*ƘARSHEN MAKIRCI*
_(Nadama)_Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 4.
Bakin gadon ta isa ta tsaya tana kallonsa shi kuma yana ta mutsu-mutsu, k'amshinta ne ya daki hancinsa sai ya samu Kansa da lumshe ido ya kuma bud'e su tare da karkato kansa gareta ya tsura mata ido, itama ta bud'e manyan idonta suna kallon juna ido cikin ido tana nazartar yanayin da yake ciki, tayin minyi biyu suna a haka daga bisani sai tayi breaking kallon ta shiga duba raunin jikinsa dake fitar da jini
"Sa'a bani kayan dressing komai da komai zaki had'o min sannan da Allurar barci" tace a nutse.
Cikin hanzari Nurse Sa'a ta fita ta had'o kayan ta kawo mata. Minti Ashiri ta d'auka tare da yi masa dressing ciwukan dake jikinsa, Imran yanata kallonta kifta ido kawai yake yi, Dr Freeda ta d'ago kai suka k'ara had'a ido sai ta tamke fuska ta kawar da idonta
"Khalil zo ka kama min shi nayi masa allura"
Cikin natsuwa Khalil ya matso ya karkata shi sai ya fara mutsu-mutsu ya soma kuka kamar k'aramin Yaro, Allurar ta tsira masa ta baya Imran ya saki kuka sosai harda shasshek'a cike da shagwab'a, abin ya bama su Nurse Sa'a dariya Fadeela ta juyo ta kalle su nan take suka kunshe dariyar, sosai take zasarin sa a ranta tace
'Da alama ka samu matsala a kwakwalwar ka, amma bari in bincika tukunna in gasgata'
"Sa'a Ku shirya min komai a d'akin bincike zan duba shi by 1pm insha Allah" ta fad'a a bayyane.
"To Anty" Sa'a ta furta cike da girmamawa.
Imran tun yana iya kallonta har ya soma ganinta dishi-dishi yana lumshe ido, kafe shi tayi da ido itama fuskarta d'auke da murmushi, shima sai ya mai da mata murmushi tare da rufe idonsa barci mai nauyi ya d'aukeshi fuskarsa cike da annuri.
"Bari na je gida ku tabbatar da kuna kulawa dashi, kuma Ku barshi a d'aure karku kwanceshi, sai nadawo"
"To Adawo lafiya" suka had'a bakinsu gaba d'aya.
Tana fita ta nufi inda tayi parking motarta tana k'ok'arin bud'ewa ta shiga sai ga Dr Bilal nan yayi parking gefenta da sauri ya fito ko rufe motar baiyi ba ya cimmata ita kuma tana k'ok'arin zama, rik'e marfin motar yayi yace
"Hajiyata barka da asuba kece da sassafe haka? halan an kawo emergency patients ne?" Ya jero mata tambaya gaba d'aya kamar d'an jarida.
Fuska d'aure ta kalle shi
"Lafiya lau sannan, kuma abinda yasa nake zama a cikin Asibiti kenan d'an kula da patients, Malam bana son kana shiga hurumi na da yawan tambaya""My Doctor kenan, ni tambaya na miki ba bak'ar magana ba, Dr Fadeela ina so ki sani duk cije-cijen ki wallahi ina sonki bazan janye k'udurina akanki ba"
Guntun murmushi tayi tare da zabga masa harara
"Malam Bilal kana b'atamin lokaci sakar min marfin mota in tafi""Bazan saki ba sai na gama magana ta, anjima da k'arfe hud'u zanzo mu fita shan ice cream daga nan kuma ina buk'atar lasar zumarki hop ba damuwa?"
Wani kululun Abu taji ta taso ya tsaya mata a mak'oshi, fitowa tayi a motar ta zabga masa mari
"In har ba zaka koyi iya magana ba to ni kuma bazan daina marin ka ba, fasik'i mara hankali ka sani ni nafi k'arfin iskancin ka sannan zuma ta bana irinku sha-sha-sha bane, zaka mutu baka lasa ba"
Dafe yake da kuncinsa yana wani irin murmushi mai ma'anoni da yawa ya matsa sosai gab da ita suna jin numfashin juna
"Wannan shine karo na uku da kike sanya hannunki masu laushi kika mare ni, har gobe ba zanji haushinki ba saboda kina da abubuwan da nake so wanda dole bazan iya d'auke idona akansu ba har sai na mallakesu.
KAMU SEDANG MEMBACA
K'ARSHEN MAKIRCI (Nadama)
RomansaFarida ce ke tsula gudu a mota hawaye ya wanke mata fuska jikinta yana rawa ta kira number Nura, bugu d'aya ya d'auka ta tari numfashinsa da sauri "Nura, Nura wallahi bai mutu ba yana nan a raye, yanzu na ganshi a Asibitin Mahaukata na nan cikin Ab...