page 22

438 28 0
                                    

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟

2⃣2⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*


_*wannan page taku ce yan kainuwa writters association, nagode sosai yadda kuka tarbe ni hannu biyu biyu cikin kungiyar ku, Allah ya saka da Alkairi, Allah yasa mu anfana da juna, na kara gaida ku kyawta 👌🏻*_

Sannu da zuwa tayi mashi sannan tace da shi
"mon coeur(mu heart) wannan fah"

Tayi maganar tana nuna akwatin da ke aje , saida ya sauke ajiyar zuciyar sannan yace da ita

"mon amour (my love ) zauna muyi magana"

Babu musu ta zauna amma fah already cikin ta har ya murda , ta riga da ta raya a ran ta Habib in ta aure zai kara.

Tana zama Habib ya jawo jikin shi ya fara mata da nasiha sannan da kalamai masu dadi sannan ne ya fada mata zai kara aure, ai batasan sanda ta kwace jikin ta daga nashi ta tashi tana cewa
"mi kake nufi  Habib ( hhhhh yaw babu my heart) , kishiya fah kace, ni zaka yiwa kishiya, duk abinda nake maka amma ka rasa da mi zaka saka mani saida kishiya , lalle Habib amma ko wacece tayi nasarar shiga tsakani da kai sai tayi nadama"
ta gudu ta wuce fuuuu sai dakin ta,
tana zuwa ta dauki gyelen ta da wayar ta ko yaran ta bata tsata dauka ba ,ta fito da sauri tana shirin barin palour yayi azamar kamo ta , ya rungumme ta sosai a jikin shi , yana jin yadda zuciyar ta, take bugawa da sauri sauri saida ta fara sauke ajiyar zuciya ya fara mata kalamai masu dadi yana kara jaddada mata da har gobe tana cikin zuciyar ki kamar da. Ya kara da cewa
" wlh my love har gobe ina sonki, banida niyar wulankanta ki, dan zan kara aure ba ina nufin na bar son ki ba ne , ina sonki har gobe, ina son mu kasance tareda har karshen rayuwar mu tare, kuma dake da wadda zata zuwa duka kowa da matsayin shi a rai na , ki bar tada hankali kinji, nayi imani sai tayi maki biyaya , dan ma bakisan ko wacece ba, dan Allah kiyi hakuri muje kiga kayan da na sayo maki , duk abinda bai maki ba sai a sauya maki , kinji uwar gida na sarautar mata"

Taso ta kwace amma da yake ba rikon wasa ne ba yayi mata shiyasa bata samu nasarar kwacewa ba har ya jata suka koma dakin shi , sannna ya tafi dakin ta ya dauko twins ya aje su, ya koma ya rufe kofar palour , sannan ya zaunar da ita saman gado saboda tana nan a tsaye kamar gunki , yaje ya dauke mata ruwa ya bata , kin sha tayi saida yayi lallashi sannan ta sha ya fara bude mata kayan , kayan sunada kyaw amma tsabar kishin Hafsat gani take babu abinda yayi mata cikin kayan saboda ita hankalin ta ya can wani waje, tana yita tunanin yadda zata suburbudi amaria Habib(lalle akwai ta), koda Habib yaga hankalin ta baya wajen shi kawai shima sai ya haye saman gadon , yana yita ban baki da ban hakuri ganin bama ta jin shi kawai sai ya fara yi mata abinda tafi so (ni kuma sai na koma palour kar inga abinda yafi karfi na)

Aiko sune banga fitowar su ba saida safe fuskar Hafsat tayi jajir alamar taci kuka shi kuma bawan Allah har ya rame ga rigima ga babu abunda yaci jiya da dare, rigimar Hafstat ta hana shi yaci wani abu , shi dai Allah yasa ta hakura in kamar yadda tace mashi.
kuma yanzu hakanan ma ya fita bai ci komi ba , kuma a lokacin ha 11 na safe tayi dayake makara tashi sukayi kasancewar basu kwanta da wuri jiya ba , jiya ana ta zabga rigima da kyar ya shawo kanta tayi shiru sai 2 na dare suka kwanta shiyasa suka tashi a makare .

yana fita daga gidan ya sauke ajiya zuciya  yana cewa tin yanzu tana bala'i ina ga taji wacece amaria (akwai bala'i kenan ), bai zama ko ina ba sai gidan su , yana zuwa bayan sun gaisa da hajiyar su ne take fada mashi ai su kawun shi sun tafi can garin su Samira tinda safe suka tafi kuma yaw zasu dawowa ma sabida daga sun kai kudi ba zasu kwana ba , tareda ma su innar samira da tsoho malan aka tafi saboda inna tayi masu jagora kasancewar basu san garin ba. Fatan Alkairi yayi masu da samun nasara ,
sannan yake fada mata dan Allah ta taya shi bawa Hafsat hakuri , ya kara da cewa
"Hajiyata fah kunga tana jin maganar ku , in kun mata magana ta kara kwantar da hankalin ta "

Hajiya tace
" babu ruwana tsakanin ka ne da matar ka, "
Da kyar ya samu tace zataje da dare , yayi ta mata godia sukayi sallama.

Yana fita daga gidan ya kira Samira , bayan sun gaisa yake cemata
"my baby"
tace " na'am"

yace
" wai ina inna ta bada ajiyar ki , naji ance sunyi tafya kuma an bar mani baby ita kadai"

Tayi murmushi tace
"ina gida ni kadai , yaw ko islamiya banje ba , gidan babu dadi inna bata nan"

yace da ita
" keda ma kin kusa tafyar ki gidan ki kibar inna ita kadai , aiko tinda gidan ba dadi bari in zo in taya ki zama "

Da sauri tace
"a a yi zaman ka wlh da dadi "
, murmushi kawai yayi saboda dama wasa yake mata. Daga nan ya cigaba da jan ta da hira saboda so yake ta shaku da shi sosai kafin auren , shi in ma badan zaya gini ba ai da sai yace a sanya wata 1 (sai kace shine uban amaria ) amma yanzu yasan sai an kai bayan sallah karama nan da wata 3 dawani abu kenan

______¥_¥_¥_¥_¥_¥______

A bangaren Hafsat kuwa Habib yana fita daga gidan ta dauki yaran ta , ta basu nono suka sha sannan tayi masu wanka ta sanya masu kaya daga nan ta zauna tana ta tunanin duniya , lalle Habib wai tace zai yiwa kishiya duk abinda take yi mashi amma dan tsabar jaraba shine zai kara aure aiki wlh duk ko wace yarinya wannan sai ta shayar da ita mamaki amma ba komi , bari ta kira mama ta fada mata , tana kira bugu uku aka dauka , aiko tanajin muryar momyn ta sai ta rushe da kuka , subhanallah mama ta kawai take cewa , tana fama tambayar ta lfy, saida tayi mai isatar sannan tayi shiru take zayyane ma mama ta aure Habib zai kara ,
Dogon tsuka mama ta , taja sannan tace da ita

"wlh Hafsat in kina wani abu sai inga kamar yarinya y'ar shekara 16 , ke dan za'a maki kishiya shine kike ta yiwa mutane kuka , har kina cewa sai kin ba yarinyar mutane kashi, ko kuma dan kinga ni ba'a mani kishiya ba sai ke akace ba za'amaki ba , tin wuri ma ki dawo cikin hankalin ki sabida daga ranar da kika kuskura ki sanya hannu kika bigi kishiyar ki , ko a gaban idon mijin ko bayan idon  mijin ki to girman ki zai fadi a idon shi , abinda ya kamata kiyi yanzu shine ki kara mashi biyaya da girmamawa ,kuma ki cigaba da yi mashi duk abinda kika san zai sanya shi farinciki , ko kuma ma ki linka ga yadda kike mashi, "
daga nan mamar ta tayi ta bata shawarwari yadda zata kula da mijin ta sosai, ta kara da cewa

"to in dai kin rike wannan abubuwa da na lissafa maki inshah Allah babu abinda zai hada ki fada da mijin ki, kuma ki nuna mashi kina son auren , kina son abinda yake so , kuma kema kina taya shi son abinda yake so, nasan akwai zafi sosai balle duk da ba'a mani ta ba, amma kiyi kishi mai anfani ba na hauka ba , kin dai ji abinda na fada maki ko ? "

Tana share hawayen fuskar ta tace
"tace shikenan mama merci beaucoup (thank you very much) , "
Mama tace da ita ina su Iman tace da ita
"tin jiya ya kai su gidan su dan yasan bayada gaskiya,daga can ma suka tafi school yaw "

Murmushi mama ta tayi sannan tace
" ai yanada gaskiya kinsan halin yara yadda suke ba wayo garesu suna iya gani kuna rigima su tafi su fada ma wani , amma Habib ai ya kyawta da ya kai su can , kice ma suyi zaman su can har ki wuce ko" ta kara da murmushi a fuskar ta ,
Ita kuma Hafsat cewa tayi
"mama kenan hada ke ake hada baki wai har in wuce , shikenan ma sai an jima ku"
Mama ta tace
"wace ni 😳?  yarinya kin dai jin avinda na fada maki , kuma kiyi aiki da shi"
Daga nan ta kara jaddada mata yadda zata kara kula da mijin na ta


~🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀ na tafi kauyen su samira sai na dawo kuma🚲🚲🚲🚲~

Bayan sun kai cikin garin kafin su ida isa kauyen su Samira suka aje mota suka bar mai tukin motar ciki sannan suka taka da kafa sai gidan su kawu,

Abinda ya bani mamaki nasan dai kawun su Habib masu kudi ne , sunada hali,  kuma sai naga basu yi shigar masu kudi ba , kuma wai da akwati guda , kuma sai naga ba cikin wanda aka aje gidan Hajiya bane, to mike faruwa ne ? 

bansan mike faruwa bane ba ?  Ko dai sun bar sauran akwatin ne cikin mota ?
ko kuma wani auren ne aka zo nema ba na Samira ba ?


_*kuyi hakuri da wanan yaw ma gari naje wlh se mun hadu da dare inshah Allah*_

*GOOD AFTER NOON FANS*
*BON APRES MIDI FANS*

*je vous aime tous*
*love you all my fans*❣❣❣

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Where stories live. Discover now