*JAGORAN AHLUSSUNNAH*

284 3 0
                                    

📚 Wallafar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

*Fitowa ta 1*

 
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Gabatarwa*
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta; shugaban mu, jagoranmu, masoyin mu kuma abin koyinmu Annabi Muhammad dan Abdullahi, tare da iyalan sa da almajiran sa da masoyan sa masu bin sawun sa har yaumut tanadi.
Wannan littafi na daga cikin albarkatun Madina birnin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Domin a cikin ziyarar da na kai ma wannan birnin ne domin samun tubarrakinsa kafin Hajjin wannan shekara ta 1438H Ubangiji mai rahama ya cusa min son rubuta littafin, nan take na shata yadda zai kasance sannan na fara rubuta shi. Bayan da muka kammala aikin Hajji lafiya sai na dukufa ga wallafa shi a nan birnin Makka mai daraja kafin komawa gida.
Makasudin wannan littafi shi ne ya zama jagoran sanin tafarkinmu na Sunnah wanda muke jinginuwa zuwa gare shi, bayan la’akari da yadda akai akai wasu bata-gari suke fitowa da soye-soyen zukatansu wadanda suka tsakuro daga wasu ‘yan Bidi’a na baya, sai su jingina wannan son zuciyar nasu zuwa ga tafarkin Sunnah don ya samu karbuwa. Babbar damar da suke amfani da ita ita ce, rashin tantancewar mutane ga wannan tafarki da karancin sanin su ga hanyoyin da ake bi don tabbatar da magana ko kore ta a cikin sa.
Tafarkin Ahlus Sunnah ba wani abu ne na daban ba sai karantarwar Musulunci tsantsa. Duk abinda ya saba ma ta ba ya cikin tafarkin Sunnah ko da kuwa wasu daga cikin Ahlus Sunnah sun rungume shi bisa rashin sani ko son zuciya ko wani ajizancin dan Adam na daban. Jinginuwa ga tafarkin Sunnah shi kadai ba ya tsarkake mutum har sai aikinsa ya zama bisa godaben da jagoran wannan tafarki ya shata, shi ne Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam. Mun sha fadi muna maimaitawa cewa, zama memba na wata kungiya ta Sunnah ko limami na wani masallacin Sunnah ko shugaba a wani aikin alheri irin na Ahlus Sunnah, duk ba su ba mutum damar yin gaban kansa ya kirkira wani abu a cikin addini ko ya shata wata hanya wacce ta yi hannun riga da ta Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam.
A cikin wannan *Jagora* an taqaita ne kawai ga kawo manya manyan ka’idoji wadanda Sunnah ta ginu a kan su, wadanda kuma ta hanyar bin su ne kadai mutum yake iya zama Ahlus Sunnah, da bin su ne kuma kadai ake iya auna kusancinsa ko nisan sa da wannan nagartaccen tafarki mai albarka. An rubuta ka’idojin ta yadda za su yi saukin hardacewa, aka biyo bayan kowace ka’ida da takaitaccen sharhi wanda zai bayyana manufarta da hujjojin da aka dogara da su wajen kafa ta. A bayan wata babbar ka’ida kuma wani lokaci akan kawo mata rassa wadanda ba lalle ne su bukaci wani sabon sharhi ba.
Wannan littafi, kamar yadda Hausawa ke cewa: *_Ba ni na kashe damo ba rataya aka ba ni_*. Ba ni da wani abu a ciki wanda na zo da shi daga tunanina ko ra’ayina. Na tattaro abubuwa ne da malaman Sunnah na lokutta daban daban suka rubuta su a cikin littafansu game da wannan tafarki.
Allah nike roko ya sa ya zama mai amfani ga duk wanda Allah ya ba shi ikon karanta shi.
Godiya ta musamman ga shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau bisa ga karfafawar da ya yi mini a kan wannan aiki, kasancewar muna tare da shi a wadannan lokutan tun daga Madina har a nan Makka. Babu shakka, na samu kwarin guiwa matuka da karfafawar sa. Ina kuma rokon Allah ya kara yi masa jagora wajen sauke nauyin da yake dauke da shi, ya kara masa lafiya da basira da mashawarta masu tsoron Allah da hangen nesa.
Alhamdu Lillah.

*Baban Ramla*
A Birnin Makka
12 ga Dhul Hijja 1438H

MATSALOLIN MA AURATADonde viven las historias. Descúbrelo ahora