page 2

1K 66 0
                                    

0⃣2⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*


Zaune suke cikin palour su bayan sun gama cin abinci rana Alhaji Habib da matar shi Hajiya Hafsat tareda yaran su Iman da Muslim suna, hira cike da nishadi da yake Habib in ya dawo daga kasuwa yana dan jimawa bai koma kasuwa ba, Iman ce tace da baban su "yawwa baba tinda babu islamiya yau a kaimu gidan Hajiya ni da Muslim in zaka komawa kasuwa in kun dawo sai ku biyo ku dauko mu"

Habib yace da iman "yi hakuri Iman ki bari a weekend sai muje tare tinda kinga maman ki bata zuwa aikin ranan sai in kai ku gaba daya in zani kasuwa"

Iman tace " toh baba Allah ya kaimu"
Daga nan suka cigaba da hiransu har zuwa lokacin da ya masu sallama ya tafiya wajen sana'ar shi ita kuma Hafsat tace da yaran suje suyi alwala lokacin sallah la'asar ya gabato.

__________________

"Inna na tafi gidan aiki sai na dawo" samira tace da innar ta lokacin da zata tafi gidan aikin ta

Inna suwaiba tace "toh diyar Albarka se kin dawo dan Allah ki hanzarta bani so kiyi dare"

Samira tace "insha Allah maman chérie"

Inna suwaiba tayi murmushi tace "Allah nuna mani kin koma school diyata zanyi kowa farincinki"

Wani tsalle da samira tayi se gata ta komo gaban innar ta, ta rungumeta tana me farin cikin da adu'ar da tayi mata daga nan kuma sai tayi gaba sai gidan aikin ta.

Tana shiga da sallama a bakinta ciki ciki Hafsat ta amsa mata sabida tinda taga Samira ta fara girma ta fara jin bata kaunar ganin ta a gidan ta dan babu yadda ta iya ne kasancewar innar ta ce ta roke ta akan ita bazata iya zuwa aiki ba sadaniyar rashin lfy da ta tafi yi likita ya hana ta aiki shiyasa ta bar zuwa aiki Samira ta cigaba da aiki a gidan. Maganar da samira tayi ne ya tsamo ta daga duniyar tunanin da ta fada

"Anty mai za'a dafawa"

Seda Hafsat ta ga dama sannan ta amsa mata da

"yau dambun shinkafa naso ki mamu sai dai baki zo da wuri ba kin je kin yi zaman ki dan rainin hankali, dan haka kiyi sauri ki dora mamu jalof in macaroni in kin aza ga salat can ki wanke mani shi"

Samira ta amsa da toh tana me yin gaba zuwa kitchen nan da nan ta gyara kayan miyar ta kasacewar komi akwai na aiki a gidan,
Bayan ta gama sauri sauri take wanke mata salat inta tana sauri tabar gidan kafin me gidan ya dawo tana can tana tunanin ta har hafsat ta fado kitchen in bata sani seda ta daka mata tsawa sannan ta ankara da ita

"wai ke wace kalar yarinya ce ana maki magana kinyi banza da mutane"

Samira tace da ita "dan Allah anty kiyi hakuri ban ji ki bane ba"

Hafsat tace " ina fa zaki jini kin zo kin sa mutane gaba dan banzan tunanin kawai, imbécile kawai" ( nace oh ni nana mi kuma yayi zafi hada su zagi😡)
"Kuma in kin gama wankewa kije na zuba maki abincin ki kiyi gaba"

Aikin bakon raggo , raggo bakon aikin nan da nan ta wanke ta aje mata a inda ya dace ta je ta dauki abincin ta tayi gaba abunta,

Nima bin ta nayi a baya sabida gudun tsaro ba dan tsoro ba se gidan inna suwaiba. Tana gaba ina bin ta a baya ha gidan su kasancewar basu da wani nisa tsakinin su daga gidan aikin na su tafiya 10 min ma tana kai mutum gidan.

Samira na shiga gidan da "Asalam Aleikum "

Inna suwaiba ta amsa da

"wa aleiki slm diyar Albarka , ina ta cewa mi ya tsaida ki har warhaka ana kan kiraye kirayen sallah magriba"

samira tace "wlh innata ban samu dama na gama da wuri ba nima inata sauri kar mai gidan ya dawo ya tarda ni cikin gidan shi"

Inna suwaiba tace "toh ki dai kiyi sauri ki dauki buta kiyi alwala ya fiye maki wannan surutun " tana me yin gaba zuwa toilet,

wacece Samira ?

amsa tana cikin page 0⃣3⃣

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora