiti take yarda ne,
Tun yaushe take aman yaya?
Kusan 2 wewks fah,
Kai yaya,
Ina ai kuwa bazai yuwu a kyaleta ba,
Nan Aisah ta kirah Ya haisam dinta,
Ta sanar dashi,
suka tafi asibiti likita ya tambayeta symptoms din da take ji yace za'ayi urine test ,
Anayi sai ga zanen ja biyu, nurse ta mika mishi result yace wa Badar congratulation,
Ya mika mishi hannu,
Aisah ta cewa shafa ANTI HAAMILA,
HAMALTUL JUNAIN FI BADANIKI.........Ta'aliki
Zaba
Watsa
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾
YOU ARE READING
🖕Gaskiya Daya Ce 🖕
RandomLabarin dake kunshi da kalubalen rayuwar zaman gidan Aure tsantsar munafurci, kissa, fuska Biyu.