Haduwar jini 4

18 2 0
                                    

Ta fito daure da towel a jikinta alamun tayi wanka, tayi brush din. Gaban madubi taja gujera ta zauna tafara feshe jikinta da dadadan turarunkanta tashafa mai sannan ta miqe ta nufi wardrobe dinta dansa kaya. Royal blue din abaya ta ciro wanda aka watsa masa silver stones ta ko ina, yayi matukar  amsar jikinta yamata kyau sosai ta dauki veil dinsa tayi rolling tafita zuwa dining don yin breakfast.

Bayan kwana biyu.
   Yana kwance a daya daga cikin gujerun wajan pool din, wata kyakkyawar yarinya tafito daga cikin ruwan ta nufi inda yake.
Wajan kunnensa taje tafara magana a hankali cikin rada tana cewa
"You May hold my hand for a while, but you hold my heart forever...... 
"I Love you hayateey..........I love you....
  Firgigit yayi yatashi yana zufa yana ajiyan zuciya, "subhanallah yauma banga fuskantaba"
Shi ne abunda suhaib ya furta yana tashi.
Yau kimanin shekara goma kenan suhaib kullum sai yayi mafarkin wata kyakkyawar yarinya, wanda yamata laqani da "my dream girl" Amma bai taba ganin fuskantaba saida muryanta ah mafarki.

"Ya Allah kabani ikon gani fuskan wannan yarinya, kimanin shekara goma kenan sonta na azabtar dani amma bantaba ganintaba"

Tashi yayi ya shiga toilet yayi alwala, yafito ya zura farar jallabiyarsa yayi nafilfilu, yayita roqon Allah tun karfe ukun dare har asuba yafita yaje masallaci, baidawoba har saida gari ya danyi haske ya dawo ya kwanta, da tunanin dream girl dinsa bacci barawo ya saceshi.

Bai tashiba sai karfe tara na safe, ya shiga toilet dinsa yayi wanka, ya fito daure da towel a kugunsa daya kuma yana goge kansa.
Yaje jikin mirror dinsa yagama abunda zaiyi,
Ya shirya cikin wasu fararen yadi masu matukar kyau sunsha aikin hanu da baqin zare, baqar hula da takalmi yasa, sanna ya dauki shades dinsa na Cartier yasa, yaja trolley din kayansa, ya dauki makollin mota yafita.
Dan yariga yayi booking flight din komawa Nigeria, jirgin zai tashi karfe 11:00pm.
Karfe 10:40 ya isa sabiha gokcen international airport. Ya kira wani wanda yasaba bashi ajiyar motarshi in zai koma gida har sai yadawo.
    "Merhaba (hello) omer"
"Mergaba efendim (hi sir)"
"Havaalanindayim ve ucak yakinda havalanacak (am at the airport and the plane will take off soon)"
    "Tamam efendim, ben bes dakika sonra olacagim (okay sir,I will be there In five minutes)"
"Tamam tesekkur ederim omer (okay, thank you omer).
Bayan mintunan da basufi biyar ba saiga wanda aka kirada omer yazo ya karba makullin motan ya mishi Allah ha kiyaye hanya ya tafi.
  Karfe 11 dadai jirginsu ya daga daga turkey zuwa Nigeria lagos.

Bayan awa shida da minti sha uku jirginsu ya sauka ah murtala muhammad international airport lagos.
Yana sauka kuma dama already ya riga yayi booking flight daga lagos zuwa abuja karfe 5:30pm jigin zai tashi.
Ba bata lokaci yana sauka jirgin yashiga wanda zai kaishi abuja.

Abuja.
Girke girke hajiya khadija ta ketayi dumin tarban danta, abinci kala kala ta girka itada mai aikinta naima, da kanta ta shiga part din suhaib ta gyara mishi ko ina tasa turaren wuta tareda kulle masa.
Bayan kaman minti talatin suka kammala komai, hajiya ta haura sama tayi wanka takira alhj domin sannaddashi cewa ta shirya, dan zasuje airport daukoshi.
Cikin wani tsadadden leshi sky blue dake da adon gold ajiki tasaka, ta saka babban gold veil da dan flat shoe dinta mai kyau, don hajiya ba ma abuciyar son takalmi mai tsayi bane.
Tana saukowa daga stairs din saiga alhj ya shigon falon.
"Hajiya kiyi sauri don inaga jirgin nasu kaman ya sauka fa"
"Gani nan ai nafito alhj"
"Toh ku dinne mata kinfiso kusa mutum yata jira"
Murmushi tayi tace "am sorry darling" tareda kama kunnenta
Murmushin shima yayi yace "ai hajiya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida"
Dariya sukayi dukkansu tareda ficewa zuwa mota.
Parking space din gidan suka nufa suka shiga motarsa Mercedes Benz s-class, maigadi ya bude gate suka wuce zuwa airport dauko dan lelensu.

Love Where stories live. Discover now