🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*NI DA YAYA AL'AMEEN*
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*STORY AND WRITING*
BY
*RAHEENAT M ABBAKAR*
_(Heenat)_
Whattpad
@rahinamustaphaMARUBUCIYAR
*1 KOMAI YAYI FARKO....*
*2 HALIN RAYUWA*
*3 RAYUWAR SAUDA*
*4 RAYUWAR HANEEFA*
*5 MAHAK'URCI....*
*6 RUK'AYYATU*
*7 RAINA FANSA NE GARETA*
Loading.... *NI DA YAYAH AL'AMEEN*SADAUKARWA GA
*MAMAN LABYB (MAMIEN MU)*
*FAUZEEYYA MUHAMMAD WAKILI*
*SHAFA'ATU BALA BABA*
*ADAMA TANIMU A BIYE*
*AISHA NICHOI**🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A W)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛'''Page 6
Har lokacin Al'ameen yazo d'aukarta cika take tana batsewa, bayan sun d'au hanya ne ya kalleta cike da kulawa yace "waye tab'a gimbiyar Al'ameen ne take fushi haka.?"
Kallonsa tayi sannan ta kau da aki gefe tare da sakin wani dogon tsaki tace "aikin banza, ni wallahi bana son zub da aji, ai wannan zubar da aji ne da kimar ya mace. "
Shi dai Al'ameen ya tabbatar ko giyar wake Meenat tasha ba zata fad'a masa wannan maganar ba, dan haka yace "dawa akeyi kuma my meenat.? "
Turo baki gaba tayi wanda ya riga ya zamar mata jiki dan Meenat shagwab'ab'b'iya ce number d'aya tace "Suhailat ce mana. "
D'an k'ara girman idonsa yayi yace "yau kuma me ya had'aku da aminiyar taki.?"
Tsaki ta k'ara ja tare ta cewa "rabu da ita kawai yayah, to wai nima ina ruwana ne dan tace ..."
Sai kuma tayi shiru.Al'ameen yace "dan tace me.?"
Shiru tayi zuwa can kuma tace "babu komai. "
Murmushi Al'ameen yayi yace "ni dai nasan k'anwata bata b'oye min komai, wannan d'in ma ina zaman zamana nasan za a gaya min. "
Murmushi itama tayi ba tare da tayi magana ba, haka suka ci gaba da tafiya babu wanda ya k'ara magana cikinsu har suka k'araso gida.
***************
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, kwanaki suna shud'ewa suna zama sati, sati yana zama satittika a haka aka kwashi watanni biyu da rabuwar Salis da Meenat, zuwa lokacin Meenat tuni ta cire wani Salis a babin rayuwarta, yayin da b'angare d'aya kuma shak'uwa tare da soyayya ke k'ara k'arfi tsakaninta da yayanta, ana cikin hakane kuma ta haɗu da wani guy me suna Kamal, sun haɗu da Kamal ne a sahad store taje siyayya, ranar basu fita da Al'ameen ba direba ne ya kaita sakamakon aiki da ya riƙesa a hospital, tunda Kamal ya ɗaura idonsa akan Meenat yaji ya kamu da sonta, be tsaya ɓata lokaci ba ya tinkareta, farko dai Meenat taƙi sauraransa, dadai ya isheta da naci ne ta sauraresa har ma ta basa number wayarta, nan suka rabu yace zai kirata, koda Meenat ta dawo bata faɗawa Al'ameen haɗuwarta da Kamal ba, dan haka kawai taji ba ta son faɗa masa yanzu.
A wannan daran Kamal ya kira wayarta, kuma wasa wasa sun ɗauki lokaci dashi suna waya, sosai Meenat ta saki jikinta dashi kai kace sun daɗe da haɗuwa ne.
Yau ta kama asabar Al'ameen ne tare da Meenat suka fito cikin shiga iri d'aya, wata arniyar shadda ce coffee colour ajikinsu me d'an karan kud'i, d'inkin da akayi ma shaddar kad'ai ka kalla kasan kud'i yayi kuka a gurin nan.