Bayan dawowarsa ne mahaifiyarsa ta bukaci yayi aure, inda yace shi yar mai aikin gidansu yakeso wato khadija.
Kadija yar mama ladi asalinsu buzaye ne, gudun hijira sukayi har Allah yasa mama ladi tafara aiki a gdansu. Sunada kyau sosai ga gashi baa magana uwa uba kuma tsafta da iya girki.Mahaifiyarsa bata musaba ta amince da bukatarsa aka musu aure, mama ladi kuma ta tashi daga yar aiki ta koma yar gida itama don an waremata part dinta daban.
Bayan auren abdulrazak da Khadijah
Alhmdllh lokaci yaja dukiya sun zauna ma ya yan hajiya Aisha sosai, tukur junior wato ameer baya gajiya duka karshen wata saiyazo gida duba mahaifiyarsa da kuma kanin nasa.
Rayuwa tayi dadi har Allah yasa abdulrazak shida matarsa suka haifi dansu wato suhaib
Yasha gata sosai dan kowa ah gidan yana matukar kaunarsa. Anan garin abuja yayi makarantarsa tundaga nursery har yagama secondary school dinsa, mahaifinsa yace yazaba country dayakeso yakarasa, yace turkey yakeso.
Aka masa komai da komai yaje turkey yana karanta medicine, dan burinshi bai wuce na zama likita ba.
Yana maida hankali sosai wajan ganin ya cimma burinshi na zama babban likita ah fanin yara, kuma yana kokarin zuwa hutu sosai wajan iyayen nasa.Wannan shi ne takaitaccen labarin suhaib
....Cigaban labari...
Yana isa gida yafada toilet yayi wanka,
Ya fito daure da towel a kugunsa da kuma karami yana goge kansa.
Jikin mirror yaje ya shafa mansa body cream na MIDNIGHT.
Bashida man dayawuce midnight dan yanajin dadin amfani da kamfanin midnight, dan komai da komai na midnight yake siya kama daga shower gel har hair cream dinsu.Yana gama shafawa ya feshe jikinshi da dadadan turarunka..
Yaje jikin wardrobe dinsa ya ciro wasu English wears black trouser da black t-shirt yasa, wanda suka karawa farar fatarsa kyau.Yasa shades dinsa bakake na kamfanin Cartier panthere, ya dauki makolin motarsa yafita...........
"Suhaima's POV"
Kwance ta ke kan lafiyayyan gadonta tana bacci cikin nitsuwa...
Suhaima fara ce, kyakkyawa ajin farko
fuskarta dauke yake da sexy eyes masu kyau, dogon hanci kaman biro, da karamin pink lips, tanada dimples wanda ko kuka takeyi lutsawa sukeyi..
Shekarunta bazasu wuce 17..
Gatada shape kaman meh shekara ashirin da dori, kirjinta cike yake da dukiyar fulani, sanna tanada hips sosai wanda akafi kiranshi da figure eight.Mahaifiyarta ce tashigo dakin tareda sallama
Murmushi tayi da taga suhaima na bacci cikin kwanciyan hankali...
"Ohh ni samira suhaima akwai son bacci"
Zama tayi bakin gadon tafara tashinta ah hankali.... har ta bude idanontaGood morning ammi" shi ne abunda suhaima tafada tana bude idonta
'Morning my daughter'
'How was ur nyt'
'Splendid mum'
Inacan ina jiranki a dining muyi breakfast ashema baki tashiba..
Wallahi ammi jiya bansamu nayi bacci da wuri bane shiyasa..
Toh mamana meh kuma ya hanaki bacci da wuri...kallo koh? Hmm?
Ammi..mmm..dama...
Ammine ta katseta tareda cewa
Dama me suhaima..kinaso muyi fada dake koh banason kina kallon daren nan bakyaji
Dan kawai kun samu hutu kuma shknan bazaayi karatu ba sai kallo haba suhaima ko yar tilawan nan na al-qurani ba saikiyiba amma kallo kuma mamana ihmmmm
..ammina kiyi hakuri bazan sakeba I promise suhaima tafada tareda kama kunenta tana kallon mahaifiyarta data bata rai...
Toh shknan tashi kiyi brush ki sauko muyi breakfast dan abbanki yajima da fita wajan aiki...
toh ammi......
Tafada tareda mekewa tashiga toilet dinta donyin brush din..........
Vote, comment and follow....