*ƘARSHEN MAKIRCI*
_(Nadama)_Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 3.
*Gargaɗi*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a kafar youtube channel ko website ko facebook ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, da fatan za a kiyaye_.
Dr Fadeela gidanta ta wuce wanda yake cikin Asibitin, akwai gidajen Ma'aikata daga ciki don katon Asibiti ne kusan Anguwa guda.
*
Baba Habu ya isa gida lafiya ya tadda Matarsa zaune a tsakar gida ta rafka tagumi sai ya shigo da sallama, firgi-git ta farka daga tunanin da take ciki tare da amsa masa ta d'aura da cewa"Malam lafiya shuru yau baka shigo gida da wuri ba? Wallahi duk hankali na ya tashi kasan wannan Gonar naku cike yake da hatsari?"
"Hansatu babu ko sannu da zuwa kin tsareni da tambaya, lafiya lau nake kawai dai wani abu ne ya tsareni ban samu shigowa da wuri, yanzu ruwan wanka zaki bani in watsa ina son in tafi masallaci Sallan Isha'i ya kawo jiki" ya k'arasa maganar yana tafiya harya shige d'aki.
Binsa da kalli Hansatu tayi tare da mik'ewa ta shiga madafa ta d'ibar masa ruwan zafi a bokiti tare da sirkawa ta kai masa bayi.
*Bayan Sallan Isha'i*
Suna zaune bisa tabarma a tsakar gida, Baba yana cin abinci Hansatu ta jefo masa tambaya
"Malam naga ka shigo da kaya a leda, nace ina ka samu kud'i haka harda siyayyar kayan abinci?"
Murmushi yayi tare ta rufe kwanan abincin sa ya kurb'i ruwa ya saki gyatsa tare da yin Hamdala, sannan ya fuskance ta ya soma bata labarin duk abin da ya faru, sosai Hansatu ta girgiza tace cikin kid'ima
"Malam wannan aikin kasada ce kayi gaskiya ba zaka kuma komawa Asibitin ba, iya taimakon daka mishi ya wadatar, haba Malam muna d'an zaman mu lafiya zaka jawo mana matsala" ta k'arasa magana a hasale.
"Ai in matsalar tazo iya ni zai shafa babu ruwanki a ciki ki zuba min ido kiyi kallo, ni taimakon Musulunci nayi kuma nayi dan Allah ne, sannan banji ko d'ar da dana sanin abinda nayi ba, kuma ina rokan Allah ya cigaba da taimako na bisa kyakkyawar niyyata, babu ruwanki".
"To shikenan Allah ya baka hak'uri tunda gyara kayanka bai tab'a zama sauke mu raba, ni dai gaskiya na gaya maka" sai ta mik'e ta shige d'aki, yabi ta da kallo yana murmushi tare da girgiza kai
'Hansatu sarkin rikici' yace a ransa.
*** ***** ***
*GARIN KADUNA*
Nura ya sauka lafiya ya tari Napep ya nufi gifan Imran, tun a mota yake k'ir-k'iro kuka amma ya kasa fidda hawaye duk yanda yaso amma abin yaci tura, tsaki yayi a ransa yana mamakin yanda hawaye yak'i zuba masa, can dabara ta fad'o masa sai ya sanya yatsa ya tsokale idonsa na dama nan take hawaye ya ciko idonsa, d'ayan idon hagun shima ya masa haka nan da nan idonunsa suka yi ja suka soma fidda hawayen azaba, sosai yaji zafin abinda yayi wa idonsa amma ba yanda ya iya domin hakan ne mafita.
_Hausawa suka ce dama mugu bai cika mugu ba sai yayiwa kansa mugunta._
Suna kaiwa bakin gate d'in gidan yama mai Napep magana ya tsaya ya biya shi kud'insa ya wuce.
Sai ya bud'e gate ya shiga yana rusa kuka, jakar kayansa a nan tsakar gidan ya saki ya wuce part d'in inna Rabi da gudu yana kuka kamar Yaro.
Duk da halin da Matan falon suke ciki na Alhini sai da suka tsorata da kukan Nura, yana shiga ya je jikin Inna Rabi ya d'aura kansa bisa cinyarta yana Kuka mai tsuma zuciya.
KAMU SEDANG MEMBACA
K'ARSHEN MAKIRCI (Nadama)
RomansaFarida ce ke tsula gudu a mota hawaye ya wanke mata fuska jikinta yana rawa ta kira number Nura, bugu d'aya ya d'auka ta tari numfashinsa da sauri "Nura, Nura wallahi bai mutu ba yana nan a raye, yanzu na ganshi a Asibitin Mahaukata na nan cikin Ab...