♣ *DANGANTAKAR* *MU*♣
*NA*
*Fatima* *batula*( *Bhatoolerty*)
~SADAUKARWA~
Ya umar ɗalha
Aunty Beelat
Fatima MazaduWattpad @fatimaumarmoddibo
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN (08107707692)*
*bismillahi* *rahmani* *rahim*
page 1to2
Tsugun ne take ta duƙar da kanta, tana yin hawaye da alama bata saba yinsu ba.
Cikin muryar kuka tace ma matar da ke gabanta wanda kallo ɗaya zaka mata ka gane mahaifiyarta ce
"Dan Allah Inna ki bawa baba hakuri, ba fa ni kadai zanje ba, kuma Farida ni ce babbar 'kawarta ba zata ji daɗi ba in banje bikin ta ba, kuma kwana daya za'a yi, dan allah Inna ba abind zai faru in Allah ya yarda ..
Innar tai saurin katseta, tana kallan ta, tace"Khadija ni ban san yadda zanyi da ke ba, nayi mishi magana amma ya'ki amincewa, kuma ni kaina banga laifin shi ba, taya za'a barki zuwa kai amarya Gari har abuja, alhanin duk ƙauyen nan ba wanda ya taba zuwa abuja zai dai muji labarin, babban gari ce kuma garin sai ahankali, ko ita kan ta faridar kud'i iyayenta suka gani, dan basu san waye mutumin ba, balle iyayenshi, haba khadija taya kike ganin babanku zai yarda ki je e..
kuka ma 'karfi khadija ta fara yi
taba Inna tausayi da mamaki dan tunda khadija take shekaru goma sha bakwai a duniya bata taba yiwa abu kuka haka ba, duk yadda take son abu ta rasa shi bata kuka da shiga damuwa haka
"Ya isa haka, kiyi shiru zan mishi magana, kuma kema zan kira ki inya dawo ki ro'ke shi ,maza tashi ki je ki yi sallah ki ci abinci yaushe rabunki da cin abinci.
Duk da taji daɗi amma ta kasa cewa Inna komai tashi tayi ta wuce d'akin su.
Binta da kallo Inna tayi tana kara mamakin khadija.
Tana shiga d'akin ta tadda kanwarta Hasfa tana linkin kayan da suka wanke.
Hafsat najin shigowarta ta juyo, duk ta karancin shekarun hasfa zai da ta fahimce sauyin yanayin fuskar Khadija, ahankali tace
"Yaya Khadija kukan me kike yi?
Khadija tai saurin kauda kanta tana goge hawayen fuskarta tace
"Ba komai Hasfa ,je ki kicin ki ɗi bomin abinci
"To Yaya ta fita daga d'akin
*like*
*comment*
*shire*