Part 3

485 31 0
                                    




DAMA TA BIYU
(The Second chance)

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.
Insta:fateeykibia.

RAYUWAR FATIMA da NABEEHA tasa na gane ANA BARIN HALAK..ko don kunya kuma QADDARA CE SILAR data sa ake samun DAMA TA BIYU....

Littafan marubuciyar (ZahraArkel)
1.Rayuwar fatima
2.Nabeeha
3.Ana barin halak
4.Qaddara ce sila
5.Dama ta biyu


0️⃣3️⃣
Mooha saida ya raka mahaifin su har cikin sashen sa a falon sa ya ajiye masa jakar sa sannan ya koma ya shiga sashen mahaifiyar su Hajiya Asiya tana zaune kan darduma da alamu sallah ta idar tana jan casbaha ya tsuguna gabanta ya gaida ta cike da jin dad'i da kulawa ta amsa kana tace "Ina d'an uwan naka kuma."

Ya d'an sosa kai yana qunshe dariya yace "Yana can Yana Sana'a."

Murmushi tayi don sarai ta gane me yake nufi tace "Me kuka yi masa kuma?"

Sake dariyar sa yayi yace "Mummy kinsan halin kayan ki ba sai an masa wani abu bama."

Gyad'a kai tayi tana miqewa tace "Bari naje wajen Abi in yaso sai in zo inji abinda kuka masa."

Ya miqe yana sake dariya yace "Mu bamuyi masa komai ba hali ne dai mai shi baya fasawa."

Daga haka ya fice ita kuma tayi sashen mahaifin su,ta tadda shi a falo ya fito d'aukan ruwa,da sauri ta qarasa tana cewa "Bari na d'auko maka mana."

Da kallon tsantsar so ya bita yana murmushi yace "Nagode."

Ta bud'e masa ruwan ta zuba a cup ta miqa masa ya sha ya miqo mata cup d'in yana cewa "Nagode Allah yayi miki albarka mace ta gari farin cikina."

Cikin wani irin yauqi da murmushi na jan hankali kamar bata ajiye su Mooha ba tace "Uw mijina and thank you muje kayi wanka sai muje kaci abinci nasan kana buqatar sa."

Dariya yayi ya wuce ta bishi a baya ta had'a masa ruwan wanka kafin ya fito ta dauko masa jallabiya milk colour silk mai kyau sosai ta feshe ta da turaren sa designer yana fitowa ta taimaka masa ya shirya suka fita falo suna hawa dinning emmatan gidan Jannah shekara sha biyu da Amnah mai shekara goma suka shigo daga makarantar islamiyya da sukeyi ta weekends da Murna Amnah ta tafi wajen sa tana cewa "Oyoyo Abeeyn mu ka dawo mana da Granny??"

Girgiza kansa yayi yana dariya tare da shafa kanta yace "Ai granny baza ta biyo ni ba saboda bata son binni."

D'an turo baki tayi tace "Saboda me bata son binnin to?"

Yayi murmushi yace "Bata saba ba amma zan kaiku ku ku ganta kuna yin hutun islamiyya this week."

Da murna tace toh,ta juya ta haye sama d'akinsu sai a sannan sarkin mulki Jannah ta motsa kamar bata so ta gaida mahaifin nasu sai kace me ciwon baki.

Da murmushi yace "Mamana kenan sarkin qunci ya kamata ki daina wannan fushin kinfa girma."

Ta turo baki Hajiya Asiya kuwa sai tayi kamar zata mangare ta tace "Rabu da shashasha karma ta daina ita da za a kai gidan wani dangin wasu idan suka gyara mata zama ta saitu ai tana girma tana cin qasa sokuwa mara wayo."

Tuni qwallar data tarar mata ta shiga zubowa tana turo baki kafin Alhaji Khamis yayi magana Mooha ya shigo falon ya canja kaya shima ya saka qananu marasa nauyi,ya kalle ta "Cutie menene?"

Da hannu ta nuna masa Hajiya Asiya data d'auke kanta kamar bata san da halittar Jannah a falon ba sai yayi murmushi yasan sunyi halin ne yace "Maza je ki cire uniform kizo kici abinci kinsan halin Mummy ai."

Wata harara ta galla masa tace "Tasan halina kamar yaya?"

Sosa kai yayi yana danne dariyar sa yace "Aa nufina tasan halin ki na bakya son tab'ara ba kya son rashin jin magana."

Qwafa tayi tace "Ai wallahi gab nake da yi mata dukan tsiya ma inta sa wasa shashasha kawai."

Gaba tayi tana zumbura baki ta haye sama lokacin kuma Amnah ta sauko ta shirya cikin doguwar riga daidai ita aabun sha'awa Jannah ta bangaje ta ta wuce murmushi kawai tayi ta dawo kusa da Alhaji Khamis tace "Abi ka bani labarin Gogel."

Murmushi yayi yana shafa kanta yana tsananin son Aminatu Amnan sa yarinyar duk da qarancin shekarun ta akwai haquri da juriya da kauda kai a abubuwa da dama yanzun kowa yaga yanda Jannan ta bangaje ta amma maimakon tayi kuka ko rigima irin ta yara sa'o'inta sai tayi murmushi kawai ta nuna bata san anyi ba shiyasa lokuta da dama Jannah ke sawa yake mata fad'a fiye da Amnah.

A hankali ya dinga bata labari tana cin abinci tana jin dad'in labarin har ya gama cike da zumud'i tace "Toh Abi yaushe zamu je??"

Yayi dariya ya maida dubansa ga Hajiya Asiya yace "An saka ranar Khadijatu er wajen Hafizu wata biyu saboda haka lokacin zamuje."

Cike da murna da jin dad'i tace "MashaAllahu Allah yasa alkhairi yasa ayi damu ya kuma saka gidan zaman tane."

"Amin." Mooha da Alhaji Khamis suka amsa.

Mooha ya yafito Amnah yace "Zo na nuna miki en garin ku ki gani kinji."

Ta koma wajensa da sauri tana cewa "Yawwa Ya Mooha nuna min."

Daidai lokacin Jannah ta sauko tazo ta d'ebi abinci ta koma falo ta zauna saboda wai fushi take da kowa harda Moohan da yayii mata magana kuma ya goyi bayan mahaifiyar su.

Babu wanda yabi ta kanta har ta gama cin abincin ta miqe ta kai kwanon kitchen ta koma ta haye sama abinta kai tsaye kuma ta wuce bedroom d'insu ta kwanta daman kuma bacci take ji tana kwanciya bacci ya sace ta.

A falo kam Amnah da Mooha kawai ya rage don Alhaji Khamis ma yana gamawa ya koma bedroom d'insa shida Haj Asiya suka cigaba da hirar su.

Suna zaunen Lameen ya shigo Amnah ta miqe da gudu ta taro shi tana cewa "Jaan L inata neman ka."

Ya shafa kanta yana dariya yace "No Jaan A baki neme niba ai ina d'aki na kuma bakije ba."

Dariya tayi itama har dimples d'inta suka lotsa tace "Eh banje ba ina kallon videos ne a wayar Ya Mooha shiyasa."

Kumatunta yaja yace "Its Ok My Jaan bari na fito muje shan ice cream."

Tsalle ta fara da gudu kuma ta haura sama ta d'auko hijab d'inta ta sauko tana jiran fitowar tasa.

Mooha duk abinda suke yana zaune yana kallon su yana murmushi yana mamakin irin so da shaquwar dake tsakanin Lameen da Amnah,don ko fushi Lameen yake Amnah tazo wajen to ya daina kenan saidai ko zai cigaba sai ta bar wajen kuma a duk cikin su babu wanda yake tsananin so yana riritawa irinta in ana son aga hargowa da tashin hankalin sa to a tab'a masa Amnah yanzu zai haukacewa kowa kuma har iyayen su yake wa don akwai watarana da Amnan tayi wasan ruwa Mummyn su ta dake ta ranar yi yayi kamar zai rama mata kukan ma tare suka yi ya yini yana mita da surutun dukan ita kanta Haj Asiya mamaki ne ya hana ta magana da tsoro.

Yana murmushi da tuna irin shaquwar su ya miqe ya fice yana ce mata sai sun dawo ta amsa da to ta cigaba da kallon cartoon tana jiran fitowar tasa.

ZahraArkel.

DAMA TA BIYUWhere stories live. Discover now