🅱 *BRILLlANT WRITERS ASSO* 🖊
{ pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers }🌹🌹🌹 *_MATAR DADDY*🌹🌹🌹
*Story and writing*
*By fatiey afirst*~Base on true Life story~
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ faty afirst*
*Dedicate this page to brilliant writers association*
0⃣1⃣
Xaune yake a katafaren parlorn sa ya daura kafa daya kan daya yana karan ta jarida kasan cewar yaw weekend ne ba ayki alhaji Haruna naira kenan.
Daga gefensa kadan kuwa yar matashiyar budurwa ce me shekara goma sha shida tana daddan na wayar ta kiran iPhone sanye take da Black trouser da Red Top kanta ko dan kwali babu,halima kenan wato mima diya ga alhaji Haruna naira.
Dan gajeran tsaki taja kafin xuwa can tafara kwalama me aykinsu Kira " tala! Tala!! "
Cikin sauri tashigo parlorn ta duka kusa da ita duk da ta girme mata nesa ba kusa ba amma sam mima bata ganin girman ta ba ma ita ba kaf masu aykin dake gidan bata daga ma kowa kafa dan batasan talaka.
Batare da ta juyo ta kalletaba tace " tsabar wulakanci ne yasa Ina kiranki kikai min banxa "
Kara kankantar da kanta tai " kiyi hakuri ranki shi dade Ina kitchen ne banjiki ba "
Tsaki ta saki kafin tace " ban ruwa me sanyin"
Cikin sauri ta dauko ruwan ta miko mata da cup jikinta na rawa dan bata so ta kwafsa ay mata tashin mutunci.
Amsar ruwan tai taxuwa a cup ta kurba kadan ta watsa mata sauran a fuska.
" Mayya sokike ki shake Ni Ina sha kina kafeni da Ido"
Mikewa tai da sauri ta nufi kitchen.
Daddyn Nata na xaune yana jinta amma ko dagowa beyi ba bekuma kalli inda suke ba dan shi sam Bega laifinta ba.
Sai da ya kai karshen page din sannan ya dago ya kalle ta.
"Mima" ya fada kamar yana tsoron abun da xai gaya mata.
"Naam daddy" ta fada batare da ta dago ba
"Dauko mayafinki ki muje xiyra wurin su granny kinga mun kwana biyu bamuje ba"
Dan yatsina fuska tai cikin shagwaba " nidai gaskiya daddy kaje ka dawo banajin fita yaw "
Dan murmushi yay "ay ba dadewa xamuy ba kuma har ice cream xan siya miki a hanya "
"Daddy kai ma kasan banasan xuwa bama kamar gidan su malam kaga fa rannan hajiya marina tai "
"Mari?" Ya maimaita cikin mamaki danshi tunda suke bai taba daka mata tsawa ba bare kuma takaiga Mari.
Sauke ajiyar xuciya yay dan da ace ba mahaifiyar sa bace da yaw sai inda karfin sa ya kare kan yar marainiyar sa.
Hakuri yashi ga bata kamar itace ta haifesa ba shiba dakyar ya shawo kanta ta yarda suka fito xuwa gidan kakan nin Nata.
Tun a moter take xuba masa korafin itafa kar sudade a haka har suka isa gidan iyayen shi.
Gidane irinna alfarma ginin xamani tun daga harabar gidan yagane akwai baki dan motoci sun karu a kan wanda ya sani.
Driver na gama Parkin yafito Mima na binsa a baya tana tuttura baki tareda harare harare.
Kanyakai bakin kofar parlorn har yan aykin gidan sun taru suna gayshe shi cikin mutun ci yake amsa musu amma Mima ko kallan banxa basu isheta ba, hannu yasa a aljihu yafito da rafer yan dubu dai dai guda biyu ya basu kafin yasa kai xuwa cikin.