🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*GIDAN MIJINA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
(kalubale gareku iyayen miji)☀FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀
F.C.W.A☀home of qualities and trusted of the nation
*Mummyn seeyama*
*The first class writers of* *the 2019*The author of
*kuncin rayuwa*
*zaman takewa and now* *GIDAN MIJINA*i dedicated this page to my sis maman ameera ina jin dadin comment naki sosai allah yabar xumunci😘😘😘😘😘😍😍😍😍😍😍😍😍😍
*page* *~3&4~*
*WACECE FARHAT*
Malam musa saeed shine cikakken sunan mahaifinta malam musa dan asalin garin gombe ne yqna xaune a unguwar pantami malam musa talaka ne futuk dai dai akwai wadatar xuci
Yana da mata daya aisha yaransu biyu a duniya aliyu sai kuma hafsat wadda suke kiranta da FARHAT
FARHAT yarinyace kyakykyawa mai tarbiyya ga riko da addini a halin yqnxu farhat nada shekara ashirin da biyu yarinyqce yar dogowa siririya dai dai akwaita da dara daran idanu masu daukar hankali da karamin bakinta ga hanci ga kuma na shanunta kamar xasu fashe dan girma 🙈🙈
Ga maxaune tsola tsola kai komai na farhat yayi fa ba karya sai dai qce masha allah yanxu haka ta haddace alqur.ani akanta
Malam musa yana sana.ar kayan gwari ne a kofar gifan sa kuma yqna ciniki sosai gidansu dan madai daici ne
A halin yqnxu farhat batq da wani mane mi bawai basa kawo mata hari bane kawai dai bata sauraransu ne hasalima ta tsani kula samari
Tana da aminiya mai suna khadija ana ce mata nana tun suna yara tare suka taso har yqnxu nana suma talakawa ne kamarsu farhat sai dai suna da rufin asiri
*CIGABAN LABARIN*
Khaleel da abdul haka suka ta tattauna yadda farhat take da kyau shi dai abdul har yqnxu mamakin yadda khaleel ya canja yake tashi daya mutum ya susuce akan mace
Haka dai suka tayi har duka isa kofar gidan su abdul ya ajiye shi sannam ya nufi hospital dinna dan yana da marasa lafiya
Yana shiga ya fara dubasu haka ya kai har magriba sana ya kuma gida
Yana shiga ya samu sabeer da shaheed ne kawai a falon sukace bro sannu da dawowa yace yauwa ina ammi sukace ta tafi gidan alhaji sani dubiya yace ok
Ya juya yayi fanninsa domin ya huta
Washe gari da misalin karfe biyar na yamma khaleel ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda mai mugun kyau sai tashin kamshi yake yi ya nufi gidan su farhat
Yana isa yayi parking dan nesa da gidan sannam ya samu wani yaro yace kai jika gidan can kace ana sallama da farhat
Yaron yaje da gudunsa yana shiga ya tarar da farhat da innanta suna hira da sallamarsa yace wai ana sallama da farhat
A firgice da dago tace kace bata nam
Yaron har ya juya inna ta kirasa tqce kai yaro kaje kace tana fitowa
Yana fita inna tace haba farhat ya kamatq yqnxu kam ki tsaya ki nutsu har allah ya kawo miki miji na gari kiyi aurenki amma ke sam bakiso
Duk wanda yaxo sai kin koreshi dan allah wannam kam ki tsaya ki saurareshi duk da ban sam wanene ba haka inna ta ta mata sannam ta gamsu da maganar inna ta tadhi ta dauki hija binta tayi waje