Mafarin tushe

2K 61 3
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

*1*

BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM!

Ta ina zan fara? Asalinta ko cikin labarin zan shiga?

Ayshat d'iya ce ga Alhaji Mallam Yusuf, Alhaji Mallam Yusuf d'a ne ga sheikh Mustapha Ilyas Maiduguri wanda aka fi sani da Mallam Babba.

Su shida ne wurin iyayensu, Alhaji Mallam Yusuf shine babba, sai Alhaji Ilyas, wanda aka fi sani da Alhaji Ilyas Mustapha Ilyas, sai Hajiya Fanna wadda suke kiranta da Aunty Fanna, sai Uncle Ali, sai autarsu Aunty Yana.

Tunda kuka ji ance shehin malami kun san gidane na malamai, gidane daya taso cikin aminci da salama, gida ne da yake d'auke da k'aton makaranta da almajirai a ciki, wanda sassa daban daban da ciki gari ke cikinta.

Ba nan ta tsaya ba, harta 'yan cikin gari na zuwa cikin makarantar, Alhaji Mallam Yusuf shike kula da makarantar, dai-dai da almajiran dake ciki, ba a barinsu suje bara, abinda ya kawosu shi suke yi, sai dai idan ka girma kana da buk'atar sana'a da kanshi Mallam Babba yake d'aukan jari ya basu.

Baya barin almajiranshi cikin k'ask'anci wanda idan suka fita ma ba zaka gane almajirai bane, irin wad'anda malamansu suke barinsu a titi cikin datti da wahala.

Shi kam ba zaka ga nashi cikin haka ba. Alhaji Mallam Yusuf Allah bai bashi haihuwa da wuri ba.

Sai dai ya d'auko 'ya'yan 'yanuwanshi ya ri'ke, da sun girma su da kansu suke neman gidan iyayensu su koma.

Saida girma yazo mashi kana Allah ya bashi 'ya mace da taci sunan Hajja mahaifiyarsu wato Aysha suna kiranta da Humaira.

Alhaji Ilyas yana da 'ya'ya uku, Najib shine d'anshi na farko sai Jawad, da autarsu Maryam.

Aunty Fanna nada shida, Asiya, Fatima, Aliyu, Usman, Mustapha suna kiranshi Baba, sai Yusuf wanda tayi ma Alhaji Mallam Yusuf takwara.

Sai Aunty Yana tana da hudu, Lubabatu, Maimunatu, Bilkisu, sai Sani.

Auncle Ali kuma nada uku, Zainaba, Mariya, Sa'adatu.

Cike suke da k'aunar junansu, gaba d'ayansu suna cikin Maiduguri illa Alhaji Ilyas da yake zaune a kaduna.

Mahaifiyar Aysha Humaira 'yar asalin jihar Yola ce, ya samota dalilin zuwa neman karatu da yayi har garin Yola, dan Alhaji Mallam Yusuf yayi yawo gari gari, k'asa k'asa domin neman ilmin addini.

Kuma an dace da abinda aka je nema, dan shine ya gaji Mallam Babba a ilmi, sai kuma muce Uncle Ali da shima Koda yaushe yana tare dasu, shima yana taka muhimmiyar rawa a cikin zawiyar Mallam Babba.

Mahaifin Humaira na son ya ganshi da 'ya'ya amma Allah bai nufeshi ba, ganin girma nata zuwa mashi baida magaji yasa ya dangana da Allah, ya san shi ke badawa shi ke hanawa, sai dai duk da danganar da yayi da girma daya zo mashi hakan bai sa ya ha'kura da rok'on Allah ba, kullum cikin rok'on Allah yake akan ya bashi haihuwa.

Cikin hukuncin Allah kuwa, Allah maji rok'on bawa ya kalleshi ya amsa mashi addu'arshi.

Ba k'aramin farin ciki yayi ba, haka 'yan uwanshi da abokan arzk'i da duk wani makusancinshi ya tayashi murna.

Cikin hukuncin Allah kuwa mahaifiyarta Amina ta haifota yarinya kyakyakyawa ta k'arshe, sai dai da ka ganta ka san ba'ka ce amma kyakyakyawa.

Ba k'aramin gode ma Allah suka yi da baiwar daya basu ba ta samun 'Ya data ci sunan kakarta Aysha.

Tana da shekara d'aya da rabi Allah ya bama Ammi wani d'an daya ci sunan mahaifinshi Yusuf suna kiranshi da Aryan.

Rayuwa mai cike da jin dad'i suke, iyayensu na basu kulawa da tarbiya ta musamman.

Allah sarki rayuwa! Humaira nada shekara biyar Alhaji Mallam Yusuf ne ya tafi wa'azi babbar birnin tarayya Abuja, kan hanyarsu ta dawowa ya had'u da ajalinshi, wanda suka yi accident, ba wanda ya fita cikin motar shi da almajiranshi.

Ba k'aramin tashin hankali gidansu da cikin garin suka shiga ba na rasa babban Malami kamar Alhaji Mallam Yusuf.

Sunyi kukan rashinshi har sun dangana, nan kowa ke rige rigen kyautata ma 'ya'yanshi, dan sun San abinda zasu yi mashi kenan da zasu kyautata mashi, dan akwaishi da son 'yan uwanshi da zumunci, idan har yaji kwana biyu bai ji d'uriyar wani ba, da kanshi zai nemosu yaji ko lafiya, shiyasa rasashi ba k'aramin rashi bane a wurinsu.

Haka Ammi taci gaba da kula dasu, wanda tun rasuwar mijinta bata k'ara lafiya ba, yau ciwo gobe lafiya.

Mallam Babba da kanshi yasa aka kaishi wurinta, yayi mata nasiha na ta dangana, kowa data gani irin ranar yake zuwa kuma zata zo ranar, lokacinshi ne yayi, ba wanda zai zauna yayi gsdin duniya, shima daya tafi ba wai yayi gaggawa bane. Nasiha yayi mata sosai mai ratsa zuciya.

Sai dai ba yanda za ayi da hukuncin da Allah ya tsara. Ciwo ne yaci k'arfinta wanda yasa itama ta koma ga mahaliccinta.

Nan fa Humaira ta ri'ke makaran da mahaifiyarta take ciki tana kuka, dan dan bata manta ba, irin shigar da aka ma mahaifinta kenan aka fita dashi, wanda har yanzu bata k'ara sashi a idonta ba, gashi kuma yanzu za a k'ara fitar mata da Amminta, ita ba zata yarda ba.

Haka aka r'iketa suka d'aga gawar mahaifiyarta suka fita da ita, tana ihun ina zaku kai min Ammina? Kada ku tafi da ita.

Ranar ba wanda bai tausaya mata ba.

Haka rayuwarta ta koma gidan Mallam Babba da zama ita da Aryan, damuwar rashin Ammi ya ragu mata saboda samun kulan da take yi, kuma dama ta saba da zaman gidan. Shiyasa bata damu sosai ba.

Karatu take d'auka sosai na islamiyya dan akwaita da k'ok'ari both boko da islamiyya, duk abinda aka mata yanzu zata d'aukeshi a kanta.

Haka taja d'an uwanta a jikinta, bata da abokin fira kamarshi idan ka d'auke Hajja da Mallam Babba.

Haka zata zauna suna fira, duk da firan yawanci sai an tashi da fad'a, dan Allah yayi ma Humaira tonon fad'a. Bade ta zauna da mutum ba bata hayak'ashi ba duk girmanshi, shiyasa take cin duka cikin 'yanuwanta.

Ko cikin aji ne kaji wani abu ya faru da ita ne, sai dai bata da fushi, kowa nata ne, ita dai barta da tonon fad'a, wanda ko malamai bata k'yale ba, kullum cikin kawo k'ararta ake wurin Mallam Babba.

To shi kanshi bata k'yaleshi ba, haka take har girmanta wanda yanzu tana da shekara sha biyu.

Humaira doguwa ce bak'a mai matsaikaicin hanci da dara-daran idanu, dan idanunta shi ya k'ara mata kyau tunda bata da hanci. Duk da bak'inta bai sa sa tayi shafe-shafe ba kamar yanda matan yanzu suke, da bala'i sai sunyi fari.

Matsalar Humaira d'aya tana da rawar kai, gaba d'aya ta jawo 'yan matanci tun baizo mata ba, ba zaka ta'ba ganinta da 'kananan yara ba sai manya, sune tsararrakinta.

Abin na damun Mallam Babba, ya rasa yanda zaiyi da ita.

Zan sha tambayar ina k'udirina, a dalilin ciwon mahaifina na tsaya da typing na daina yi saboda hankalina ba kwance yake ba, da kuma ya rasu, idan ina typing yana yawan tuna min da ciwonshi, shiyasa labarin ya fita a raina, amma zanyi k'o'k'arin inga kun sameshi complete.

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now