Ita ta fara isa dining area din,inda ta dauko su plates,spoons da ruwa tare da hado wa da smoothie din data hadawa dadyn ta,ta kara shirya komai yadda ya dace gwanin ban sha awa,sannan ta dawo in da ta barsu tare da fadin
"Table is ready bismillah"
Tsam!suka mike suka biyo bayan ta zuwa teburin cin abincin,sai da ta jajja musu kujerun sannan kowannen su ya zauna,kafin ta soma serving din su,waina ce da miyar taushe da ya ji alayyahu da gyada tayi sai ta hada da farfesun 'yan ciki,dukkanin su da adua a bakunan su suka soma cin abincin.
Dady ko yaji dadin abincin sosai musamman ma smoothie din domin shi ma abocin san sa ne sosai,har yake cewa
"Gaskiya mamana kin yi kokari sosai wannan irin abinci haka"
Tare da gyada kansa alamar gamsuwa.
Momy ce suka hada ido da maryam,ta yi mata alamar kan cewa dadyn ta fa santi yake yi,aiko budan bakin ta sai ta ce
"Momy ko zamu sa wa dady waigi ne don naga alamun kamar santi yake yi"?
Ta karashe maganan tana gimtsa dariyar da yake son taho mata,momy ma ta karbe ta re da fadin
"Ai kam barin sa masa tun wuri"
Dariya abin ya bai wa dady ganin sun hade masa kai ya ce
"Haka ne koh mama na har da ke,toh na ma fasa baki tsarabar da na taho miki da shi"
Jin haka ne ya sa ta shi ga bawa dadyn hakuri akan ita dai babu ruwan ta momy ce.
Da haka suka karasa cin abincin cikin raha da annushuwa tare da kwanciyar hankali,sannan suka kammala.Maryam ce ta shiga tattara wurin,kafin suka dunguma zuwa falo.
Bayan zaman su ne dady ya kara gyara zaman sa ,sannan ya fuskanci in da maryam din ke zaune,ganin hakan ne ya sa ita da momy maido hankulan su zuwa gare shi domin dai sun san wata muhimmiyar magana zai yi,kafin ya fara magana da cewa
"Wai mama na ya maganar makarantar ki ne?wan da mai girma gwamna ya baki scholarship akan ki zabi kasa daya da cikin kasashe 3 da ya baki zabi don gudanar da karatun ki,kin yi tunanin kuwa,kuma wanene kika zaba a ciki?
Jim!ta yi,kafin a hankali ta dago da kan ta,idanuwanta suka sauka akan na dady wanda ya tsayar da ta sa idanun a kanta don jin amsar da zata fada,bude baki tayi,sannan ta ce
"Eh dady na zaba,daman ya bani zabi ne cikin England, Ukraine ko South Africa,amma kafin na zaban sai da nayi research sosai ta kafar yanar gizo(internet) dangane da kasashen da kuma makarantun da ke wuraren,sannan a karshe nayi making conclusion (na tsayar da hankalina) kan ingila(England),saboda akwai makarantu masu kyau a kasar,in da hankalina ya karkata zuwa ga wata makaranta domin ya burge ni sosai sunan sa BRUNEL UNIVERSITY,sannan suna yin kwas din da nake son karatawa wato medicine amma ta fannin mata wato gynecology,domin dady ina da sha awar ganin na taimakawa mata yan uwa na musamman ma gajiyayyu da basu da shi,sabida mata na cikin wani hali a kasar nan musamman na kauyuka,sannan ilimin mace babbar ginshiki ne ga alumma,don mace in tayi ilimi tayi wa duniya ne baki daya..
Ta dan nunfasa kafin ta cigaba
"Shiya sa nake son karanta course din din taimakawa iyaye na,yan uwana da sauran alummar kasata,suma su amfana da karatun da nayi,sai dai dady in kuna ganin abinda na zaban bai yi ba,kuna iya canza min zuwa wanda kuke so"
Ta karasa maganar cikin sanyin muryar ta tare da sunkuyar da kan ta,tare yin adua akan Allah ya sa hujjojin da ta kawo su sa iyayen nan ta su yarje wa zabin ta,domin tana ji a jikin ta ba lallai bane dadyn ya amince ta tafi wata uwa duniya tayi karatu ,in don ta momyn ta ne ,ta san a'a zata ce..
YOU ARE READING
K'ADDARA TA
RomanceBanko kofar dakin ta yi a fusace,dole yau ayi wacce za a yi a kare tsaknin ta da shi,hakimce a zaune ta same shi ya bama kofa baya daga shi sai boxers,ba riga sai karfaffn jikin sa d ke a murde,macbook pro na a gaba shi abnda ta hango a ciki screen...