🏢GIDA BABBA🏢 By Mrs Mz

794 22 0
                                    

Asali mu mummy Fulani Cameroon ne aiki ne ya kawo iyayen ta nan yola tun yana gongola.
Hajiya Bilkisu mace ce mai kyau ga fari da sayo gashi
Bata da damuwa ko kadan don ko hajj Bilkisu kowa na ta ne. Ga uwa uba tana da kirki sosai, abin duniya sam bai dame ta ba. Don ta taso a ciki kudi mai yawan gaske saboda mahaifi ta babba mai kudi ne a Cameroon don ko zuwa shi Adamawa aiki ne ya kawo shi Wanda yake yi shi da wasu turawa aprofil
Harka tayi kyau sai turawan suka nuna cewa ya dan zauna mana . a nan ne Alhaji Audu berema ya zauna
A Adamawa tun tana gongola har ta zama Adamawa
Zaman tai mai dadi har ya sayi fili yayi gini na a zo a gani. Alh Audu.B yayi tashi suna a Adamawa don ba
Wanda bai San da shi ba, in ba fada ma ba sai kace shi dan Adamawa nema.
Tunda Alh Audu.B ya bar Cameroon bai wai waye su ba har sai da yakan shekara biyar a Adamawa. Iyaye shi suka matsa mai ya dawo kasar shi don su a gani su bariki ba wurin zama bane, ga babba damuwa su bashi da aure gashi matashi. Mama Babba ita ce mahaifiya Alh Audu.B shine dan ta na farko kuma dan na miji. Su goma sha biyu mahaifi su ya haife su. Mahaifi Alh Audu.B wato Alhaji berema yana da mata uku . Matan shi ta farko wato hajiya hauwa Wanda yara suke ce mata mama babba yara ta biyar Alh Audu shine dan ta na farko , sai hajiya Rakiya, sai hajiya Amina, sai hajiya nana, sai Auta ta Alhaji Ahmed. sai mai bi mata mama karama itama yaran ta hudu. Akwai Alh sadiq, sai hajiya fati , sai hajiya Aisha, sai hajiya Ramatu. Sai ta ukun Shukurah itama yaran ta biyu. Akwai hajiya rukaiya da Alh jamilu. Mama babba ta damu sosai taga dan ta kuma na fari yayi aure Shisa ita da Baba duk su damu suga Alh Audu yayi Aure.
Mama babba tace wai kai haka za'a sa ma ido kaki aure? To wallahi in baba Shi bai ce komai ba ni zan je wurin shukura ta samo ma mata.
Haba Shi kenan kai ko yaushe ai ta. Maimaita abu daya ! Ni ko dai so kake mu mutu kafi kayi aure?
Haba don Allah, ba a fada da kai sai anzo magana aure. Ni dai na fada ma in kana so mu shirya ka fito da mata.
Alh Audu yace insha Allahu mama zan fitar da mata
Kawai dai har yanzu ban samu matan bane
Amma Ina samu sai aure .
A to fada mata dan nan. A ce mutum ya ta zuba ba dalili inji Baba ai shi aure lokaci ne in lokaci shi yayi
Sai kiga anyi har a mata ma.
To na fahimce ka Allah yayi masu albarka.
Amin Amin. Inji baba Addu'a da ya kamata kina yi masu kenan.
A haka Alhaji Audu.B yayi hutu sa ciki yan'uwa shi gwani dadi har ya dawo Adamawa.

ADAMAWA
Ni gaskiya umma Na gaji da zuwa taya Adda Amina aiki ko naje ba mu shiri mun ta fada kenan sai ka ce a kanta aka soma ciki in ji Halima.
Umma ta aaah lalle dole ki ce haka ki fada mun hali dubu in baki je kin taya yar'uwa ki aiki ba wa kike so ya taya ta? Ai fadan nan da kike gani ba laifi ta bane,
Tana haihuwa zata dai na. Ke da ta fada min takwara zata maki, yi maza ki je gidan yar'uwa ki yauwa hali dubu na.
Umma haka koyaushe kike fada min ni gaskiya na gaji inji halima.
To wallahi baki isa ba, tunda ke baki jin magana
A ce mutum da dan'uwa shi , ki fada min in baki je ba ni kike so naje? Wallahi maza ki ta shi tunkan a ji mu ja'ira yau da kin fitar da miji wa ma zai tura ki gidan wata.
Halima tace ni umma kun dame ni da fitar da miji .
Komai miji !miji!! Miji!!! Ohh Allah ka fito min da
Nagari ko don na huta da su umma.
Umma ta kwashe da dariya tace miskila ace kina so aure. Hmmm umma kenan ai ko don gori ki da na Abba dole na fitar da miji.
Halima ta shiga daki ta shirya ta sa hijabi ta fito tama umma sallama ta wuce.
Ta fiya tace a nitse kanta a kasa tana wasa da hannu ta sai taji horn na mota bata juya ba don a kan hanya take.
Sai da taji horn ya tsanan ta sai ta juya don duba hanya. Innalillahi abin da ya fito daga baki na
Ya salam!!! Kafi ta gama ya salam sai taji ana cewa na baki tsoro ko. Ni mai zan ce na fada a zuciya na?
Ko nace a ko aa? Ohh ya Allah wanan wani irin mutum ne haka?
Ba tsammani naji yana cewa duk abu mai kyau bai dace da yana yawo a kan titi ba.
Ban San lokaci da nace hanya dai don ni ba a titi nake ba.
Sai yace da zai fi kyau kizo na rage maki hanya.
Bana shiga moto mutane.
Ai ba mutum bane mijin ki ne.
Ta ya ka zama miji na?
Yau kuma yanzu.
Don Allah ki shiga na rage maki hanya.
Ni sunan na Alhaji Audu .B
Audu .B??? Abin da zuciya na ta fada min kenan
Iko Allah lalle yau na fito da sa'a sai naji yace don Allah ki shigo na rage maki hanya.
Na bude murfi gaban mota na zauna nace Ina yini
Lafiya lau .
Ko zan San sunan malaman?
Suna na halima
Kice mai dubu hali
Nayi dariya nace na gode.
Don Allah Halima Ina so Ki fahimce ni ba da wasa nazo maki ba. Don Allah Ina so ki bani hadi kai
Tun da nagan ki naji kin min kuma ina so in hada zuri'a da ke ina fatan zanji alheri?
Ba komai Allah tabbatar mana da alheri
Amin Halima na
Nayi dariya na sukunar da kai na.
A haka har muka iso gidan Adda Amina .
Halima nan ne gidan ku?
Aa ba gidan mu bane gidan yar'uwa nane bata jin dadi shine naxo taya ta aiki.
Aiya Allah bata lafiya , karfe nawa zaki koma gida?
Bayan isha'i. Ok ba damuwa ga number na sai ki min flashing sai na dawo na kai ki gida.
Aa nagode ba sai ka dawo ba.
Ni dai sai in har ba a amince da ni ba.
To ba damuwa in na gama zan fadi ma nagode
Nine da godiya Queen,
Murmushi nayi na shige ciki gida Adda Amina
Bai tafi ba har sai da yaga na shiga.
Salamu alaikum !!!
Wai ke Halima ma baki girma ne? Haba don Allah
Mutum na dan barci shi kin tashe shi,
Haba don Allah Adda wallahi da kin San mai ya sani ihu da kema kin taya ni.
Allah ya tsareni da ihu da tsakar ranan nan.
Ni duk ba wanan ba ya naga duk yau sai wani murna kike yi?
Hmmm ke dai bari Adda , yau dai Allah ya amshi addu'a ko.
Ban gane ba, har kin sani bude ido. Yi sauri ki sanar da ni😂
Hmmm Adda Amina yau nayi saurayi🙈
Saurayi kuma? Kedai baki wuce shirme to sai me
Ai dama yanzu lokaci yin saurayi ne. Kuma kinsa su
Abba basu so tara samare nan, su fi so in kinga wanda ya maki sai ki tura gida yayi sallama da su.
Amma ko ni ban baki shawara tara samare ba don ban ga amfani shi ba.
Ya na ga kin bar ni sai zuba nake tayi kina dariya
Wato ga mahaukaciya ko? Zaki sani
Wallahi Adda ba haka bane cemin yayi shi da aure na yake so na. Shisa yace zai zo bayan sallah isha sai yaga gidan mu sai ya gaida Abba.
Iko Allah. Yanzu hali da kanki kike fadi haka? Baki San mutum ba har kin aminci ki mai isowa gidan ku
Don yaranta?
Wallahi Adda A. Ba wani boyayye bane an sanshi fari sani ma kuma hali shi ba boyayye bane don in kana garin nan dole kasan waye Alhaji Audu.B.
Alhaji Audu.B😳 don Allah hali ki rufa mana asiri
Kin San Abba Sarai ba lalle bane ya yarda kuma kema sani kanki ne Alh Audu.B ba dan nan bane .
Wallahi anty Ina so shi gani daya nayi mai yau kawai Amma ji nake yi in har ban aure shi ba zan samu damuwa.
Iko Allah hali sai dai nace Allah daura ki kan Abba Amma bana tunani amince wa Adda.
Adda Amina ki taya ni da addu'a insha Allah Abba zai amince. Yau mai kike sha'awa ci?
Hmm hali ni duk jiki na ya mutu bana jin ci komai sai da ko ke da kabir.
Laaa dama uncle kB na gida nata zuba haka?
Yana nan yana jinki tun danzu yake kofa baya so ya kase mana hira ya koma ciki.
Lalle Adda kiyi dani. Yanzu duk abin da na tacewa yana ji na.
Hmmmm Ina ruwa Auta mama ai ba abin kunya kika fadi ba , gaskiya kika fadi nafi so ki bar komai a hannu na da kai na sai na fada ma Abba Duk Wanda naji a hiran naku.
To ba damuwa uncle kB nagode Sosai.
Ina yini ya jikan Adda?
Lafiya lau Auta, jiki da sauki da taimako ki.
Kar ka wani ce da taimako ta kafi ta ji kanta.
Laaa Adda haka zaki ce ko?
Kyale Auta yi girki ki barta ai ta San kina taimaka mata.

Yanzu ace ka haifi mutum baka haifi hali shi ba.
Malam wani abu ne inji umma.
Ina fa lafiya yanzu nan na idar da sallah sai naga bako bayan mun gaisa shine yace wai hali ce ta mai iso wa. Abin ya min dadi har ga Allah don haka Adini yace a yi, kafi ka fara gani yariya sai ka sanan ma magabatar ta. Amma sai me. Auta ta Debo mana ruwan dafa kanmu.
Ni malam kana ta jawabi ban gane mai ka ke nufi ba.
Haba Asabe kina nufi kema Auta bata fadi maki abin da ta ke ciki ba.
Ni ba abin da ta fada min, danzu mun rabu da ita zata gidan yar'uwa ta Amina ko dai wani abu ta yi ma Amina ? Don da kyar ta tafi wai ta gaji.
Asha asha.
Malam kayi min bayani mana?
To ba komai bane ita Auta ta turo min saurayi yaxo Neman izini ya fara zuwa hira wurin ta. Amma abin gudu a nan kin San wa ta kawo?
Malam wa ta kawo! ?
ALHAJI AUDU.B
Innalillahi wa inna ilaihim raji'un!!! Malam ita Auta ?

GIDA BABBA by mrs MZHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin