page 6&7

793 49 3
                                    

0⃣6⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*



Ina kike sister ta , ta kaina, kawar arziki, my salima, na baki wannan
page kyawta kiyi yadda kike so da ita babu me hana ki,

merci beaucoup pour ton encouragement ma belle cherie, tu es une amie exemplaire, une soeur d'une autre mère❣❣❣❣ je t'aime beaucoup princesse muahhhh💋💋💋

Sakon gaisuwa gare ku
Maman Fahad
Hajiya Abou
Maman fati
Mamy blew💙
Zaynab Aleeyu
Oum Amatullah
Nafeesat Umar
Sweety Nafissa kema gaida ki ❣

Kunada yawa masoyana❤❤ na gaida ku a duk inda kuke 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Washe gari juma'a bayan Samira ta gama aikin ta na yamma masu gidan sukace mata gobe ba sai tazo aiki ba saboda gari zasu wuni tayi zaman ta , ta huta , taji dadi sosai kamar tayi tsalle dama tana son zuwa wajen yar tsohuwa kakar ta ,

bayan tazo gida take fada ma innar ta abinda akace ma ta a gidan , sosai innar ta , taji dadi itama ta dora da cewa

"kenan muma inshah Allah se muyi samako muje muga su malan ko, tinda kinga mun dan jima bamuje wajen su ziyara ba"

Samira tace " Hakane inna ta Allah ya kaimu lfy "

inna ta amsa da ameen daga nan Samira tayi toilet domin yin dahara saboda lokacin sallah yayi da yake ita inna har tayi alwala ita .

bayan sun gama sallah  ne Samira ta zubo masu abinci sukaci tareda innar ta daga nan suka taba hira kafin lokacin sallah isha'i yayi.

*bari mu leka gidan Alhaji Habib muje wace wainar ake toyawa*🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀

zaune na iske Habib da Hafsat saman kujera mai zaman mutun uku suna hira su cike da nishadi , da so da kauna( na so na sauraro maku mi suke cewa sai dai hira ce sukeyi kasa kasa🤪🤪) , su kuma su Iman hankalin yana a kan TV suna kallon tashar arewa 24,

Iman ce tace da Muslim "yaro gobe ne zamu gidan hajiya tinda babu makaranta"

Muslim "da gaske Iman"

Iman tace "wlh ko, kuma se munga Muhsina, da Ridawan (diyan yayan Habib ne waje guda suke da iyayen shi) muyi ta wasar mu ko"

Muslim se ya tafi wajen iyayen shi dan kara tambayar su, yana zuwa se yace da Habib

" baba way inji Iman gobe ne zamu gidan Hajiya"

Habib yace
"inshah Allah Muslim"

Hafsat tace " ohhh su Muslim anji yawo ko sai dadi akeji to ba'a zuwa da kai nida my iman kawai zamu tafya kai sai dai kabi baban ka kasuwa " tayi maganar cikin sigar wasa

Ay ko sai naga yaro ya fashe da kuka yana fadawa jikin baban shi

Habib yace "Haba mon amour minene na sanya yaro na kuka sai ma a fasa tafya duka gabadai in dai ba'aza da Muslim i na ba , i shiru mon adorable enfant ( my dear son) , da kai za'a tafyar kaje kaga amariar ka ko"

Se ko ga yaro yana murmushi😅😅😅 yana tsallo , yace
" kuma baba in hajiya ta bani kudi hana ma Iman zaniyi"

Iman tace nima ay in papi( da yake haka sukace ma kakannin su maza)  ya bani kudi na ban baka ( ashe kowa dai da wanda yake bashi)

Daga nan yaran suka cigaba da kallon su suma uwajen suka canza hira zuwa tasu ta masoya,

_________¥¥¥¥¥¥_______

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Onde histórias criam vida. Descubra agora