Daya gama shiryawa ma bai ce masa komai ba ya dauki wayar shi, yasa a aljihu ya fita daga dakin sabida kiraye kirayen sallan magrib da akeyi, dai dai da zai shiga masallacin ne ya sake juyowa yaga koh Abdallah ya biyo shi amma ba shi ba alamun sa, wayar shi ya ciro daga aljihu yayi dialing numbern shi kamar ba za'a dauka ba.
"Ka koma Christian ne ban saniba? Ba tare da ya tsaya jin amsar shi ba kashe wayarshi, ya maida aljihu tare da ida shigewa masallacin, har za'a tada sallah sai gashi ya shigo, sukayi sallar sannan suka jira akayi isha, suka fita tare.
"Wai kai meke damunka ne ka zama wani iri" khalifah ya tambaye shi a lokacin da suka nufi cikin gidan, ajiyar zuciya yayi
"Idan nace maka ga abun dake damuna na maka karya, kawai ina tsintar kaina a wani yanayi ne wanda banyi zaton shi a nan kusa ba"ya ba shi amsa tare da jawo daya daga cikin kujerun dining din ya zauna, har khalifah zai bashi amsa sai ga mommy tazo sai kawai yayi shuru
"Shine baku fara cin abincin ba?khalifah ya zaka bar mun da'a na da yunwa ne" tace tana hararan shi dariya yayi
"Toh mommy shi dan naki bashi da hannu ne? Koh na mai Kama da baby sitters ne tunda na lura jinjiri kika maida shi"
"eh din baby na ne meye ruwan ka ja'iri kawai "gwalo Abdallah ya mai tare da cewa "kyale shi mommy kishi yakeyi kinfi ji dani"dariya ce sosai ta kama khalifah
"Sai na rasa wa zanyi kishi dashi sai jibgagen kato dakai da kuwa nayi asara" gwalo yaci gaba da mai daga na mommy tace "ya isa haka kowa ya kawo plate dinsa na sa masa abinci"mika mata sukayi kuwa ta saka wa kowa ita ma ta saka ma kanta aka nastu kowa ya fara ci. Sallama akayi a kofar parlorn sai da suka amsa tukuna aka shigo daddyn khalifah ne da kuma salim a bayan shi.
Ai kuwa salim na hada ido da Abdallah ya zo da a guje ya janyo kujera ya zauna a kusa dashi yana cewa "dama nemanka nakeyi yaya na yita kiran numbern ka baya zuwa"tsawa mommy ta buga mai tace "wannan wane irin rainin hankali ne mutun yana cin abinci koh gaidashi bakayi ba zaka cika shi da surutu" hade rai yayi tare da gyara zaman shi a kujerar.
"Sannu da dawowa daddy" su khalifah suka gaidashi "yawa sannu, me ake ci haka ne ba tare da an jira mu mun dawo ba, yanzu da wane zamuji da fadan da aka mana daga shigowa koh kuwa da jiran mu da ba'a yiba? daddy ya fada cike da zolaya.
"Duk wanda kuka zaba" mommy ta bashi amsa daga nan dai suka gaisa yace zai je yayi wanka tukuna kowa yaci abinci iya ci wanda ma bai ishe sa ba ya kara, akayi dariya ya wuce ciki mintuna kadan mommy tabi bayan shi. Abdallah ya dubi salim yace
"Bro wai fushi kayi ne akan abin da mommy tace? naga ai bai kai ayi fushi ba, get your mind off it please ka fada mun me yasa kake nemana" juyowa yayi da kujerar shi suna fuskantar juna yace
"ai duk wanda yayi fushi da mommy akan ka toh kuwa ina tausaya mai ne sabida bakin ciki kashe shi kawai zaiyi.dariya ya basu gaba daya ya sake cewa
"Dama na yiwa yaya khalifah maganar iPhone 11 ne data fito amma yace wai baya da kudi, shine nace kai zan tambaye ka.ya fada yana sosa kanshi, imani ne ya kama khalifah kafin Abdallah ya amsa shi yace
"Amma dai salim baka da mutunci na dauka wata magana mai muhinmanci ce zaka fada baka da hankali wlh, ya dubi Abdallah "wlh kar ma kace zaka siya mai idan ba haka ba a kunnen daddy dan ba abun da zai hanani gaya mai"bakin ciki kamar zai kashe salim Allah kadai ya san sau nawa ya zage shi a ranshi, Abdallah ya dubi khalifah yace
"Sannu sarkin sa ido na rasa wanne kafi kwarewa a akai sa ido koh bakin ciki" tsaki khalifah yayi hadi da tashi tsaye yace "kan ku akeji kun dai ji abun da na fada idan kunne yaji jiki ya tsira" yayi gaba abun shi,bayan ya wuce ne Salim yace
"Ni Yaya ka barshi kawai idan ba haka ba wlh zai yi abun da yace Kuma bana so daddy yaji cewa Kai na tursasawa ka siya mun waya"Shima Abdallah wayar shi da car keys din shi ya dauka yace
"Karka wani tada hankalin ka,ka same ni office gobe zamuyi maganar zan wuce gida dare yayi kafin mamu ta kirani" jijiga kanshi yayi yace "ok toh ya sai da safe ka gaida kowa da kowa harda small daddy sai nazo" hannu kawai ya daga mai da yake har yanzu su mommy basu fito ba da ya mata sai da safe sai kawai ya fita harabar gidan a zauna kan kujera ya tadda khalifah yana waya sai murmushi yake zubawa,bai ma san yazo gurin ba gyaran yayi ai kuwa da sauri khalifah yayi sallama da wace suke waya ya juyo
"Bro ka fito kenan ai na dauka a nan zaka kwana"dariya ce taso kama Abdallah amma sai ya fuske yace "eh na fito tun lokacin da kake ce mata I love you" zaro ido yayi yace"Kai bana son sharri me ma ya kawo ka nan da har yasa kaji abun da nace,Kai idan ma na fadi hakan meye ruwanka a ciki" murmushi yayi ya nufi motar shi yace"Ni dai nayi gida ka kirata kawai ku ci gaba daga inda kukah tsaya good night"
"Da dai yafi maka Allah ya tashi mu lafiya zamu karkare maganar mu ta dazu a office gobe"hannu Abdallah ya daga mai yayi wa mai gadi horn ya bude mai gate ya fita,gida shida ne a tsakanin gidajen su so a cikin mintuna 15 ya isa gida.
***********
Jiddah ce take tafiya da sauri sabida exam dinsu 8 ce amma gashi 8:30 tayi,fuhutu sai kiranta take tayi wai an kusa a fara jarabawar gaba daya kanta ya dauki charge ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a aji,da kyar ta isa ajin ta karbi answer sheets da question paper ta tafi kusa da fuhutu ta zauna.Murmushi kawai suka yiwa juna daga nan kowa ya fara rubutun shi,bayan hour daya suka fito daga gurin exams din fuhutu ta dubi jiddah tace "wlh kin kuru da kin rasa exams dinnan da kin yi bayani"dariya tayi tace
"ai na san ba zaki bari nayi missing dinta ba,wlh banyi saurin bacci bane Koda na tashi lokaci ya wuce Kuma ba Wanda ya tadani wai sun dauka banida exams"shuru kawai tayi tana duba wani karamin littafi dake hannunta jiddah sake cewa
" Muje cafeteria muci abinci mana,yunwa nakeji sosai duk rubutu ya kwashe mun wanda naci a gida kuma idan muka gama zaki rakani gidan wani guri" tashi tsaye fuhutu tayi tare da daukan Jakarta sai da sukayi nisa a cikin tafiya tukuna ta turo baki tace
"Ni ba inda zani baki ji yanda nake jin bacci bane shi yasa" jiddah ta kalleta da fuskar tausayi tace"haba mana khairin Abba dan Allah ki raka ni kinji"ta sake girgiza ganta alamun ba zataba gardama ce sukeyi har suka isa.
________________________________
Follow
Comment
Vote
And share
Thanks 🙏Marmiee_suleiman🌕
YOU ARE READING
Fuhutulkhairi
Short Story"Jiddah kin san Allah tafiya zanyi na barki a nan gurin"a yanda tayi maganar zaka fahimci cewa akwai gajiya a jikinta "Ki bari nazo mana report din mu fah nake submitting kin san cewa idan ba muyi ba wlh zai iya bamu carry over ba imani ne dashi ba"...