BURIN HAFEEZ

61 2 0
                                    

BURIN HAFEEZ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.

Episode 2

K'aran alarm din k'aramin agogon dake cikin d'akin ne yafara amsa kuwwa, mai nuna alamar Lokacin da aka saita shi yayi, Balkisu na daga cikin bargo tami'ko hannunta dan tsaida wannan k'aran kasancewar agogon na gefen gadonta, hannu tasa ta danna wani abu sannan k'aran yatsaya, a hankali ta zuro 'kafafunta daga kan gadon da take kwance yayinda idanuwanta ke lumshe a haka tanufi toilet, tana shiga ciki tayi brush sannan tad'aura alwala, bayan tafito tafara gabatar da sallahr asubanta kasancewar lokaci yayi
Balkisu na idar da sallah kamar wadda aka tsikara ta tashi da sauri tafad'a  toilet a karo na biyu ta silo wankata, dasauri-dasauri ta shirya tsaf cikin atamfarta mai ratsin orange da lemon green, Balkisu dukk da ba wata doguwar kwaliya tayiba amma kayan sun matuqar amsarta, gyalenta ta dauko Wanda yayi matchn da kalar kayanta tayafashi gamida d'aukar handbag dinta tanufi hnyar falo.

Daniel! Daniel!! Where are you? Dasauri Wanda Balkisu takira da Daniel yafito daga cikin kitchn sanye da kayanshi na kuku' dasauri ya iso gaban Balkisu cike da rissinawa Daniel yace

"yes madam gani,"

Balkisu tadubi Daniel sannan tasake duban dining area kafin tace wani abu tuni Daniel yafuskanci abinda takeson tambayarsa dasauri yace

"am very swry Madam, yau nadan makarane bansamu na kammala breakfasts din da wuri ba"

Balkisu tadanyi jimm kamar baza tace komai ba, chan dai ta numfasa tace

"it okey yanzu dame dame ka kammala?"

Daniel yace "madam sos din kwai ne sai ruwan zafi na tea yanzu ne nakeson daura ferfesun kayan cikin"

Balkisu tace "okay jeka kawomin tea da sos din its OK".

Dasauri Daniel yashiga kitchen yazo gaban Balkisu yacika umarninta nan da nan yahada mata breakfast, balkisu na kammalawa ta d'auki handbag dinta gamida kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunta 7:30am tagani Dan haka dasauri takira Daniel tabashi umarnin yayi sauri ya kammala breakfast din saboda yanzu Yaya Hafeez zai fito yin breakfast d'inshi...cike da bin umarnin ta yace "okay mam"

Parking space tanufa kai tsaye tad'auki wata jar mota k'irar jeep, dasauri mai gadi yabud'e mata gate ta fice a gidan"

Balkisu bata nufi ko inaba sai anguwar da suka hadu da wannan yarinyar ta jiya, tana shiga cikin anguwar tafara tunanin ta ina zata fara ganin wannan yarinyar? tayaya zata fara nemanta? Wad'annan tambayoyin ta fara jero ma kanta, shiru tayi na d'an wucin gadi, Nan take dibara yafad'o mata, gurin wani mai sai da biredi da shayi dake cikin unguwar ta nufa Wanda dukk abunda yafaru jiya a gabansa ne dan haka tayi tunanin zuwa gurinsa koh Allah zaisa yasanta.
Daga gefen hanya kad'an tayi parking motarta bayan takulle sannan tanufi garesa.

Balkisu na isa gurin mai wannan shayin  yaganeta, cike da rissinawa Balkisu ta gaidashi kasancewarsa dattijon mutum, Cikin sanyin magana Balkisu tace "Baba Dan Allah kokasan wannan yarinyar da wannan Abu yafaru jiya a an an wajen?

Shiru maishayi yayi, cikin ransa yace"anya kuwa yadace nasanar da ita gidansu kuwa? Domin bansan wanne irin tashin hankali zataje ma wannan baiwar Allah dashi ba?" Maganr Balkisu ce takatse mishi dogon tunanin da yatafi, Baba karka damu inason ganin yarinyar ne saboda inason inbata hakuri akan abinda yafaru jiya, mai shayi yayi murmushi yace auu toh ae shikenan, nan mai shayi yayi mata kwatance gidnsu wannan yarinyar "yace dazarar kinshiga cikin kwanar kikace a nuna miki gdan Yaganaa mai awara toh babu wanda bai sani ba, Balkisu tayi mishi godia tanufi inda ta ajiye motarta dasauri tanufi cikin kwanar da wannan mai shayi yayi mata kwatance, Balkisu sai murmushin mugunta takeyi domin kuwa
ayau tayi al'kawarin sai tad'auki wannan yarinyar takaita gurin yayanta yacika burinsa koh zata samu ya sau'ko daga fushin da yakeyi.

Balkisu nashiga cikin kwanar tane mugun parking, sannan tafito daga cikin motar gamida kwalama wata yarinya kira keee!!"zo yarinyar dake 'ko'karin wuce wa tagaban Balkisu tatsaya a dai-dai inda take ba tare da ta 'karasa wajen maikiranta ba, ganin yarinyar batada niyyar 'karasowa wajenta yasa Balkisu tafahimci akwai alamar tsoro atattare da yarinyar, murmushi kawai tayi gamida jehoma yarinyar tambaya tace kokinsan gidan Yagana mai awara?? Yarinyar ta gyada kai gamida nuna mata gidan da danyatsa tace gashi chan gdan maibishiyar mangwaron chan.

Balkisu tagyad'a kai gamida murmushi alamar ta gane, godiya tayima yarinyar dai dai lokacin tasa key tarufe motarta sannan tanufi gidan cike da Burin son ganin wannan yarinyar Balkisu nashiga cikin gidan tafara jiyo ihun mutun alamar ana dukanshi, batasan lokacin data 'karasa cikin gdan da saurinta ba gamida ri'ke hannun wannan mata dake dukan wannan yarinyar. Dasauri Yagana ta dannawa Balkisu wata uwar harara gamida tambayarta kekuma fa?? Waye ke da zaki shigo min gida cikin gida babu ko sallama bare neman izini, Balkisu tayi murmushi gamida cewa kiyi hakuri baiwar Allah nasan bankyauta ba, Amma wannan dukan da kikema wannan yarinyar ne yad'agamin hankali banmasan lokacin dana shigoba, Dan Allah baiwar Allah kiyi hkri kimata afuwa ki dena dukanta haka.

Dasauri yarinyar da ake duka tami'ke tsaye dan ganin wacece tashigo cikin gdansu Dan cetonta daga hannun yagana domin kuwa iya tsawon rayuwarta idan Yagana na dukanta 'ka'ida ne babu wani mutum da ya Isa yazo yabata hakuri ko yaceceta daga dukk wata azaba daza'a gwada mata, dan haka tami'ke daga du'ken da take don ganewa idanunta. d'agowan dazatayi kuwa idanunta sukayi tozali da wannan yarinyar wanda fad'a yahad'ata da yayanta a jiya, nan da nan jikin wannan yarinyar ya hau rawa bakinta na rawar sanyi ta dubi Balkisu gamida had'a hannayenta alamar neman gafara tace dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri inba haka ba kuma kawai kikaini police station domin kuwa nasan abinda yakawoki kenan.

Abin ya matuqar bama balkisu dariya gamida tausayin yarinyar a lokaci d'aya, a hnkli Balkisu taja hannunta suka nufi waje, yayinda jikin wannan yarinyar ya cigaba da kad'awa alamar sanyi domin kuwa gabadaya illahirin jikinta a jik'e yake jagafff!.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 05, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BURIN HAFEEZWhere stories live. Discover now