page 11to 14

2K 28 0
                                    

1⃣1⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

*Sakon gaisuwa gareku masoyana 😘😘😘*
*Maman Fahad*
*Dr Ummiey~Boko*
*Official marcy*
*Salima*
*Fati*

.Murmushi kawai Abdulahi yayi sannan yace

" kaga ni dai wuce muje ka aje gida in ka dawo sai ka biyo ka dauke ni "

Habib yace

"Ok muje "

Yana yin gaba zuwa cikin mota , shima Abdulahi zagayawa yayi , ya zauna a daya bangaran , sannan Habib ya ma motar key se gidan Abdulahi . Suna zuwa kofar gidan se Habib ya tsaya , Abdulahi ne ya kalle shi sannan yace

"wai kana nufin baza ka shiga ba ciki ku gaisa da kanwar ta ba, naga ka tsaya a nan"

Habib yace

"pardon ( sorry) abokina wlh ina so inje gida ne in dan huta barci nakeji sosai kuma kaga lokacin ya kusa"

Abdulahi yace

"ok to se an jima ka gaida mani uwar gida Hafsat"

Habib yace

"ok zataji "

Daga nan ya fito daga motar yayi cikin gida , shi kuma Habib ya tada motar se na shi gidan.

Tafe yake cikin motar shi yana tunatin moment in su shida Samira dazu, lokaci lokaci murmushi ke subuce mashi har ya kawo gida , yana zuwa yayi horn mai gadi ya bude mashi get ya cilla hancin motar shi cikin gidan, yana gama parking ya fito daga motar yayi cikin palour shi yana mai cewa

"Assalam Aleikum uwar gida sarautar mata"

Hafsat tana zaune saman kujera me zaman mutu biyu tana hutawar ta ita kadai tinda yanzu bata zuwa ko ina saboda har ta dauki hutu a school, kuma su Iman basu taso daga school ba saboda sai karfe biyu suka tashi a lokacin kuma duka karfe 1 ne

Hafsat najin sallamar shi yace uwar gida sarautar mata kuma gashi da wani murmushi a fuskar shi saida gaban ta ya fadi amma sai ta dake tana mai cewa

"wa aleika salam mijin Hafsat uwar gida kuma amaria a gidan Habib"

Yaso ya dan gwada ta kuma sai ya basar sabida condition in da take ciki baya son wani abu ya same ta , itace ta tsamo shi daga tunanin da ya fada tana mai cewa

" bonne arrivée mon coeur( welcome my heart)  lfy ka dawo warahaka "

Ya kalle ta da kyaw yace

" daga gari muke nida Abdulahi kuma nan wajen university ne , shiyasa nace bari inzo gida kawai "

Hafsat tace

" Ok mon coeur (my heart) to wa zaya dauko su Iman daga school kaga ka taho baka dauko su ba kuma kaga kuma har karfe 1 ta wuce"

Ya kalle ta da kulawa yana cewa

"Nayi ma tonton ( uncle) in su Abubakar magana da yaje ya dauko su in lokacin tashi yayi "

Hafsat tace

" ok mijina muje kayi wanka kazo kaci abinci, kaga kuma lokacin sallah yayi "

Yace da ita

"ok matata muje   "

yayi maganar yana yin bedroom itama Hafsat binshi tayi a baya , ni kuma na tsaya palour zaman jiran su😅😅😅 sabida tsaro badan tsoro ba🤣🤣

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang