26

164 13 2
                                    

💞 NOOR

26

Fitowa nayi na nufi sashen Yarima Fu'ad don shaida mishi abinda Yarima Kassim ya aikata, a hanya muka hadu shima ya fito. Gaidashi nayi nan yake cewa ai tun dazu yaso zuwa amma wasu ayyuka suka tsare shi, murmushi kawai nayi.
Cewa yayi mu karasa sashena kawai, bayan mun shigo nayi shiru bance komai ba hakan yasa yace "Nasan da magana a bakinki, fadi ina jinki"
Nan na kwashe komi na fada masa, mamaki ne ya bayyana a fuskarsa karara duk da nima nayi mamakin abinda Yarima Kassim din ya aikata.
"Kiyi hakuri, zanyi magana dashi" yayi maganar ransa a bace duk da tsantsar kishin da yake son boyewa hakan bai hana naji shi cikin muryar tasa ba.
Sallama na mishi na fito sabida jin an fara kiraye-kirayen sallah Isha, kuma nasan masallaci zai tafi.

Bayan sallah Isha ne, Yarima Ameen ya kawo ziyara don banyi tsammanin ganinshi a wannan lokacin ba. Gaidashi nayi ya amsa ba yabo ba fallasa, duk da fuskarsa a daure take hakan be hanani ganin kyawun da yayi ba, shagalta nayi wajen kallonsa, shi kam sai yayi bakam kamar bai masan inayi ba.
"Kallon ya isa haka" muryarsa ta katsemin tunanina.
Sunkuyar da kaina nayi cike da kunya don bansan na shagalta da kallonshi haka ba.
"Kisa a kawomin abinci" naji ya fada. Saurin dago kaina nayi sabida sanin da nayi mishi shi ba mutum ne mai tambayar abinci ba yafi auki gasu shayi da kayan marmari.
"To" na amsa tare da mikewa na fita. Kai tsaye madafa na shiga nan bayin dake gurin suke shaidamin ba abinci sai farfesun naman rago. Da kaina na dora shayi sannan nasa Tala ta samomin wasu tsirrai dake farkon Lambu.
"Ki samu dogarai biyu su raka ki" na fada lokacin da take kokarin fita.
"To ranki ya dade" ta amsa tare da ficewa.
Wata baiwa nasa ta kawomin danyar kaza, gyara kazar nayi na ajiye ta a gefe. Shinkafa da daura a wuta na dan sa gishiri kada. Tafashen kazar na daura amma nasa ruwa kuma da dan yawa nasa gishiri, kayan kamshi da sauran kayan dandano. Koda Tala ta kawo tsirrain, nan nasa ta yayyanka su da yawa, na bata albasa da danyar citta nace ta yanka su amma cittar kanana sosai nakeso.
Shinkafar ta kusa dahuwa sannan na sauke ta na tace, tukunyar kasa na dora a kan wuta, na zuba shinkafa kadan a kasa sannan na zuba kaza a kai da tsirran, albasa da cittar a kai, shinkafar na sake diba na rufe saman wannan sannan na juye ragowan kazan da sauran kayan na rufe da shinkafar. Ruwan tafashen na juye a kai na rufe tukunyar da murfinta yanda tururin bazai fita ba. Ina nan zaune har abincin yayi, na zuba shi a akushi mai kyau, na zuba farfesun naman ragon a wani akushin na daurasu a tire nasa Tala ta dauko, daya baiwar kuma ta dauko shayi da ruwa.
Shiga nayi cike da addu'a Allah Sa bai tafi ba, aiko a zaune na taddashi inda na barshi. Ajiye tiren sukayi a gabanshi suka fita, gabansa na karasa na fara zuba mishi abincin a faranti.
"Ya isa haka" ya fada.
Ajiyewa nayi sannan na tsiyaya mishi shayi a kofi. Matsawa nayi don bashi don bashi damar cin abincin.
Saukowa yayi daga kan kujeran ya zauna bisa kilisar dake shinfide gurin ya fara ci.
"Ke kika dafa amma"? Ya tambaya kai tsaye.
"Eh amma ya akai kasan ni na dafa?" Na tambaya.
"Girkinki da ban ne, kina amfani da tsirai masu kamshi" ya amsa yana kai cokali bakinshi.
Murmushi nayi kawai bance komai ba.
Ina nan zaune harya gama cin abincin yasha shayi sannan na fara tunanin yi mishi magana.
"Ranka ya dade" na fada a sanyaye.
"Na'am ranki ya dade" ya amsa cike da zolaya.
Murmushi nayi na fara wasa da yatsun hannuna.
"Kiyi magana, dare nayi indai ba so kike in kwana anan ba" ya fada yana kallona.
Saurin dago kaina nayi, muna hada ido ya sakarmin murmushi.Sake maida kaina kasa nayi sannan na tashi na dauko abin nan.
Tsugunnawa nayi a gabanshi na mikamai, hannu yasa ya karba yana kallona da alamar tambaya.
"Don Allah so nakeyi ka budemin" na fada a sanyaye.
"Kalli nan" yace min tare da nuno kasan abun, ruwa ya tsiyaya a hannunsa sannan ya diga a gurin, sai gashi ya bude kamar almara. Murmushi nayi amma cike da al'ajabin abinda ya faru yanzu, mikomin yayi sannan ya mike da niyyar tafiya.
"Na gode ranka ya dade" na fada ina kallonshi.
Murmushi kawai yayi baice komi ba ya fita.

Bayan fitarsa na zare takardar dake jikin abun, warware ta nayi, nan naga wani rubutu amma da wani yare sabida na karanta yafi a kirga amma na kasa fahimtar komai kalma daya ce kawai nake da tabbacin daidai na karanta wato "Zahra". Ajiyewa nayi da zummar gobe da safe zan tambaya Yarima Ameen ko ya sani.
Kwanciya nayi cike da tunani kala-kala, ahaka har bacci ya daukeni.

#Vote
#Follow
#Comment

💞NOORWhere stories live. Discover now