© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 28 }
*DARIYA BASO BA, BA DUKA MAI MAKA DARIYA NE MASOYINKA KAMAR YADDA BA DUKA MAI DAURE MAKA BANE MAKIYINKA BA, YAU DA GOBE KE NUNA MAKA MAI SONKA DA GASKE, SANIN MASOYI SAI ALLAH👌🏼*
Ana saura sati biyu biki suka tattaro gaba d'aya, saida suka tsaya ta Sokoto da nufin zuwa ga mahaifin Salamah a shawarar Abba, tanason da k'aunar ganin mahaifinta saidai Bata da tabbas akan ko zai karb'e ta, tunda shiya korata da kansa, jikinta a sanyaye suka shiga unguwar tana Mai musu kwatancen gurin dake motarsu a gaba ita da Nuren Feenah da Kausar wancen Kuma mom da Abba saif ke jansu Nuriyya sai daga baya zasu zo da mijinta...
Ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba lokacin da ta samu labarin Wai mahaifinta yabar gari tare da matarsa, duka tunanin ta tsayawa yayi cak, to me wannan matar ke nufi da rayuwar su kenan? Shikenan ta rabasa da kowa nasa daga ita sai shi, kukan ta kasa b'oyuwa abubuwa sunyi Mata yawa akai dauriyarta ta gaza, yanzu ta Ina zata Fara neman mahaifinta, bayan ta rayu ba mahaifiya lokacin da ta samu hope akan samunta kuma a lokacin ne ta rasa mahaifi? Gashi batasan wani a garin ba Wanda zata Kira nasa batasan danginsa ba Taya zata sadu dasu su Kuma?
"Allah Kaine Allah, kaike samar wa bawan da ya maida al'amuransa a gareka mafita, Allah ka saukaka min ka samamin mafita ta alkhairi daga gareta" addu'o'i take ta maimaita a ranta tana hawaye, Sossai jikin su Abba yay sanyi, tabbas a cikin rayuwarta akwai jarabobi masu yawa, tabbas taga rayuwa, rarrashi da ban baki kawai suke da zarahin yi Mata, dolenta ta share hawayen tare da b'oye damuwarta tabbas wannan ahalin suna Mata matuk'ar halacci suna damuwa da damuwarta su kuma koka da kukanta......
Sossai ta sake kamar batada wata damuwa, musamman yadda anan ma kowa ke na'am na'am da ita basu nuna mata kyama ko wani banbanci har kakarsu sai janta take da wasa tana ce Mata kishiyar ta, kowa dai nata musamman yadda take respecting d'insu ga Kuma Kama jiki Sam ba kyuya Wanda training din Sofie ne shine kad'ai abinda takejin ta Mata na alkhairi Wanda ita sofin duk cikin cutarwa ta ajesa...
Ba laifi zasu d'an tab'a bidia a bikin Dan an tsara even yakai biyar, kamu, kalcha, budar kai, dinner, idan anje Abuja Kuma akwai get together, sunyi ankonsu na duka evens din su biyar, ita Feenah, Kausar, Ummitar da kuma Ya Nuriyya, Nan fa sauran matasan 'yan matan sa'o'insu suka ce Sam basu yadda ba Dole suka shiga kasuwa Suma suka samo irinsa ko Mai yanayi da nasun suka dinki a matsayin nasu dangin ango tunda already b'angaren amarya sunyi nasu.....
Haka aka Fara event d'in abun sai Wanda ya gani, kamu aka Fara hall aka Kama, akayi Mai decoration na musamman DJ suka saki sounds na yayi Kuma na manyan yara classic guys, ranar ankon wani material sukayi black da head red, wow ba k'arya sunyi Cara Dan kuwa kad'an ya rage su danne amarya su fita hadewa, abinda yafi komai birgewa yadda sukayi Ruwan nera lokacin da aka fitar da ango da amarya sun zuba musu liki kamar ba a jikinsu suke fitarwa ba sossai suka ja ma ya Saif girmansa Dan kuwa sun yi Karin da ba Wanda yayi irinsa haka aka watse taron dasu a baki, wasu had'uwarsu suke yabawa yayinda wasu ke yaba personalitys nasu musamman Salamah data fita daban kunsan dai doctor komai nasu unique ne.lol
Kausar da Nuren kuwa tuni aka tsarke tun su Salamah na fad'a tana cewa it's just shakuwa fa irin ta yan uwa, oga nuren Kam dake direct to d point ne Kai tsaye yace no more shakuwa it love oo.
Nan fa sukayi ma Salamah caa itama lallai ta zab'a cikin masu tururuwar son ta d'innan ku Kuma suyi sadakarta, cewar kaka, Abba ne ya tare Mata yace 'yarsa ai Dr ce karatun ta bayason shiririta Dan haka su k'yaleta masa 'ya ta zab'a cikin nutsuwa....
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love