© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 34 }
*Na samu gyara daga wata 'yar uwa ma'abociya bibiyar wannan novel d'in, wajen sunayen iyalan gidan Alhaji Yaro Majidadi, da mukace sun kasance shuwa ne, sai kuma mukayi amfani da sunayen kanuri, afuwan afuwan gareku Baki d'aya, a gaskiya ban sani bane shiyasa nayi amfani dasu kasancewar ji kawai muke Maiduguri da kebbi state nisan ya isu so kunga sanin ainihin dabi'unsu da al'adunsu saida tambaya, so gaskiya mukam tambaya normally duk rubutu irin haka ya Kama, kawai dai abu ne na yau da gobe akwai mantuwa so pls ku gafarceni, daga yanzu duk inda ya Kamata mu Kama suna zakuga sunayen sun canja zuwa na shuwa a maimakon na kanurin da mukayi amfani dashi a farko nagode😊, 'yar uwa wato Umm annur, kema godiyar ki ta daban ce, wannan ne ke tabbatar Mana da lallai munada fans masu bibiyar rubutun mu, Ina fatar Allah yasa mu amfana da rubuce rubucen mu, mudaku gaba d'aya, kuskuren da ke ciki Allah ya shafe a zuciya a kuma rubuce nagode👌🏼*
Cikin kwanaki ukun da sukayi a Skk Kuma lokutan da ta kasance da Harun, sun zame mata wasu ranaku ne sababbi, masu cike da sababbin abubuwa a cikin rayuwarta, mace budurwa matashiya Mai ji da kuruciya, ba abinda tafi buk'ata a wannan gabar bayan cikakkiyar soyayya da kulawa agun abokin rayuwar ta, idan mukayi la'akari da rayuwar gidansu Umm Ruman rayuwace da basu samu wannan 'yancin ba, to Amma dole zasusan soyayya kodon kud'anya da mutane da suke a makarantu da Kuma kawayen su, ga karance karance littafai da ba'a raba yara Mata dashi duk zasu sani anan, so irin soyayyar da takeji a bakin k'awayenta a littafai sai gashi a cikin kwanaki uku ta samu zazzafar soyayyar da bata tab'a tunanin samu ba a rayuwa, kowa yasan zuciyar mace da rauni akan soyayya, Allah Kuma yayi Harun ma'abocin iya tattali, soyayya da cikakkiyar kulawa, da wannan cikin sauk'i yayi nasarar mallake zuciyar ta, abun da yafi Bata mamaki da sakata Kara sakankancewa dashi befi yadda ya yarda ya biyota har garinsu ba domin ya tattabar Mata da soyayyar sa.......
Duk da babu son musgunawa ko sab'awa umurnin masoyin kakan nata a ranta, saidai fa batajin zata hak'ura da soyayyar Harun koya zata kasance Kuma, tunda ta kwana da sanin meye zai biyo baya, sai a yanzu ta k'ara gasgata dalilin gwaggonta Ayssa na yarda tabi masoyin rayuwar ta, lallai soyayya ta daban ce, abin Kuma ya Kara sakata sakankancewa ganin Ayssa tanacan zamanta a inda ba Wanda ya sani kuma da alama tanajin Dad'in zama acan ko daga zuwa biyun da tayi sunga alamu, da wannan itama tayi Shirin yin gaba da gaba da wannan al'adar, Dan kowa Yana kokawa da mummmunar akidar, kukan kuwa ba akansu kad'ai matasa ba har iyayensu dake zaune a Dole suna kokawa badai yadda zakayi ne....
*********
*Yau fa akeyinta*😆
Lokacin da labari ya riski dattijo Alhaji Yaro Majidadi, abun ba ya tab'a shi fiye da tsammani Dan Sam bai kawo kwatankwacin hakan a tare da wani daga cikin zuri'arsa Kuma ba, duba da abinda ya faru baya irin hukuncin da yayi wa masoyiyar 'yarsa duk Dan ya tauna tsakuwa Dan aya taji tsoro, to me yasa Kuma wannan karan ma sai akan mosoyiyar jik'arsa? Meyasa sai wad'anda yafi k'auna ne? (Amsar d'aya ce dattijo daka kasa ganewa wato a jarabawa ce ake maka kana kasa jurewa)..
Sossai dagash (Baba gana ada) mahaifin Umm Ruman ya hayyak'e ta tare da tabbatar Mata ko zata mutu bata da miji bayan Aliyu, hakanan ya k'ara da cewa idan kuwa ta nace akan bakatar to tabbas zai sallameta ita da uwarta(nifa maza na bani mamaki har yau, meyasa laifin 'ya ke shafar uwane har kullum, bayan uwar Nan batamasan yaushe akayi ba, Bata isa ta bud'e zuciyar 'yar ta saka Mata soko k'i ba, Amma a kullum da irin haka ta samu sai ace za'a koreki keda uwarki, ko Kuma a bakin auren uwarki, oh uwayen Mata na ganin takan su)
Shattima kuwa wato mahaifin Aliyu, kanin dagash cewa yayi Dan Allah su barta ta auri wanda takeso, sudai fatansu ta kasance cikin farinciki, wannan karan Kam mutane da yawa sun saka Baki akan auren Umm Ruman, wad'anda da dama al'adar ta cutar dasu ba kad'an ba.....
K'arshe dai a kotun Alhaji yaro aka Kai k'arshen lamarin...
"Rumana keda Aisha Kun kasance mafi soyuwa agareni Kuma kud'in dai nake Shan katakka daku, banaso na rasaki kamar yadda na rasa Ayssa, ina kewar Aisha Ina son ganin Aisha, saidai ban Ina zan ganta ba, bansan inane ba" Sossai jikin ahalin yayi sanyi da kalamansa, Ashe tsohon nasu jarumta kawai yake nunawa irin ta masu dakakkiyar zuciya da taurin rai shima Yana kewar 'yarsa kamar yadda suke kewar 'yar uwarsu...
"Ummu Rumana, bazan tauyeki ba kamar yadda na tauye Ayssa kije ki auri Wanda kikeso, aliyun ma nayi magana dashi yace mu Baki Wanda kikeso Dan haka mun Baki Haruna, Rumana, ko a gobe ya shirya yazo a d'aura muku aure.."
Duk ilahirin jikin Umm Ruman ya Gama yin sanyi a lokacin, batayi tsammani haka da sauk'i daga gurin tsohon ba, tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suke cewa duniya ka horon Wawa, sossai taji soyayyar ahalin ta nason ya rinjayi ta Harun, take jin haushin Kanta na meyasa Bata tuna soyayya da k'auna da suke sharing a familyn su ba? Meyasa ta manta k'aunar tsoho Alhaji Yaro gareta??? Meyasa ta....
"Baba Dan Allah karka cire Rumana a cikin zuri'arka kamar yadda ka cire Ayssa Dan Allah ka barta muyi zumunci" Bintu yayar Ayssa ta fad'a cikin rauni da jin kewar 'yar uwarta su fiye da kullum, wacce basusan ainihin inda take ba a yanzu...
"Kayya Bintu, basan sake wannan kuskuren da nayi ga Ayssa ba akan Rumana, inason ganin Ayssa ko sau d'aya ne, babu Dama, Dana ce kar ta dawo ta d'auka da gaske Nike gashi har yanzu taki dawowa" wasu Kam tuni sun Fara kokawa da tausayin tsohon da kansu,
"Jikata Rumana ba irin wannan auren zatayi ba, kune zaku kaita har mazauninta kuga inda take" da wannan aka Fara shirye shiryen biki, anko yi biki na bajinta dangin Harun duk sunzo sunga al'adun shuwa sannan aka tattara aka kawo amarya Skk cike da rakiyar 'yan uwa da abokan arziki, sun zuba Mata kaya na kece reni, kamar yadda Harun yayi k'okari sossai wurin tsara gidan....
Abu d'aya ne Umm Ruman ke tunawa Yana tsorata ta, cewar da mahaifinta yayi jindad'in auren ta ya zama nata haka matsalar auren ta ta zama, karta yadda tazo musu da sunan sabani ko matsala, zumunci kawai suke buk'ata daga gareta tunda ita ta zaba da kanta, hankalin ta kan kwanta idan ta tuna irin mijin da take tare dashi just a loving and caring husband ever....
Zaman lafia Sossai suke wanzar wa a tsakanin su, suna fahimta sossai suna girmama juna da kula da juna, kowanne a cikinsu farincikin Dan uwansa yakeson gani, matsala d'aya ce data fuskanta da Harun shine bai damu da 'yan uwansa ba dasu ka kasance a kauye, shima sannu sannu ta Fara cusa masa ra'ayin kulawa dasu Dan ba abin jin dad'inta bane, Dan mijinta bai damu da 'yan uwansa ba, domin in taji Dadi ma a yanzu watarana akanta abun zai k'are (hattadai 'yan uwa Mata masu jin dad'i Dan mazajensu basu damu da 'yan uwansu ba, domin kuwa kema 'yar uwar wasu ce Kuma dangin wasu ce, Kuma watarana uwar wani kike kenan dai Abun bulaliyar kan hanya ce fad'e yaro fad'e babba)..
*************
Bayan auren Ummu Ruman 'yan watanni tsakani dattijo Alhaji yaro Majidadi ya kwanta ciwo, tunda ya kwanta baida abun Kira sai Ayssa, su nemo masa Ayssa ya ganta ya rok'eta ta yafe masa, sossai hankalin ahalin ya d'aga ganin halin da ja gaba Kuma uba a garesu ya shiga, sunyi iya k'okarin na yadda za'ayi su samu Ayssa ba'adace.....
A haka ciwo yayi ma Alhaji yaro nisa, Ayssa na a bakinsa, Allahu Akbar Rai bak'on duniya koya dad'e cikinta Dole ya barta, Alhaji yaro ya amsa kiran mahaliccinsa, Wanda nidake dasu duk shi muke jira Allah ya bamu kyakkyawan k'arshe.........
Pls
#Vote#
#Share#
#Comment#*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Ficción GeneralIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love