21

1K 84 1
                                    

*'YAR SHUGABA*👑

_page_ *21.*

_Na_
_*Rahma Kabir*_✍🏾

Shuru suka yi suna sauraren kukan Basma, tausayinta ne ya kamasu, Ammi ce tace
"to shikenan, ni ina ganin gaba d'aya wannan abun rashin fahimta ne, dan haka sai a sulhunta su komai ya wuce, sai su tafi, Dady yace
"kwarai kuwa abinda ya kamata ayi kenan"

Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga bisani ya d'aura da cewa
"President banji dad'in yanda ka d'auki wannan lamari da zafi ba, da har ka furta mummunan kalma ga Hajiya Maryam, in hankali ya gushe ai hankali ne ke nemoshi, dan Allah mu rik'a kai zuciya nesa, duk sai mu taru muyi hak'uri komai ya wuce, kai kuma Shureym kaji tsoron Allah, in har kana cutar da ita Allah ba zai barka ba"

Abba yayi wa mai Martaba godiya, ya soma yiwa su Basma nasiha, bayan ya gama yace
"Basma kije part d'ina ki jirani, kai kuma Shureym ka shirya zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe zaku koma, shikenan zaku iya tafiya"

Haka suka watse kowa da damuwa a ransa, Amma banda Shureym da Maminsa wanda zuciyarsu yayi haske tunda an kashe magana ba tare da Basma ta tona komai ba, duka Matan suka wuce part d'in Momy, anan suka bar Mazan suna tattaunawa.

Yaya Ahmad yabi bayan Basma suka zauna a falon Abba, ya kalleta cikin nutsuwa yaga duk ta rame haske kawai ta k'ara, yace
"Basma me Shureym yake miki, ki gaya min gaskiya fa, dan bana son k'arya" guntun Murmushi tayi tace cikin sanyin murya
"Yaya Ahmad babu komai, kawai dai kasan halinsa na saurin fushi, anan ne muke dan samu sab'ani, amma bayan haka ba komai" kallonta yake cike da zargin abubuwa kala-kala domin sam bai gamsu da amsar da ta bashi ba, sai yace
"shikenan tunda ba zaki fad'a ba, in ya kusa kashe ki saiki fad'a" murmushi tayi tace
"Ni ba zai ma kashe ni ba" mik'ewa yayi yace
"bari na kawo miki abinci da maganin zazzab'i kisha, dan d'azu naga har kad'uwan sanyi kike yi" murmushi tayi race
"wlh Yaya tsabar shiga shock ne ya sani zazzab'i, amma ka kawo min zansha ko kaina zai rage min ciwo" harya fara tafiya sai tace
"Yaya d'an tsaya in baka ajiya" zage Jakarta tayi ta ciro wani k'arakin key guda d'aya, sai ta mik'e ta isa wurinsa tace
"Yaya dan Allah ka ajemin wannan key d'in inna tashi amsa zan maka magana sai ka bani" d'aga key d'in yayi yace key d'in miye ne wannan?" murmushi tayi tace na sirrina ne, ni dai ka ajemin wataran zan maka bayani akansa" gyad'a kai kawai yayi sai ya fita, tare da juya key d'in a hannunsa, yana tunanin ko na miye.

Abba ya samu Basma a sashinsa, zama yayi ya kirata, sai tazo ta zauna gefensa a k'asa, kanta ya d'ora bisa cinyansa, sai ya shiga yi mata fad'a daga k'arshe yayi mata nasiha, kuka Basma take yi mara sauti, a haka Yaya Ahmad ya samesu shima ya zauna ya zubawa Basma abincin ya mik'a mata yace taci, Abba ne ya kalle shi fuska a d'aure ya shiga yi masa fad'a akan abinda ya aikata d'azun, hak'uri Yaya Ahmad ya bashi da alkhawarin hakan ba zai sake faruwa ba, nan suka zauna suka cigaba da hira, har Basma ta kammala cin abincin kana ta mik'e zata fita da kulolin abincin, dakatar da ita Abba yayi yace
"Basma barshi Ahmad ya tafi dasu, ki hau sama kiyi wanka jakar kayanki yana d'akin kusa da nawa, anan zaki kwana" rau-rau tayi da idonta tace
"Abba ina son inga su Meena da su Ammi ne fa" murmushi yayi yace
"anjima in zamuci abincin dare zaki gansu, dan haka kiyi abinda na saki" hawaye ne ya ciko idonta, kawai saita haura sama zuwa d'aki, ta shiga rusa kuka sai da tayi mai isanta kana ta shiga bayi dan tayi wanka, zuciyarta na nazarin abinda yasa Abba ya hanata ganawa da 'yan uwanta.

Da dare Momy ce zaune a falon Abba sai Basma, magana Momy ta shiga yi tace
"Basma anya kina jin dad'in zama da Shureym kuwa? In yana miki wani abu ki gaya min" murmushi Basma tayi tace
"Momy ba komai" kallonta tayi sosai tace
"Basma ada ba kya b'oyemin matsalanki, amma meyasa yanzu zaki b'oyemin?" murmushi ta kuma yi tace
"Momyna ba komai fa" murmushi kawai Momy tayi tace

'YAR SHUGABADonde viven las historias. Descúbrelo ahora