PAGE 33

479 14 3
                                    

*SANA'A CE*


*Na*

*Aisha Alto*


*DEDICATED TO*
*HAUWA A USMAN JIDDAH*😍


   *Bismillahirrahmanir rahim.*


                    3⃣3⃣

Tuni ta farka cikin hankalinta ba tare da likita ya sani ba,  tashi tayi zauna a tsakiyar gadon take ta faman rusa kuka, ƙwaƙwalwar tana sake tariyo mata abubuwan da suka faru, ta daɗe sosai tana kuka idanuwanta duk sun jeme sun kumbura sun kaɗa sun yi jajir, in banda tausayin Nadeeya da tsananin tsanar kanta da rayuwar ta babu abin dake azalzalar ruhi da zuciyar ta, ji take dama kawai ta mutu gaba ɗaya ko ta huta da wannan abin kunyar da ta tabkawa baiwar Allah.

Kwata-kwata ba ta san da wane ido za ta iya kallon Nadeeya ba, domin ta yarda da ita a rayuwar ta, ta bata amana komai na rayuwar ta, to yanzu ta ina ma za ta fara, ina za ta bi, wa kuma yanzu za ta kama? Waye zai shige mata gaba, ina za ta bi ta nemo mata ɗan ta Mahboob? Ta san dai duk ranar da Shaheed yasan me ta aikatawa ɗansa ba zai taɓa barin ta ba, ta san sai ya ɗauki mummunan mataki a kanta, wace mafita ya kamata ta nemarwa kanta da rayuwar ta yanzu?

Wani tunani ta yi da sauri ta kalli agogon dake maƙale a jikin bangon room ɗin ƙarfe 10:30pm ta gani, da hanzari ta sauko daga saman gadon, ta matsa gaban window ta buɗe labulen ta leƙa harabar asibitin, hasken fitila ya haske wajen tamkar rana, motoci uku ta gani a pake, sai mutane ƙalilan dake ɗan kaiwa da kawowa, da alamun masu jinyar marasa lafiya ne, da sauri ta dawo da baya ta ɗauki wani ɗan baƙin gyale mai kamar ɗan kwali da ta gani a kan gadon ta yafa a saman kanta, ta janyo shi ta rufe gefen fuskarta, ta isa bakin ƙofa ta buɗe ta ɗan leƙa kanta, gurin tsit yake ba kowa, ta fito ta sake waigawa gefe da gefe still ba kowa, ƙafar ta ba takalmi haka ta bi ta wani ɗan lungu ta doshi hanyar da za ta sadata da harabar asibitin, har ta ƙarasa bakin get ba ta gamu da kowa ba kawai ta fice tana sauke ajiyar zuciya.

★★★

A gajiye ta dawo daga makaranta don da ƙyar ta kawo kanta gida ta na yin parking ta kashe motar ta ɗauki hand bang ɗin ta da wayar ta ta fito ta rufe motar ta nufi ƙofar shiga falon.

Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga cikin falon, turus ta ja ta tsaya a bakin ƙofa, tana bin Aunty Zainab da Shaheeda da kallon al'ajabi da tsantsar mamakin ganin wasu sababbin haɗaɗɗun akwatina da kaya jibge a gaban su, suna ɗaɗɗagawa.

Shaheeda ce ta fara lura da ita, fuskar ta cike da fara'a tace.

    "Ƙaraso ciki mana kema ki ga abin da muke kallo."

Da gudu Mahboob da Hilal dake zaune a can gefe ɗaya suna buga game suka jefar da abin game ɗin, suka nufe ta da gudu suna mata oyoyo, da sauri ta taresu tana sake faɗaɗa fara'ar ta, sai da ta ɗaga ko wannen su sama ta sumbace shi, sannan Hilal ya karɓi hand bang ɗin ta ya haura sama da gudu don ya kai mata ɗaki, Mahboob ya bi bayan sa da gudu suka haura tare, sannan ta ƙarasa kusa da Aunty Zainab ta zauna tana musu sannu da gida, da murmushi akan fuskar su duk suka amsa mata, tare da tambayar ta ya karatu, ta amsa musu da.

   "Alhamdulillahi."

Tana warware ƙaramin gyalen doguwar rigar dake jikinta, wanda tay rolling da shi a kanta.

Shaheeda ta ɗan dubeta tana hararar ta.

     "Ban ga leda a hannun ki ba fa, ina abin da na ce ki taho min da shi, kar dai kice dani kin manta da saƙo na?"

Dafe kai tay tana dariya.

       "Afuwan, wallahi na manta, amma yanzu bari in watsa ruwa sai inje in nemo miki."

     "Tab ashe kuwa baki nemi zaman lafiya ba, don idan ban ci abin nan ba yau, sai dai ɗan ki ko ƴar ki su fito da rowa."

Da sauri ta dafe bakin ta tana girgiza kai.

      "Ina aikam yanzun nan za a nemo shi, kwantar da hankalin ki kamar kin ci kin gama."

Aunty Zainab tay dariya tana faɗin.

     "Aikam da nafi kowa murna idan suka fito da rowar nan."

Nadeeya ta ɓata fuska.

     "Haba Auntyna, tun yanzu har kin fara kishi kenan?"

     "A'a a'a, kishin me zan yi? Bayan ga ɗa na nan zai yi aure, ya haifar min sabon miji kyakkyawa kamar sa."

Wata irin tsinkewa zuciyar Nadeeya ta yi, wanda ta rasa dalilin yin hakan.

Maganar Shaheeda ta dawo da ita daga duniya tunanin da take son faɗawa.

      "Duba wannan material ɗin ki gani idan ya yi, don shi na zaɓar mana ankon zuwa gurin dinner."

Wani ras ta sake ji a ƙirjinta, lokaci ɗaya ta ji duk ilahirin jikinta ya mutu, a sanyaye ta miƙa hannu ta karɓa tana jujjuya shi.

     "Ya yi kyau sosai gaskiya."

Ta sake ɗago mata wata haɗaɗiyar doguwar riga kalar maroon mai adon duwatsu, ta ɗora mata a cinya.

     "Kin ga wannan kuma wacce zamu saka ce ranar Arabian nights."

Da sauri ta ajiye material ɗin hannun ta ta ɗauki rigar

    "Waw Masha Allah, ai ni kinga a inda nake nan, amma dai wannan ɗin tawa ce ko?"

     "Eh mana taki ce, ai kin fini tsawo."

Aunty Zainab ta zanyo akwatinan gaban ta, ta fara shirya kayan a ciki.

      "Dan Allah ku ajiye kayan nan, ku sa hannu mu yi mu gama shirya akwatinan nan, kin san gobe za a kai su, gara mu shirya tun yanzu, don Aunty tace ba sai abin dasu ta can gidan ta ba."

Shaheeda ta fashe dariya.

    "Lallai Mami, Ya Shaheed zai yi aure yanzu an fara masa kunyar ɗan fari kenan."

Wani irin duuummm Nadeeya ta ji a kunnuwan ta, take ta nemi jin ta na lokaci guda ta rasa, in banda kalmar Shaheed zai yi aure babu abin da ke yawo a cikin ƙwaƙwalwar ta, wani sarawa ta ji kanta ya fara, da sauri ta dire kayan dake jikinta ta miƙe tsaye.

Da mamaki suka ɗaga kai suna kallon ta, kafin Aunty Zainab tace.

    "Ina zuwa kuma Nadeeya?"

Hawaye ta ji sun cika mata ido, kafin a hankali su fara zubowa saman kumatun ta, a wayance ta sa hannu tana sharewa.

     "Babu komai Auntyna, kaina ke ciwo."

Jikin Aunty Zainab yay sanyi ta dubi Shaheeda da ta zuba mata ido kamar tana son gano wani abu, da sauri tace.

      "Subhanallahi, shine kuma kika tsaya maza jeki ki watsa ruwa, bari in haɗo miki abinci ki ci, sai kisha magani."

    "To Aunty."

Ta juya da sauri ta haura sama, tana jin zuciyar ta na wani irin dokawa kamar za ta faso ƙirjinta ta fito, tana shiga ɗaki ta zube a bakin ƙofa ta ɗaura hannu akai ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.






*Kuyi manage pls ban da charge*.



*Aisha Alto ce*✍🏻

SANA'ACEWhere stories live. Discover now