DAMA TA BIYU
(The Second chance)🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....
Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu*Alhamdulillah Alhamdulillahi ina matuqar godiya ga ubangi mahaliccin mu daya bani ikon kallama littafin qaddara ce sila yanzu kuma na shigo sabo ina matuqar godiya ga masoya littafin qaddar ce sila da irin soyayyar da suka nuna min Allah ya bar zumunci.*
Ina matuqar godiya ga en uwana en qungiyar mu ta HAJOW Allah yabar zumunci ina matuqar son ku en uwa.
Wannan littafin sadaukarwa ga qungiyar Hajow dafatan Allah ya qara had'a zukatanmu ya bamu haquri d juriyar zama da juna,i heart you sisters.🥰🥰
0️⃣1️⃣
"Salamu'alaykum." Aka fad'a cikin siririyar qaramar murya mai dad'in saurare ga mutumin da yaji ta."Waalaykisalam." Ya amsa yana shan madarar da akayi mata dambu tasha sugar ga gard'i irin na dafaffiyar madara.
Da gefen ido ta kalle shi saboda bata da yawan qurawa abu ido ta d'an duqa alamun girmamawa tace "Ina wuni."
Cikin fara'ar da kana gani kasan daman caan jikin sa ce yace "Lafiya lau yan makaranta."
Murmushi tayi ta miqe tana niyyar shiga d'akin da ke fuskantar su taji mahaifiyar ta Innah Lari na cewa "Immileey an dawo?maza ciro kayan kizo na aike ki gidan Laraba."
Da kyakkyawan murmushin ta tace "To Innah."
Ta shige d'akin ta ciro kayan ta sako doguwar riga ta yadi baqi da digon yellow da ja a jiki,duk da ya kod'e bai hana shi yi mata kyau ba hijabi ta d'oro akai ta fito,wanda ke tsakar gidan ya miqe yana cewa "Goggo bari na wuce nagode zandawo anjima naci abincin dare."
Murmushi tayi tace "Sai ka dawo Muhammadu."
Ya juya ya fita yana cewa "Toh."
Immileey ta bishi da kallo ta gefen ido sannan tace da mahaifiyar ta ta "Innah wanene wannan?"
A takaice tace "Muhammadu d'iyan Ja'afar ne dake birni."
Ta gane waye Ja'afar d'in don haka tace "Oh daman yana da manyan yara Innah amma baya zuwa dasu?"
Dariya Goggo Lari tayi tace "Ha'a banda shirmen ki Immileey baban kuma baki ga yana da su Surajo ba kuma sa'anni suke ai ko."
Gyad'a kai tayi tace "Haka ne,bani saqon to na tafi."
Saqon ta miqa mata ta mata bayani ta tafi ita kuma ta cigaba da gyaran tsakar gidan.
***
Immileey kam data fita gidan su qawarta Fad'ima taje maqotan su tace tazo ta raka ta don tafiyar da er tazara don haka bata fiye son zuwa gidan Goggon nasu ba.Suka fito suna ta hira abinsu daga gani da yarinta a tare dasu amma kuma da cikakkiyar nutsuwa.
Sun kusan isa gidan Goggon wasu gungun samari sun yi goma suka hango su tun daga nesa fad'ima tace da Immileey "Lah kinga su Turajo Immileey."
Kai ta d'aga ta hange su da abokan sa shima kamar had'in baki suka ce masa ga su Immileey can fa.
Sauri ta qara harda gudu gudu don tana iya hango gidan Goggon ta su,ita ko Fad'ima tsayawa tayi har suka qaraso suka gaisa sannan ta wuce gidan da tuni Immileey ta dad'e a ciki ta samu harta bada saqon ta fito tana lab'e a zauren tana kallon su so take su wuce ta tafi ita ma.