page 1

6 1 0
                                    

💖💐 AHNAF 💖💐

D Yuguda

Bismillahirrahmanir rahim

Yammacin yau na ranar lahdi cike yake da wani irin yanayi mai dauke da ababe masu ban sha'awa gami da sa nishadi acikin zukata tare da kwantar da hankalin duk wani mahaluki da ya tsinci kansa kansa a irin wannan yanayi.

Duba da yanda iska ke kada bishiyoyi yayinda da suke ta shawagi da rausaya ga dukkan alamu suma suna jin dadin kasan cewar su a wannan yanayin.

Matashiyar matar da bazata gaza shekaru talatin zuwa da uku ba tana tsaye dai saitin windon da zai sada ka da farfajiyar gidan yayin da tayi zurfi cikin tunani na rayuwa da yanda alamura suke zuwa suke shudewa ba tare da la akari da me hakan zai haifar ba ya LA Allah farin ciki ko akasin haka , kallo daya Zaka mata ka tabbatar tayi nisa awannan yanayi Wanda Sam har ta manta yawan mintunan da ta dauka atsaye a gurin.

A hankali kwakwalwarta ke tariyo mata wassu abubuwa da suka shafi rayuwar ta atake kuma ta share hawaye tare da murmushi hade da godewa Allah buwayi gagara misali sakamakon jin 'ya'yan ta na kwallo mata kira.

Mommy! Mommy!! We are back take ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da sauke labulen gami da  biyo inda takejin muryansu tana musu oyoyo  my sweet hearts barkan Ku da dawowa yayin da take kokarin hugging dinsu tare da manna musu peck a kumatun su a tare sukace we love u mum, ta kalle su tare da yin murmushi tace I love u too yarana, maza kuyi sauri kuyi alwala kai Affan ka shige masallaci an fara kira ke kuma Anam muje muyi tare suka amsa  da to, yayin da Affan ya fice zuwa masallacin jikin gidan ita kuma ta haura sama da Anam don gabatar da sallar magrib.

Bayan sun idar da sallah suka zauna suka ci gaba da karatun kur ani har aka kira isha suka mike sukayi hade da shafai da wuturi sannan sukayi addua.

Anam ta kalle ta tace mommy I'm hungry a hankali ta shafa kanta tace tom muje kasa muci abinci suna mikewa sukaji sallaman Affan suka hadu duka suka wuce table a hankali cikin nutsuwa ta zuba musu sukayi bismillah suka fara ci har suka gama ba Wanda yayi magana saboda ta hanesu magana  yayin da suke cin abinci.

Bayan sun gama affan ya kwashe kwanukan ya kai kitchen ya fito yana tambayar maman su wai ina john ne yau ban ganshi ba tace ya je dazu aka kirashi gida  mamansa ba lfy, Affan yace ayya Allah ya bata lfy suka amsa da ameen dukkan su.yayin
da ta kalle su tace ya kamata kuje ku yi wanka kuyi shirin bacci gobe akwai school suka amsa da to mommy, ta rike hannun Anam suka haura sama, yayinda da affan ma ya shige dakinsa don yin wanka ita kuma ta mawa Anam ta kwantar da ita ta fita zuwa gun affan ta masa addua ta kashe masa wuta ta dawo ta kwanta kusa da Anam bayan ta mata addua ne ta fada duniyar tunani a hankali ta fara tariyo tarihin rayuwar ta........

D yuguda😘

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 06, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AHNAFWhere stories live. Discover now