page 6

536 20 11
                                    

*ƘARSHEN MAKIRCI*
_(Nadama)_

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 6.

Abuja.

_Washe Gari Ranar Laraba_

Babban Asibitin Mahaukata (psychiatry) dake cikin garin Abuja cike yake da Al'ummar Annabi kowa na hada-hadar sa. Manyan ofishoshi ne jere guda biyar duk d'auke suke da manyan Likitoci a ciki suna ganawa da marasa lafiya da suka zo (Out Patients). Dr Fadeela Umar tana d'aya daga cikin Likitocin kuma Matasiya wacce ake ji da ita a duk fad'in Asibitin saboda kwazonta da kuma sanin makamar Aiki, kyakkyawa ce mai kyau da Ado wacce ba zata wuce shekara Ashirin da takwas ba a duniya, zaune take a cikin Office d'inta tana gudanar da wani bincike a na'ura mai kwakwalwa bayan ta kammala ganawa da Marasa lafiya kimanin Mutane guda Ashirin da biyu. Tana tsaka cikin aikinta Malam Habu ya shigo office d'in tare da yin Sallama sai ya samu guri ya zauna a kan kujerar da yake fuskantar ta.

Dr Fadeela ta d'ago kai ta kalle shi cike da murmushi a fuskarta tace
"Sannu da zuwa Baba"

"Yauwa 'Yata ya Aiki, ya mai jiki kuma?"

"Alhamdulillah, jikinsa da sauk'i har yanzu dai baya magana Abinci ma baya ci da kyar yake karb'ar Tea"

Jinjina kai Baba yayi "Allah Sarki, Allah ya bashi lafiya"

"Ameen Ya rabb, Yauwa Baba, Alhamdulillahi result d'insa ya fito sai dai ina so kayi hak'uri da duk abin da zan fad'a maka, shi dai ciwo Allah yake saukar dashi tare da maganinsa, a bisa ga dogon binkicenmu da muka yi masa, hakan ya tabbatar mana da cewa ya samu tab'in hankali a kwakwalwarsa, ma'ana yana d'auka da ciwon hauka"

A razane Baba Habu ya d'ago kai ya kalleta yana Ambaton "Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un, Hauka kuma?"

"Eh Baba sai dai tunda ba dashi aka haifeshi ba insha Allah zamu d'aura shi bisa magani da yardar Allah zai dawo cikin hankalinsa"

Idon Baba ya kawo kwalla yace cikin rawar murya "Allah sarki bawon Allah kaga jarabawa Allah yasa kaci ya baka lafiya mai d'aurewa"

"Ameen ya rabb, dan haka yanzu zamu bashi d'aki daga cikin gidan majinyata dake ciki wannan Asibiti insha Allah zai samu kulawa mai kyau, kai kuma lokaci zuwa lokaci saika zo ka duba shi, a yanzu baya buk'atar komai sai Addu'a".

"Hakane 'Yata ni ba abin da zance miki face fatan Alkhairi da gamawa da Duniya lafiya, Allah ya Albarkaci Rayuwarki, hak'ik'a kin min karamci" sai ya k'arasa maganar yana kuka.

"Haba Baba nima fa 'yarka kace kamar yanda yake d'a a gunka, duk abin da nayi maka na yiwa kaina ne, ga number ta a cikin wannan paper zaka iya kirana duk lokacin da kake buk'atar sanin halin da yake ciki"

Baba ya amsa yana shi mata da Albarka.

"Emmmm Baba baka gaya min sunansa ba?"

Dammm zuciyar Baba ta harba, cikin rawar murya yace "Imamu" nan take sunan ya zo masa a rai.

"Masha Allah, nagode Baba Allah ya kaika gida lafiya zaka iya zuwa ka duba shi kafin mu sauya masa d'aki" ta k'arasa maganar tana duba file d'in Imran a system, nan take ta sauya sunansa da Brother Imam.

10k ta ciro a drower ta mik'awa Baba
"Ga kud'in mota da zaka rik'a zuwa dan ba lallai bane ka sameni kullun"

Ba musu Baba ya amsa dan yana cikin buk'atarsu, yayi mata godiya ya fice cike da jinjina karamci irin na Doctor Fadeela.

Baba d'akin Imran yaje ya k'ara duba jikinsa, ya shiga jero masa Addu'a dan samun lafiya, daga bisani yayi wa Khalil godiya sai ya wuce zuciyarsa cike da damuwa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 23 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

K'ARSHEN MAKIRCI (Nadama)Where stories live. Discover now