*ƘARSHEN MAKIRCI*
_(Nadama)_Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 5.
Duk kallonsu ya koma gurin Abba, Fadeela taji wani abu ya tsaya mata a k'ahon zuciya nan take kwayar idonta suka sauya kala zuwa jaa, juyawa tayi tabar falon a fusace ta nufi d'aki, Abba ya kwala mata kira amma tayi biris dashi ta shige d'aki tare da rufe k'ofar da key, ta aje jakarta saman gado ta shiga toilet ta kunna ma kanta shawa da kaya a jikinta ruwan na ratsa kwanyarta tare da bin sassan jikinta ko hakan zaisa taji salama, ta d'auki minti sha biyar a haka daga bisa ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sai ta kashe shawar ta cire kayan jikinta tayi wanka kana ta d'auro Alwala ta fito.
A falo kuwa Abba ya soma magana cikin fad'a
"Yanzu irin Tarbiyya da muka yi muku kenan? Duk iya k'ok'arin mu akan ku zama tsintsiya mad'aurinki d'aya ashe aikin banza muke yi, kanku a had'e yake tun kuna k'anana a haka kuka taso sai yanzu ne da kuka girma shine kuke so ku watsa mana k'asa a ido.
Ke Kausar ya dace ki gayawa 'Yar Uwarki haka? Yau ko wani kika ji ya fad'a mata haka ai sai inda k'arfinki ya k'are, shi aure hauka yake k'arasawa ashe da rashin Hankali bansani tunda gashi kin nuna mana, nayi zaton kinyi hankali ashe da saura, gashi nan kinyi mata rashin kunya shima Abdul ya miki gaba d'aya kun raina kanku kenan?
To wallahi bari kuji doka ce daga yau karna sake jin irin wannan abun sannan dole ki bata hak'uri, koda muke takura ta akan zancen aure bawai bama sonta bane, soyayyar ce tasa muke mata haka amma daga yanzu ba zan sake matsa mata ba in lokacin yayi da kanta zata kawo min zancen. Kai kuma Abdul"
Ya maida kallonsa gareshi,
"Ka fita idona kafin na rufesu in ba haka ba duk saina sassab'a muku".
Ya mai da kallonsa ga Ammi
"Kema da laifinki domin k'arara kike nuna rashin adalci a tsakanin su, to Kul na kuma jin an kuma tado maganar Auren Fadeela, da farko laifina ne dana nima takura mata to yanzu karna kuma jin kin fad'i mata magana mara dad'i Addu'a zamu bita dashi, sannan wannan lamarin tsakanina ne da 'yata babu ruwan kowa a ciki na gaya miki".
Duk suka yi jugum-jugum Ammi ranta ya kuma b'aci, sanin halinsa yasa tayi shuru in ba haka ba sai ya kwance mata a gaban Yaranta ya bata kunya, sanin kanta ne in ransa ya b'aci ko gaban uban waye jizgata yake, gashi yanzu ma kusan hakan ne ya tasata a gaban Yaranta yana mata fad'a.
Kausar ta shiga dana sanin furucin da ta yiwa Fadeela ta kuma d'auki k'udirin zata bata hak'uri, nan Abba ya cigaba da yi musu Nasiha suka bashi hak'uri da alk'awarin ba zasu kuma ba.
Fadeela ta gama shirinta caf tayi Sallar La'asar da aka kira, jakarta ta d'auka tabi ta bayan kitchen, mai gadi ya bud'e mata gate ta fita saida tayi tafiya kad'an saita turawa Abdul text
_"Bro ina waje ka fito da mota ka kaini filin jirgi zan tafi, karka sake kuma ka fad'a masu Ammi"_
Abdul yana gurfane gaban Abba dake musu nasiha, k'aran sak'o ya shigo wayarsa ya bud'e sai ya karanta, murmushi yayi a zuciyarta
'Hooo Anty Fadee ta d'au wuta' a fili kuma yace tare da d'ago kai
"Ammm Abba zanje kafe yin browsing wani Assignment da aka bamu a school, Abokina yana jirana a waje"
"To ba damuwa Allah yayi muku albarka ya bada sa'a tashi ka tafi" Abba ya furta haka.
Cikin sauri ya mik'e ya bar falon yana jin Abba na cewa
"Hajiya duba Fadeela ki kira ta tazo nan muyi magana nasan k'ila yau zata koma Abuja"
Abdul yayi murmushi wanda ya bayyana hak'oransa domun yanan kwanan zancen, ya isa wurin parking spice ya shiga mota mai gadi ya bud'e masa ya fice da sauri.
YOU ARE READING
K'ARSHEN MAKIRCI (Nadama)
RomanceFarida ce ke tsula gudu a mota hawaye ya wanke mata fuska jikinta yana rawa ta kira number Nura, bugu d'aya ya d'auka ta tari numfashinsa da sauri "Nura, Nura wallahi bai mutu ba yana nan a raye, yanzu na ganshi a Asibitin Mahaukata na nan cikin Ab...