💞 NOOR
10
Baya nayi tare da kare kaina da takobin dake hannuna banyi aune ba naji na zube gaba daya a kasa, tashi nayi hade da kakkabe jikina.
"Ki nutsu" shine abinda naji ya fada .
Gyara tsayuwata nayi sosai na riqe takobina da karfi, sara na kai mishi ya kare na sake kai mishi ya kare, zuciya nayi na fara fadan kaman a filin daga. Sosai muka galabaita daga ni har shi amma zuciyar sa cike take fam da mamakin yadda akayi na iya yaki sosai haka, kasa daurewa yayi har sai da ya magantu.
"A ina kika koyi fada haka" yayi tambayar yana tsareni da ido.
"A gurin mahaifina" na fada ina maida numfashi.
Hango inda na ajiye ruwa da tiren kayan shayi nayi a gefe, zuwa nayi na tsiyayo mishi ruwa na kawo, ba musu ya karba ya shanyeshi tass. Kofin ya mikomin tare da fadin na karo, sake tsiyayo ruwan nayi na mika mishi amma sai yaki karba, tsayawa nayi da ruwan a hannuna.
"Ki shanye" shine abinda naji ya fada, badan nasan muryarsa ba da nace bashi yayi maganar ba.
"Kayi hakuri ranka ya dade amma bai kamace ni ba shan abu daga wanda gasha" na fada ina dan sunkuyawa.
"Sha" ya sake maimaitawa, ba yadda zanyi dole haka na shanye.
Takobinsa ya mikomin tare da fadin "biyo ni" ba musu na fara binsa har muka shiga sashensa, naga munbi wata kofa da nake da tabbacin hanyar dakinsa ce. Wata kofa Ya bude ya shiga ni kuma na tsaya a waje, wani sassanyan kamshi naji ya doke hancina na dago kaina, tabbas dakin ya kayatu matuka, nan na shagalta wajen kallon dakin.
"Shigo" itace kalmar da naji, gabana ne ya fadi amma sai na dake na shiga ciki. Kallona yayi sannan yace "ki kwantar da hankali ki, gyaramin daki zakiyi"
Fita yayi daga dakin, nan na fara gyara gadon na hada kayan wanki na fita dasu. Gurin wanki na tafi dasu, ina zuwa na shaida musu kayan Yareema Ameen ne, wani ya taso da saurinsa ya karba. Daganan garwashi na samo na kunna turaren wuta, ko ina na dakin ya dauki kamshi, fita nayi daga dakin tare da rufo kofar.
Abu na taka na aikam na tafi gaba daya zan fadi, ji nayi an rikoni ta baya, murmushi na saki ganin Yarima
Ameen ne, kasa dauke idona nayi diga fuskarsa. Ji nayi yace "Sakeni ko?" Sakeshi nayi da sauri tare da fadin "ni nace ka riqeni? " a zuciya ta.
"Bake kika ce ba" ya fada ba tare daya juyo ba.
Kunya ce ta kamani hadi da tsoro, nasan a zuciya ta nayi maganan amma ya akayi yaji? Bani da mai bani amsa don haka na wuce abuna.Ina shiga daki nabi lafiyar gado na kwanta don dama a gajiye nake. Cikin baccina naji an shafamin ruwa a fuska hadi da kiran sunana, sake juyawa nayi na cigaba da baccina. Ban farka ba sai karfe 2, sauri nayi na dauro alwala nayi sallar azahar. Bayan na idar ina nade sallayar idona ya kai ga wata takarda ajiye gefen gado na, dauka nayi na bude na karanta
"Ki sameni a bangarena bayan la'asar. Fu'adu." Yar dariya nayi ganin yanda ya rubuta sunanshi."Barde" Sarki Ahmad ya fada.
"Na'am Allah Ya ja zamaninka" Barde ya amsa masa.
"Kai amintacce ne a gurina duk da haka banason kamin karya duk da nasan baka taba ba. Mecece gaskiyar maganar da naji gurin Zannun?" Sarki ya fada a kausashe.
"Ranka ya dade, Allah Ya ja zamaninka! Duk abinda ya fada haka yake don ni da kaina nasa akamin binciken amintaccen bawansa kuma haka take shima a gurinsa"
Barde ya fada da sanyin murya gudun kar yayi laifi.
"Barde! Duk wani wanda yake da sa hannu a ciki a kawomin kanshi, a kawo min kan Haruna (sarkin Milan)
data zuri'arsa, ban dauke kowa ba sai Fu'ad shima yaci darajar abotarsa da Alkassim" Sarki ya fada hade da daga murya.
"Angama ranka ya dade Sarkin sarakuna" Barde ya fada fuskarsa dauke da bacin rai amma can ciki murna fal ransa.Bayan na idar da sallar la'asar sashen Yarima Fu'ad nufa, a bakin kofar na jira aka bani iso na shiga. Zaune yake bisa wata kujera yana murmushin nan nasa, kasa kallonsa nayi nayi kasa da kaina. Dayar kujerar ya nunamin alamar in zauna, ba musu na karasa na zauna hade da gaiseshi ya amsa.
Kallona ya tsaya yi, nayi saurin cewa "Yarima Ameen bai ce komi game da tafiya ta ba"
"Karki damu ya fadamin cewa kin amince sabida haka kin zama tawa amma bana tunanin Ameen zai barki" ya fada yana murmushi.
"Kamar yaya fa?" Na tambaya
"Karki damu" ya bani amsa tare da jingina bayansa jikin kujerar da yake. Shiru ya ratsa tsakaninmu kamin ya sake cewa "Ki fadama yan'uwanki su shirya yau da daddare zasu tafi"
"To" na amsa jiki a sanyaye. Jin haka ya sashi sake magana "Mage kina ta bacci dazu nazo tashinki sallah, kina kyau da bacci" ya fada yana kafeni da ido.
"Bansan kazo ba ai" na fada kaina a kasa.
Baice komai ba, na mishi sallama na fita neman su Mimi.#Follow
#Vote
#Comment
YOU ARE READING
💞NOOR
General FictionStory of Noor and the 5 princes of Ming Empire. Betrayal among them and read as love turns to hatred.